Abin Da Ya Sa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Ke Yin Asara, Cewar Shugaban PAN
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Ke Yin Asara, Cewar Shugaban PAN

byAbubakar Abba
2 years ago
Agricorp International decided to do something about the chicken shortage in Nigeria and is investing over 20 billion Nigerian naira (NGN 20bn) in its production. Photo: Agricorp

Agricorp International decided to do something about the chicken shortage in Nigeria and is investing over 20 billion Nigerian naira (NGN 20bn) in its production. Photo: Agricorp

Shugaban Kungiyar masu sana’ar kiwon Kajin Gidan Gona  reshen jihar Kaduna PAN Musa Bala ya bukaci masu sana’ar da ke a daukacin fadin kasar nan, musamman a jihar Kaduna da su dinga tuntubar kwararrun Likitocin Kajin kiwon Kajin Gidan Gona  a yayin da Kajin basu da lafiya.

Bala ya bayar da wannan shawarar ce a hirarsa da Leadership Hausa a Kaduna jim kadan bayan tashi daga taron bita na kwana daya da aka shirya wa wasu daga cikin masu sana’ar da ke a jihar, inda ya kara da cewa, ta hanyar tuntubar ce kawai, za su kauce wa yin asara a cikin sana’ar ta kiwon.

  • Manchester City Ta Lashe Gasar Zakarun Turai
  • Ba A Dakatar Da Mele Kyari Ba —NNPCL

Shugaban ya ci gaba da cewa,  kungiyar ta jima ta na ilimantar wa da kuma fadakar da masu sana’ar kan mahimmancin  tuntubar kwararrun Lokitocin kiwon Kajin Gidan Gona  idan Kajin sun kamu da wata rashin lafiya, musamman don gudun kar su dinga yin asara a cikin sana’ar ta su.

Ya yi nuni da cewa, idan ba sa tuntubar kwararrun Likitocin kiwon Kajin Gidan Gona, tamkar suna jefar da jarinsu da suka zuba a cikin sana’ar ce, inda kuma ya bukci su ma kwararrun  Likiticin da su dinga yin aiki mai kyua a inda aka bukace su .

” Kungiyar mu ta jima ta na ilimantar wa da kuma fadakar da masu sana’ar kan mahimmancin  tuntubar kwararrun Lokitocin kiwon Kajin Gidan Gona  idan Kajin sun kamu da wata rashin lafiya, musamman don gudun kar su dinga yin asara a cikin sana’ar ta su.”

” Idan  ba sa tuntubar kwararrun Likitocin kiwon Kajin Gidan Gona, tamkar suna jefar da jarinsu da suka zuba a cikin sana’ar ce, inda kuma ya bukci su ma kwararrun  Likiticin da su dinga yin aiki mai kyua a inda aka bukace su .”

Da yake yin tsokaci kan irin gudunmawar da masana’atar take bayarwa a kasar nan Bala ya ce, masana’antar Kiwon Kajin duk da kalubalen da take fusknata, ta na  bayar da gagarumar gudunmawa, musamman wajen daukar miliyoyin ‘yan Nijeriya aiki kai tsaye da kuma sauran miliyon ‘yan kasar da take dauka ban a kai tsaye ba , inda ya sanar da cewa, masana’atar na kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan.

“Duk da kalubalen da take fusknata, ta na  bayar da gagarumar gudunmawa, musamman wajen daukar miliyoyin ‘yan Nijeriya aiki kai tsaye da kuma sauran miliyon ‘yan kasar da take dauka ban a kai tsaye ba , inda ya sanar da cewa, masana’atar na kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan. “

Shi ma a hirarsa da Leadership Hausa bayan taron, wani kwarararren Likitan Kajin Gidan Gona Dakta James Baba Wageti ya goyi bayan ra’ayin shugaban kungiyar ta PAN, inda ya ce, duk da cewa, akwai tsada wajen dauko Likitocin na Kajin Gidan Gona da zasu duba lafiyar Kajin, amma ya bayar da shawara a dinga yin tuntubar, musamman don su kauce wa tabka asara.

A cewarsa, wasu masu kiwon Kajin Gidan Gona a kasar nan sun shiga sana’ar ce a makance, inda ya yi nuni da cewa, akwai bukatar su fahinci yadda nauyin Kajin yake kasance wa tare da kuma sa ido a kan Kajin.

Dakta James ya kuma shawarci masu kiwon kiwon Kajin na Gidan Gona da ke a kasar nan da su gabatar da rokonsu ga Majalisar Tarayyar kasar don a gabatar da kudurin da zai tsaftace fannin, musamman don a magance mutuwar Kajin Gidan Gona a kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, yawancin Gidajen Gidan Gona da ake kiwata Kajin don neman riba, na kusa-kusa da juna ne, inda y ace kamata ya yi Gidajen Gidan Gonar su kasance nesa da kilomita daya don a kare Kajin daga harbin kwayoyin cuta.

Taron bitar mai taken: “ Hanyar Yin Kiwon Kaji Mai  Ingancin”, kamfanin  Betor Libe stocks Solutions da hadakar  kamfanin Adamore ne suka shirya taron.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Manoma A Jihar Benuwe Sun Koka Kan Jinkirin  Saukar Ruwan Sama

Manoma A Jihar Benuwe Sun Koka Kan Jinkirin  Saukar Ruwan Sama

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version