Abin Da Ya Biyo Bayan Bugun Matar Aure A Gidan Sanata Ali Wakili

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Matar nan mai suna Balkisu Muhammad wacce wani ɗan sanda mai suna Jonathan Ɓong ya lakaɗa wa duka a gidan Sanatan Bauchi ta Kudu, Ali Wakili ta bayyana matuƙar damuwarta a bisa yadda ake neman juya mata kokenta zuwa ga wani abin na daban.

Ta bayyana maƙutar damuwarta da cewa, tun bayan lokacin da ta bayyana wa duniya halin da take ciki ne kuma sai labari ya ke neman canza wa daga haƙiƙani zuwa wani abin na daban “Tun bayan da na kawo kuka na ga manema labarai, abubuwa da dama sun faru, saboda da, da na kai ƙara ofishin ‘yan sanda na GRA akan za su zo a zauna a yi magana kan abin da ya haɗani da jami’insu mai suna Jonathan Ɓong da ya buge ni, bai zo ba har dare, sai suka ce na tafi da safe mu dawo da ni da mijina. Mun dawo kuma basu nan, muka jirasu har zuwa ƙarfe 12 na rana”. A cewarta

Ta ƙara da cewa; “Tun daga wannan ranar ta juma’a ‘yan sandan nan ba su sake naman mu ba, sai bayan sati ɗaya, muna zuwa sai shi wani ɗan sanda Baba ya kirani ya ce mu zo ga wanda ya buge ɗin ya zo yan musu”.

Ta ci gaba da cewa zuwansu ke da wuya kuma sai aka wuce da ita CID ofis inda ake zarginta kan wasu laifuka “zuwanmu ke da wuya aka wuce da ni CID ofis, aka shaida min cewa wai nine ake zargi, waye mai ƙara aka ce wai ɗan sandan nan da ya bugeni shi ne mai ƙarana, sai na shaida wa ‘yan sandan cewar ni fa nine na kai ƙara GRC a dalilin bugu na da ya yi, sai ‘yan sanda suka juya min kes ɗin, suka kuma juya magana”.

Ta ce a lokacin da ta ji hakan lamarin ya bata mamaki sosai “na tambayesu ta yaya aka yi na zama ni ce abin zargi? Sai suka nuna min wata takarda wai ana zargi da aikata laifuka uku, bata suna, bada tsoro, da kuma shiga gonar wani. Sai na ce idan Allah mai adalci ne zai yi sakayya, sakamakon ni ba ‘yar siyasa bace, bana da kuɗi, bana da mai tsaya min na bar wa Allah, Allah shi ne mai adalci”.

Balkisu ta ce sun za su tsareta “A lokacin wai za su tsareni, sai jama’a suka yi roko gani da ciki, juna biyu, ga kuma bana da lafiya sai suka rabu dani. Ni ina rokon duk wata hukumar kare haƙƙin bil adama da ta shigo cikin lamarin domin ni gaskiya an zalumceni kuma ana shirin zalumtata. Maimakon ‘yan sanda su yi bincike a kan lamarin sai suka juya zance. Ga duka juya min kes”. A cewarta

Da take bayyana matsayar da suke a halin yanzu ta ce “yanzu dai sun ce nine abar zargi, sun rubuta min takardar koke, za su kaini kotu ne, ban tabbatar ba. juna biyu ma da na ke ɗauke da shi basu yarda ba sai da suka je asibitin BAKAS  aka sake tabbatarwa. Yanzu ba su kaini kotu ba, muna ta lilo dai, kuma bana da lafiya mijina ne ke ta ɗawainiya a kaina”.

To wake zarginki da laifuka uku ɗin nan? Sai ta amsa da cewa Sanatan Bauchi ta kudu Malam Ali Wakili ne ya ke zarginta “Lauyan Sanata Ali Wakili ne ya zo CID ofis, ya ce ga abin da Sanatansa ya rubuta a kaina, sai su kuma ‘yan sandan suka zauna a kan abin da ya rubuta”. Ta bayyana

Meya sa baki yi musu bayani kan bugunki da aka yi da kuma halin da kika samu kanki na shiga gidan ba? sai ta amsa mana da cewa; “ba su buƙaci hakan ba, saboda suna tsoron sanatan, suna tsoronshi saboda shi yana da muƙami, ni kuma bana siyasa bana da kowa ubana ba kowa bane, bana da kowa, shi ya sa. Ba a tambayeni ba, ba a nemi ɗan sandan ba, ba a kuma je gidan domin neman shaida a tabbbatar da abin da na faɗa ba, kuma akwai shaidu, shi kansa Sanatan na gida kamar yanda ɗan sandan ya bayyana da bakinsa, a matsayinsa na shugaba da sai ya bi kadinan wanda aka zalumcuta”. in ji ta

Balkisu dai ta bayyana cewar ita tun usuli ta shiga gidan Sanatan ne ma ba tare da sanin wai gidan sa bane, sun je ne da abokiyar tafiyarta domin yin sallah, kuma ta haƙiƙance kan cewa ita babu abin da ya haɗa ta da siyasa “na sha mamaki ni ban ce Sanata Ali Wakili ya dokini ba, babu inda na je na bayyana hakan, duk inda na kai koke na, ni da ɗan sanda na ke yi, kuma ban ce Ali Wakili ya min komai ba, bi hasalima ni ban sanshi ba, kuma bana da wata matsala da shi, don meye zai nemi kaini kotu alhali ban ci masa ba ban kuma sha masa ba. a gidansa ne abu ya faru da ni don haka dole na bayyana inda aka dokina, domin zalumcin ya yi yawa”.

Mata mai cikin ta buƙaci adalci gami da tabbatar da daidaito a tsakanin jama’a, ta roƙi masu binciken gaskiya da su tabbatar da yin bincike domin kareta daga faɗawa hanun masu mulki, da kuma jami’an tsaro ganin cewa haƙƙinta ta nema.

A wani labarin kuma, Balkisu Muhammad ta aike da takardar koke wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya a bisa dukan tsiya da wani ɗan sanda mai suna Jonathan ya yi mata a gidan sanatan Bauchi ta Kudu Ali Wakili. Takardar koken mai kwanan wata 26 ga watan Satumban, 2017 wacce lauyan wanda ke koken ya sanya wa hanu mai suna S.G Idrees ESƘ.

Ta kakardar koken ta ce “mune lauyoyin Balkisu Muhammed wacce take da zama a Bauchi, 21 ga Satumba, 2017 a lokacin da Balkisu suke ƙoƙarin cike takardar neman rance a wajen gwamnatin jihar Bauchi, shigowar lokacin sallah azahar ke da wuya sai Hauwa Yufus Uman (Mummy) ta ce su shiga wani gida domin su yi sallah. Bayan sun shiga sun nemi a yi musu iso zuwa ga ɗaya daga cikin matan Sanata Ali Wakili, daga baya dai aka shaida musu bata nan”. A cewar takardar lauyan

Takardar ta ci kuma gaba da cewa “Bayan da suka fita, suna cikin a daidaita sahu ne sai Balkisu ta lura ta mance da Jakarta a gidan Sanatan. A ranar juma’a 22 ga Satumba 2017 ne wacce muke tsaya mata ta je gidan domin bin sahun ko Allah ya sa wani ya ga jakar nata, wacce ta mance da shi, a ciki akwai ID Card, Post Natal Card, Hand Card ATBUTH, kuɗi naira dubu biyar, da wasu fasfo da sauransu”.

Takardar lauyoyin ya ci gaba da yin bayani wa rundunar ‘yan sandan inda suka ci gaba da cewa bayan suna zantawa yanda aka yi ta mance jakar nata da wani ɗan sanda kamar yanda ya kamata sai wani ɗan sanda mai suna Jonathan Ɓong mai lambar aikin 453004 ya hauta da duka inda ya buge ta a wajaje da dama, a cewar takardau lauyoyin.

A bisa haka ne dai lauyoyinta suka buƙaci rundunar ‘yan sanda da su tabbatar da bin lamarin gami da tabbatar da adalci domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Kwafin takardar lauyoyin wacce suka aiketa ga babban shugaban ‘yan sandan Nijeriya IG, da kuma shugaban rundunar ‘yan sanda na zone 12 da ke Bauchi.

A lokacin da wakilinmu ya nemi Sanatan Bauchi ta Kudu, Ali Wakili don ji daga garesa bai samu gamsashiyar amsa ba; kana ya aike masa da sakon karta kwana da kira ta waya doka shiru ya zuwa aiko da rahoton nan. Amma da zarar ya amsa mana tambayoyinmu za ku ji bahasi daga ɓangarensa.

Shi mai Kamal Datti Abubakar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ya tabbatar wa wakilinmu cewar matuƙar matar nan ta aike da kokenta ga jami’ansu za su tabbatar da an binciki haƙiƙin lamarin.

Ya zuwa haɗa wannan rahoton, Balkisu Muhammad tana zaman jiran kira ne daga kotu ko akasin haka, a sakamakon takardar da Lauyan Sanata ya shigar a gaban rundunar ‘yan sandan inda ya ke zarginta da laifuku uku, ɓata suna, shiga huruminsa ba bisa ƙa’ida ba, da kuma bada tsoro.

Exit mobile version