Yusuf Shuaibu" />

Abin Da Ya Kamata Mata Su Gane

Babban abin da namiji yake tunani shi ne yadda tsadar rayuwa ta dabaibaye wannan zamani na mu, masamman abin da ya shafi kudin haya, tsadar abinci, kudin makaranta da dai sauran al’amura na yau da kullum. Da zarar an ce yara za su fara jarabawa, uwayensu za su fara tunanin kudin makarantarsu in sun dawo hutu kenan, duk wanda zai yi aure dole ya duba wadannan sassan guda uku, in dai mutum ya ce zai auri bazawara a yau, kuma ya ce ba ya bukatar budurwa kila saboda sauki ne, to binciken farko da zai yi shi ne “Ta taba haihuwa? ‘Ya’yanta nawa? A ina yaran suke, a gabanta ne ko a gaban mahaifinsu?”

In ya kasance a gabanta ne suke to tabbaci za ta zo gidansa da su kenan, shi ma yana da yaran, bisa lalura dole ya kama musu wani daki idan idan ya kasance haya yake yi, kari kenan kan dakunan da tun asali yake biya. Rayuwar maraya kuma mutum bai iya ajiye abinci na shekara, sai dai a wata ya sayi buhu ko rabi, ko kuma ya rika yin awo, kenan ba sauki ka auri mace mai yara a gabanta.

Wani mutum ne kamili mai cikarkiyar kamala, ya zo neman auren wata bazawara to sai yana neman shawara sai ya tambaye wani mutum, ko tana da yara? Sai mutumin ya ce masa yaranta 3, ya ce “A gabanta suke ko a wajen mahaifinsu? Sai ya ce masa “Mahaifin ya rasu” sai ya ce ya hakura, matsalolin gabansa ma sun ishe shi. Saboda ya san za ta zo masa da yaran gidansa.

Sau daya rak na ga wani bawan Allah ya same ni yake cewa wani makwabcinsa ya rasu ya bar mata 3, ta farkon yaranta 6, ta tsakiya yaranta 4, karamar ita ce take ta yara 2, don haka ya yi kwadayin auren uwargidar don ya kwaso yaran, amma ta bugi kasa ta ce “Bat!” Ita za ta yi zaman yaranta ne. Daga nan ya koma wajen ta byun, ita ma ta ki, sai ya hakura, don dama yaran suka dauki hankalinsa saboda zaman mutuncin da ya yi da maigidansu, dalilin da ya sa ya nemi auran daya daga cikinsu kenan don ya dauki nauyin yaran, da suka ki bai ko tuntubi karamar da take da yara biyu ba, mai danyen jini ba don ba ta da yara, burinsa kuwa ya dauki nauyin yaran ne, su kuma matan sai suka yi masa wata irin fassara, irin wadannan mutanen ba su da yawa cikin wannan zamani. Ko ni wannan ne kadai na taba gani a rayuwata.

Mutum ba kin taimakon yaran wasu yake yi ba, amma shi ma yana da nasa matsalolin, ta ya ya zan dauko nauyin wasu na jibga a kaina? Mata sau tari maganarsu ita ce ba za su bar yaransu a hannun kishiyoyin su ba ko ‘yan’uwan mijinsu, domin wai kada su tagayyara. Ita shiriya ta Allah ce, za ka taras yaran da suka sha wahala a cikin rayuwarsu, su ne suke zama wani abu a gaba, duk wahalar da za su sha baya yana nufin an gama ba za su zama wani abu a rayuwarsu ba. Mace ta tsaya da ce wai ba za ta yi aure ba, zaman yaranta za ta yi. To ta sani cewa ta hana kanta aure ko kuma rashin uba na gari bai nufin shi kenan ‘ya’yanta sun gama rabauta a duniya. Duk wanda ya sake ki bar masa yaransa, in mutuwa ya yi ‘yan’uwansa su ne suke da alhakkin kula da su, in kina da hali sai ki rika taimaka musu da abin da ya samu daga gidan mijinki.

Mata Me Yake Ba Ku Tsoro?

In kina ganin cewa ba ki san namiji ba ga shi za ki yi aure, ko kin riga kin yi amma har yanzu kina fama da matsalolinsa dole ki lakanci wadannan abubuwan kamar haka:-

-Kafin ki yi aure ko bayan daura auran kar ki taba sanya wa a ranki cewa za ki sami matsala a aurenki ta kowani bangare. Indan kina tunanin cewa wada za ki aura mai fushi ne sosai sannan gashi yana yawan bata rai, ki kalle shi kawai ki kyale, a tafin hannunki yake, zai gama zafinsa ya sauko ba abin da zai iya yi. Ki tambayi tsohowar hannu ki sha labari.

-Wata siffanki ko tsarin halitta ko wata kalarki kar ki bari ta yaudare ki. Shin a wurin zabar miji ne ko kafin aure, ko wurin tafiyar da gidanki bayan kin yi auren da zarar ya aure ki ya biya bukatarsa yanzu abin da ya rage ki rataya masa dauwamammar igiyar da za ki ta jansa har karshen rayuwarku. Yanzu ba kala da kirar halitta ba ne, hidima ce da dabi’u na kwarai gami da tsoron Allah S.W.A, duk kyawun jiki da kyawun kira indai ya zama ba tsoron Allah a zuciyarki ko ba ki da ladabi da biyayya ko ya zama ba ki da gaskiya a lamuranki ko bala’i ya dabaibaye ki kullum cikinsa kike ko ba ki iya dafa abinci ba ko kuma gyaran kai a shimfida to duk kyawunki na banza ne. Abubuwan da kike tunkaho da su ba za su taba yin tasiri ba.

– Kar ki dauki maigidanki a matsayin sa’anki da za ki rika gaya masa duk maganar da ta zo daga bakinki saboda gadarar cewa kuna kwana tare a shimfida daya ko kuna cin abinci a faranti guda, bare har a sami dalilin da za ki zage shi ko ki ci kwalarsa a dalilin yana cutar dake. To ki tuna in ma rabuwa za ki yi da shi wani namijin za ki aura, kuma zai nemi sanin yadda zamanki ta kare da tsohon maigidanki. Kar ki manta ke fa mai tarbiya ce a gaban diyinki, koma zaulayar mijinki za ki yi, kin fi kowa sanin kimar maigidanki. Domin kin san kalaman da yake so da wadanda suke tunzura shi. Kar zamantakewar wata ya rude ki, ki ce kema irin shi za ki yi, kamar yadda take magana da shi, ki ce kema haka za ki yi. Kowani tsuntsu kukan gidansu yake yi. In kin fada masa kalmar da ba ta kai mutum ya hasala ba, sai ki gay a bata rai to sauko ki ba shi hakuri. Durkusa wa wada ba gajiyawa ba ce, matsalar dai ke kika fadi kuma kin janye maganarki, wani namijin yana da naci, kar ki damu ki saba da halinsa.

– Kunya abu ce mai kyau, bai yuwuwa a zarge ki da kunya, sai dai a ba ki shawarar ki rage idan ta yi yawa. ita ma in aka ga ta zarce yadda ake bukata ne, bare kuma zamantakewa wacce dole tsakanin mace da namiji akwai kwarjini wani sa’in, amma akwai bukatar fahimtar hakika. Wuraren kunya tabbas a yi, wasu wuraren kuma a kawar da su. A shekarun baya wani mutum a shafin zamantakewa na ‘Facebook’ ya ba da labarin wani dattijo da ya auro wata karamar yarinya yana tunanin ba ta san komai ba, sai ga shi ita da kanta ta fara kwance masa tazuge. A dalilin haka, kashe-gari ya ce duk diyinsa mata su fitar da miji zai yi musu aure. Dole ki ji kunyar mijinki amma wasu lokuta fuskantar hakki ita ce dadin zaman auren.

 

Exit mobile version