Safna Aliyu ita ce zakakurar da ta jagoranci kafa Kungiyar Marubuta ta Perfect Writers. A wannan tattauwanar da muka yi da ita, ta bayyana yadda gwagwarmayar kafuwar kungiyar ta kasance. Ga cikakkiyar hirar:
Ya sunan Malamar?
Sunana Safna Aliyu Jawabi, daga kungiyar Perfect Writers Association.
Ko masu karatu za su iya sanin asalin wanda ya assassa ita wannan kungiya?
Toh wanda ya kafa ita wannan kungiya ta marubuta ba kowa ba ne fa ce ni da kaina.
Me ya ja hankalinli har ki ka bude ita wannan kungiya?
Eh to a gaskiya abin da ya ja hankalina har na bude ita wannan kungiya dai saboda wayar da kan al’umma ne, misali kin ga akwai marubuta a cikinta masu buri da kuma son wayar da kan al’umma ta hanyar rubutu. Yanzu al’umma Hausa dama yaruka wa ‘yan da su ke iya karatun Hausa. liltafi ya zama kamar wata hanya ta wayar musu da kai cikin sauki ba tare da wata wahala ba, shi ya sa muka yi nazari, mu ka ga ya dace mu bude kungiyar domin marubuta.
Kenan kuna da yawa wanda ku ka bude kungiyar, ba ke kadai ki ka bude ba?
A’ah! Ni na bude ta da hannuna ba tare da kowa ba.
Lokacin da za ki bude ita wannan kungiya shin kin nemi shawarar wani ko wata, ko kuwa ke da kanki ki ka yi tunanin bude kungiyar?
To a gaskiya da farko ni da kaina na yi tunanin budewa, amma kasancewar ban san yadda abin ya ke ba, shi ya sa na nemi shawar wasu daga cikin marubuta.
Bayan da ki ka bude kungiyar da mutum nawa ki ka fara, kuma ta wacce hanya ki ka bi dan ganin kin bunkasa kungiyar wajen zuba membobi?
Tab! gaskiya na sha mattukkar wahala kafin na samu marubutan da za su shiga saboda a lokacin duk wacce na gani sai na ga ai da kungiyar ta, cikin ikon Allah a hankali na fara samun mutum biyu. Hanyar da na bi na same su kuwa ita ce, lura da na yi littafin su babu tambarin kungiya a jikinta haka ya sa na bi su firabet na yi musu tayin shiga cikin kungiya ta.
Membobin kungiyar a yanzu za su kai kamar guda nawa?
Yanzu haka kungiyar ta na da membobi guda 18.
Ita wannan kungiyar ta ki iya mata ne ciki ko kuwa har da maza?
Mata ne kawai a cikin kungiyar.
Kenan ki na nufin iya zallan mata ne za su kasance cikin kungiyar ko kuwa idan wani marubucin namiji ya gani yana so shi ga zai iya shiga ko ya abin yake?
Eh Tom ya danganta da yadda yanayi ya nuna, amma gaskiya a yanzu mata ne kawai zalla Kasancewar akwai matan aure a ciki shiyasa.
Ita wannan kungiyar za ta kai kamar shekara nawa da budewa?
Ita wannan Kungiya dai an bude ta ne a 1/1/2020, wanda kuma a yau take cika shekara daya da kafuwar ta.
Kafin ki bude kungiya ta ki ta kanki kasancewar ke marubuciya ce shin kin taba zama a wata kungiyar ko kuwa tun farkon fara rubutun ki da ta ki ki ka fara?
Eh da tawa na fara sai dai ganin irin wahalar da na ke wajan ganin na samu members ya sa na kulle kungiyar na shiga wata.
Kina nufin kenan a yanzu kungiyar na kulle ke kuma kina wata kungiyar ko ya kike nufi?
A baya kafin kungiyar ta kai wannan matakin na taba zama cikin wata kungiya.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta?
Eh mai girma kuwa, Kulubalan da na fuskanta na farko wanda ya girgiza tunani na shi ne sunan kungiya wanda na fara sakawa kungiya ta sosai na ke son sunan kuma duniya ta san kungiya ta da wannan sunan, amma rana tsaka wasu suka bijiro da zancen ai sunan kungiyar su ne, wannan abin ya taba min zuciya sosai har kuka sai da na yi daga baya na mika lamura na ga Allah na sake komawa baya na canza sunan kungiya.
Wanne irin nasarori ki ka samu game da wannan kungiya?
Eh Tom a gaskiya dai yanzu nasarar da zan buga kirji na ce na samu ita ce fadakar da al’umma da muke yi ta cikin wannan kungiya, kuma wanda ina da tabbacin da yawa sun amfana cikin abinda Allah ya ba mu.
Idan wata na son shiga wannan kungiya wacce hanya za ta bi dan ganin an dama da ita?
Hanya daya ce kawai shi ne ta tuntubi daya daga cikin ‘yan kungiyar in sha Allah za a bata dama.
Mene ne burinki na gaba game da ita wannan kungiya?
Burina shi ne kungiyar ta shahara ta kuma zama na daya wajan fadakar da Al’umma.
Kasancewar yau ita ce ranar da wannan kungiya ta ke cika shekara guda rana ta farin ciki a gareki, ya za ki bayyanawa masu karatu farin cikin ki, da kuma dan takaitaccen tarihin kungiyar?
A gaskiya farin ciki na ba zai misaltuba domin rana ce da ban taba mantawa da ita ba, dan ba zan manta tarihinta ba. Alhamdullahi alhamdullahi kamar yadda jariri ya ke fara koyar zama, haka ni ma na fara. Allah cikin ikon sa gashi yau duk kanni buruka na suna daf da cika. Kamar yadda kowa ya sani rubutu baiwa ce daga Allah na fara tun ina tunanin ba zan iya ba har na fara jin zan iya ko da kuwa ban kai wacce ko wani ba. Na fara sha’awar bude kungiya ne yayin da na ga da yawa suna amfani da sunan kungiyar su a saman liltafin su. Wai bayan na fara sakawa liltafina sunan kungiya ta wacce alokacin na zaba mata suna, wai-wai! gaskiya a lokacin na sha mattukar wahala gurin neman membobi kamar yadda na fada da zasu fara amsa sunan kungiya ta. Cikin ikon Allah na fara samu.daya bayan daya, mafi yawa daga cikin su ba sa ma rubutu amma a haka. Na yi hakuri, na zauna da su a haka, kai ganin abin ya yi yawa ya sa.nayi tunanin kawai gwara na bar batun kungiya na samu wata kungiya na shiga. Gaskiya na ji dadin zama cikin kungiyar.sai dai kuma kowa yasan yadda buri ya ke, saboda haka na fita daga cikin ta, na sake bude kungiyar na yi a karo na biyu cike.da yakinin cewar Allah zai dafa min. Cikin ikon Allah kuwa na samu jajirtattun marubuta. Mu ka hada karfi da karfe muka tada kungiyar. sosai kungiyar ta samu karbuwa kuma ta na amsa sunan ta da wancen sunan na farko da na fara sakawa, daga baya kuma mu ka canza mu ka mayar da ita PERFECT WRITER’S ASSOCIATION. A takaice dai tafiya ce mai dogon zango ta yadda inda na ce zan ba da duk ka tarihin kungiyar zan dauki lokaci mai tsayin gaskiya, wannan shi ne takaitaccen tarihin kungiyar.
Ko akwai wata shawara ko karin bayani da ki ke ganin za ki bawa sauran marubuta ko shuwagannin kungiyoyin marubuta?
Eh shawarar da zan bayar ita cez, mu sani cewar alkalami yafi takobi kaifi, kuma yanzu da yawan mutane sun fi daukar zancan cikin littafi su yi aiki da shi saboda haka mu gujewa rubutun da ba shi da amfani, mu tuna irin wahallalun da iyaye su ke sha wajan ganin sun tarbiyantar da ‘ya’yan su ta hanyar da ta dace. Shin ba kya tunanin idan ki ka yi rubutun da bai dace ba hakan yana iya juya akalar yarinya zuwa inda bai dace ba. Hmm ki sani sam! tsinuwar iyaye sam ba zai bari ki zauna lafiya ba, ina kira ga shugabannin kungiya da ku yi hatttara da irin marubutan da ku ke sakawa cikin kungiyar ku domin kuwa duk abinda suka yi kenan kema ki na da na ki kason, ALLAH ya sa mu dace.
Ko kina da wa ‘yanda za ki gaisar?
Akwai kani na abin alfahari na wato Sadik sai kuma Yaya ta Anti Mairo, Yahaya Abdullah, Usman Lamiru etc.
Me za ki ce ga makaranta wannan shafi?
Ina yi musu fatan alkhairi, su ci gaba da bin wannan shafi domin akwai abubuwan karuwa ciki.
Me za ki ce da ita kanta jaridar Leadership A Yau Juma’a?
Ina yi mata godiya bisa wannan dama da na samu, sannan ina mika sakon ta’aziyyata na rasuwar shugaban wannan gidan jarida, ina kara yi wa ma’aikatan wannan jarida fatan alkhairi da samun ci gaba.
Mun gode ki huta lafiya
Ni ma na gode.