Connect with us

LABARAI

Abin Da Ya Faru Da Kemi Adeosun, Darasi Ne Ga Na Baya – Sharu Usmaniyya

Published

on

An yi kira ga ‘yan siyasa da kuma masu rike da madafun iko a cikin gwamnati har ma da kamfanoni da hukumomi da su dauki darasi daga abin da ya faru da tsohuwar Ministar kudi ta kasar nan, Kemi Adeosun, wacce ta ajiye aiki a sakamkon samunta da aka yi da yin amfani da jabun takardar shaidar yi wa kasa hidima wanda kwamitin da aka kafa ya bincike ta kan lamarin ya yi.

Kiran ya fito ne daga bakin daya daga cikin masu fada a ji a Jihar Kaduna, kuma babban dan kasuwa musamman ta fuskacin sana’ar man fetur, Shariff Abubakar Usman, Mai kamfanin mai na Usmaniyya, a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP A YAU ASABAR, a ofishinsa da ke kan titin Nnamdi Azikwe da ke Kaduna.

Shariff Usman Abubakar, ya bayyana abin da ya faru da tsohuwar Ministar da cewa abin kunya ne da takaici, wanda kuma akwai yiwuwar a samu wasu manyan jami’an gwamnatin da irin wannan kazantar a tare da su. Shariff Usman yace, “Idan da a ce an kau da kai kan abin da tsohuwar Ministar ta yi ba tare da an yi wani hukuncin da zai zama ishara ga masu aikata irin wadannan abubuwa ba, to nan gaba wasu ma za su aikata abin da ya fi nata din.

Shariff Usmaniyya yace, “Ita da kanta Kemi Adeosun din ta san abin da ta aikata, sai dai ba ta yi tsammanin watarana asiri zai tonu ba. In mun lura, tamkar abin da ta aikatan ba wani abu ne mai girma ba, domin ba wai karatun ne ba ta yi ba, sai dai, ba ta yi aikin yi wa kasa hidima ne ba, wanda kuma wannan ka’ida ce ta dokar kasa wacce tilas ne ga duk wanda ya kammala karatun shi ya yi wa kasarsa wannan hidiman. Wanda kuma wannan abu ne mai kyau, domin abu ne da aka yi shi da nufin kara cusa kishin kasa da al’ummanta a zukatan matasa, wanda daman tun mutum na yaro zuwa matashi ne ya kamata a cusa masa wannan ra’ayin domin kar ya girma ya kama aiki har ya zama wani abu alhalin yana mai ta’assubanci na Addini, kabilanci ko bangaranci, an fi kaunan kowa ya tashi ne da kishin kasarsa da al’umman kasan baki dayanta.

Shariff Usmaniyya, ya soki ra’ayin masu kiran da a je a kamo ta a hukunta ta da cewa, “Wannan gajin hakuri ne, ai kamata ya yi su jira su ga abin da gwamnati za ta yi, domin wannan ba abu ne wanda za a iya cewa a kyale ta ba. Sai dai duk da hakan, Shariff Usman, ya yaba wa tsohuwar Ministar kan yadda ta gaggauta amsa laifin ta ba tare da ta wahalar da shari’a ba, ta kuma yi abin da ya dace, inda ta ajiye mukamin na ta nan take.

Shariff Usman, ya soki lamirin masu cewa, wai wannan abin kunyan da tsohuwar Ministan ta yi zai yi wa wannan gwamnatin wani miki, inda yake cewa, “Sam wannan abin ba wani abu ne da ya shafi wannan gwamnatin ba, a maimakon hakan ma, wannan ya kara fito da gaskiyar gwamnatin ne a sarari.”

A karshe, Shariff Usman ya kirayi dukkanin jami’an gwamnati da ma na hukumomin gwamnatin da suka san suna da irin wannan laifin a boye tare da su ko kuma makamancin hakan, da su hanzarta rufawa kansu asiri su bi sahun Kemi Adeosun, tun kafin Allah Ya tona wa al’umma asirin na su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: