Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Umurnin Kotu Na Yashe Asusun Tsohon Gwamna Yari

by Khalid Idris Doya
January 29, 2021
in LABARAI
3 min read
Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Umurnin Kotu Na Yashe Asusun Tsohon Gwamna Yari
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A cikin makon nan ne babban kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta bada umarnin a yashe asusun ajiyar bankunan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari da kamfanoninsa guda biyu, sai dai abun da jama’a ba su sani ba shin wasu dalilai ne suka janyo kotu ta umarci a kwashe dukiyar gami da shigarwa asusun ajiyar gwamnatin tarayya?
Kotun ta ba da umarni wa gwamnatin tarayya da ta yashe sama da Naira miliyan dari biyu da tamanin da takwas da hudu da dubu dari uku da shida da dari biyu da casa’in da hudu da kwabo hudu (N284, 306, 294.04) na tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, wanda ya tarasu a asusun ajiyarsa guda shida na bankin Zenith da Polaris.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ita ce ta bada umarnin karshe na yashe dukiyar Yarin, tare da cewa shi Yari ya gaza tabbatar da yadda ya samu kudaden ko kafin ma ya zama gwamnan jihar daga ranar 29 ga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2019.
Yari tare da wasu kamfanoni guda biyu mallakinsa da suka hada da (Kayatawa Nigeria Limited da kuma B.T. Oil and Gas Nigeria Limited) da ake zargi da tafka rashawa da har hakan ya kai gwamnatin tarayya ta hannun hukumar ICPC maka Yari da kamfanoninsa a kotu bisa zarge-zargen tafka rashawa.
Idan za a iya tunawa dai Mai Shari’a Taiwo Taiwo, a ranar 16 ga watan Agustan 2019 ya bada wani umarnin wucin gadi ga wadanda ake zargin inda ya neme su da su tabbatar da wanke kansu da tsame kawunansu daga zarge-zargen da ICPC ke musu.
Ita dai hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa gami da dangoginta ICPC, na zargin tsohon gwamnan da kwasan dukiya daga lalitar gwamnatin jihar Zamfara wanda hakan ya kasance illa sosai ga jiharsa.
Kudaden wadanda aka shigar da su ta asusun ajiya a bankuna guda biyu sun kunshi Dala 687,874.81 da kuma sama da Naira 24,289,522.89.
A sukarsa da zarge-zargen, tsohon Gwamna Yari, wanda ya samu wakilcin lauyansa Kelechi .U ESk, ya yi ikirarin cewa tun kafin ya zama gwamnan jihar shi hamshakin mai kudi ne.
Lauyan sai ya bukaci kotun da ta yi watsi da umarnin wucin gadin da ta bayar kan zargin da ake masu tun a hukuncin kotun.
A hukuncinta na karshe kan wannan batun, Ijeoma Ojukwu, ta yi tambayar cewa ta ma yaya ne zai kasance a ce daya daga cikin asusun ajiyar banki na kamfani mallakin Yari da ya kasance babu ko sisi a ciki kafin ya zama gwamna amma tun a zamanin gwamnatinsa karo na farko asusun ajiyar kamfanin aka gano Dala 301,319 a cikinsa.
Ta ce, Yarin ya gaza zuwa gaban kotun ya mata cikakken bayanin hanyoyin da ya tara wadannan kudaden, don haka tafi gamsuwa da batutuwan masu shigar da kara.
Ta ce, babu ta yadda zai yiwu Yari ya yi ikirarin kudaden ba tare da gabatar da sahihan hujjojin da suke alamta yadda ya tara dukiyar ba.
Nan take ta sanya kafa ta shure zargin da ake cewa akwai fita da kullin siyasa a shari’ar da ake masa kan zargin tafka rashaw
Don haka ne ma ta baiwa gwamnatin tarayya cikakken ikon yashe asusun ajiyar na Yarin.
“Babu wani abu na rashin daidai wajen tara makudan kudade a daya daga cikin asusun ajiyan baki amma mene ne dokoki suka gindaya a bi wajen yin kasuwanci ko samar da kudade; wadanda ake kara an ba su damar su yi cikakken bayanin yadda lamarin ya wakana, amma sun gaza gabatar da hujjojin da doka ta tanadar.
“Masu kariya sun kasa gabatar da shaidun da za su shafe bayanan masu kara a kansu.
“Wadanda ake kara sun kasa gabatar da shaidun da doka ya tabbatar wajen tara kudade a wannan kes din, don haka wannan kotun mai albarka ta yi umarnin karshe na cewa a kwashe kudaden asusun bankunan.
“Kotu ta umarci a yashe kudaden da yawansu ya kai naira miliyan 12, 912, 848.68 da aka tara ba bisa ka’ida ba a bankin Zenith Bank Plc mai dauke da sunan Abdulazeez Abubakar Yari.
“Hukuncin karshen ya kuma bada damar yashe Dala dubu $57, 056.75 da aka tara ba bisa ka’ida ba da aka ajiye a bakin Polaris mai lambar asusun ajiya… dauke da sunan Abdulazeez Abubakar Yari.
“Sannan an umarci a yashe adadin kudi da ya kai naira N11, 159, 674 .17, da aka tara ta barauniyar hanya gami da ajiye su a bankin Zenith Bank Plc…dauke da sunan Kayatawa Nigeria Limited.
“An umarci yashe adadin kudi da yawansu ya kai Dala $319, 000.91 da aka tara ba bisa ka’ida ba gami da shigar da su bankin Zenith Bank Plc…dauke da sunan Kayatawa Nigeria Limited.
“An umarci a yashe adadin kudi da ya kai naira N217, 000.04 da aka shigar ba bisa ka’ida ba a bankin Zenith Bank Plc…mai sunan B.T Oil and Gas Nigeria Limited.
“Sannan kotun nan ta umarci a yashe asusun ajiyar banki mai dauke da kudi Dala $311, 817.15 da aka tara ba ta haramtacciyar hanya a bankin Zenith Bank Plc… mai sunan B.T. Oil and Gas Nigeria Limited.”
Daga nan kotun ta umarci cewa dukkanin kudin asusun ajiyar bankin da ta umarci a yashe ta baiwa gwamnatin tarayya damar shigarwa asusunta.

SendShareTweetShare
Previous Post

Magidanci Ya Caka Wa Sakakkiyar Matarsa Wuka A Harabar Kotu

Next Post

Saboda Barazanar Tsaro Muka Sayar Da Tsohon Gidan Rediyon Manoma – Gwamnatin Kano

RelatedPosts

Ibrahim Musa Dankwairo: Sarakuna Sun Kyale Makadan Fada A Lalace

Ibrahim Musa Dankwairo: Sarakuna Sun Kyale Makadan Fada A Lalace

by Khalid Idris Doya
7 hours ago
0

Makadan Fada na yanzu sun shiga wani hali mai ban...

Yanzu-yanzu: Gwamnan Gombe Ya Nada Sabon Mai Tangale

Yanzu-yanzu: Gwamnan Gombe Ya Nada Sabon Mai Tangale

by Khalid Idris Doya
10 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa...

jana'izar

‘Yan Majalisa Biyu Sun Fice Daga APC A Bauchi

by Khalid Idris Doya
10 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, 'Yan Majalisun Dokokin jihar Bauchi biyu...

Next Post
Kananan Hukumomin Jihar Kano

Saboda Barazanar Tsaro Muka Sayar Da Tsohon Gidan Rediyon Manoma - Gwamnatin Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version