Connect with us

Madubin Rayuwa

Abin Da Ya Sa Muka Kafa ‘Kotun Masoya’ A Kano – Salim Dayyib

Published

on

SALIM MUHAMMAD DAYIB, shi ne shugaban kungiyar kotun masoya, kungiyar da ta shahara wajen daidaita abokan mu’amula kan harkar soyyaya da kuma zamantakewa. Jajirtaccen matashi mai fatan ganin matasa na tafiya dai-dai da zamani musamman wajen kare harshe ta fuskar gudanar da rayuwa cikin tsafta, a tautaunawarsa da wakiliyarmu a Kano NAIMA ABUBAKAR, ya yi gudu har da zamiya wajen bayana yadda kotunsu ta masoya ke aikinta. Ga yadda tautunawar ta ka sance:

Za mu so ka gabatar wa mai karatu kanka da kanka?

Alhamdulillahi Ni Sunana Salim Muhammad Dayib, an haifi ne a cikin garin Kano a Ungwar Briged PRP Karamar Hukumar Nasarwa, a nan na ta so kuma nan na girma, na yi karatun Firamare a  Makarntar Nurul Islam daga shekarar 2000 zuwa shekar ta 2015. Daga nan kuma sai na tafi makarantar gaba da Firamare ta ‘ya ‘yan sojoji da ke Kano, daga nan na rubuta Jarrabawa na samu kyakyawan sakamako. Wannan ne ya bani damar shiga makarntar share fagen shiga jami’a dake Kano, inda na kammala cikin Nasara inda naje na yi aikin samun horo na koyarwa  a wata makaranta mai su Natsugune  dake cikin Barikin Sojoji a Kano.

 

Kasancewar ka shugaban wannan kungiya, da farko mene ne  ya ba ka sha’awa har ta kai ga samar da wannan kungiyar?

Haka ne. Alhamdullillah abin da ya bani karfin guiwa har ta kai ga kafa  wannan kungiya wadda na radawa  sunan ‘Kotun Masoyya’ shi ne, domin samar da wani dandamali wanda za mu  ci gaba da tattauna wasu batutuwa a tsakanimu da kuma samo bakin zaren warware wasu matsaloli da ke neman zame mana kadangaren bakin tulu, hakan zai taimaka wajen samun nasarori a tsakaninmu da kuma al’umma baki daya.

Wannan kungiya ba ita ce ta farko da na taba budewa  ba, akawai wata kungiya mai sunnan Hadakar tabbatar da Nasara dana fara budewa, amma ita a lokacin dana bude ta gaskiya ba ni da wata manufa kwakkwara, kawai dai mun budeta ne domin duk wanda muke ciki gaskiya ba kowa ne ya san kowa ba, kuma hasalima hirar da za ki ji ana yi a wannan dandamali ba wata hira ba ce wacce za a ce za a amfana da juna, kin san  kungiya idan ba a tsara  dokoki ba, tabbas babu yadda za a yi ita kanta kungiyar tayi tasiri. Amma cikin ikon Allah a cikin karshen shekarar da ta gabata na zauna na bude wannan sabuwar kungiyar mai sunan kotun Masoya ita ce wacce muka kafa ta akan ka’idoji.

Alhamdulillahi, gaskiya ita wannan kungiya kamar yadda kika tambaya haka ne babu yadda za a yi ka kafa kungiya babu tsare-tsare, wannan ta sa a wannan karon muna da tsare-tsare na musammman ga duk wasu mambobi da ke cikin wannan kungiya.

Daga cikin tsare-tsaren mu akwai cike takardar shaidar shiga cikin wannan kungiya wadda ke dauke da ka’idoji da kuma tsare tsaren wannan kungiya, a cikin wannan kungiya ba a turo hoto ko wane iri, idan ana gabatar da shirye-shiryen mako ko ka shigo ba za kayi magana ba har sai mai gabatarwa ya kammala, ba a aika sako a wannan kungiya ma’ana (boice note) sannan kuma wani ba zai dauki lambar wani ko wata ba tare da izinin mai lambar ba, muna da ka’idoji da dama gaskiya a wannan gida namu.

 

Ta ya kuke samun mambobi da ke sha’awar shiga wannan dandamali?

Tsarin yadda muke samun mambobi a wannan kungiya tamu shi ne akwai wadanda suke ciki kuma sun yi na’am da duk wasu abubuwa na wannan kungiya, gamsuwa da tsare-tsarenmu ke basu sha’awa su gayyato wasu rukunin al’umma da muke fahimta iri guda wadanda su ma suka yi na’am da su suka kuma aminta da cewa duk wata doka za su iya aminta da ita wannan gida, saboda haka sai ka ga sun zo sun sayi  takartar shiga anyi masu tambayoyi, idan sun cika sharuddan shiga sai a basu dama kasancewa mambobi da haka muka samun mambobi.

 

Shin maza ne kadai a cikin wannan kungiya, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da kuke tattaunawa akan su domin neman mafita ko har da mata?

Allahamdulillah. Kamar yadda aka sa ni babu yadda za a yi tafiya irin wanann a ce maza ne kawai a ciki irin wannan kungiya, saboda babu shakka a cikin wannan kungiya akwai maza da mata duk suna cikinta kuma kowa na bayar da gudunmawa gwargwadon iko. Wannan tasa kungiyar ke kara bunkasa ako da yaushe. Ka san irin tafiya kokari ake a samar da jama’a mabanbanta hange da kuma fahimta iri daban-daban, ta haka ne duk wani abu da ya ta so ake tunkarar sa kuma a samu nasarar shawo kan al’amarin cikin kankanen lokaci.

 

A lokuta da dama, jama’a kan yi wa irin wannan dandamali wata irin fahimta inda ake yiwa duk mambobin da ke cikinta wani irin kallo na zargi, shin ku mene ne ya bambanta ku da wadanda za a iya yi wa wannan kallon na zargi?

Gaskiya ne mu namu irin tsarin muna da kyakkyawan tanadin mutunta juna da kuma yin taka-tsantsan da duk abinda ka iya zubar da kimarmu. Wannan tasa kamar yadda na fara ambata cewa mu a namu tsarin ko hoto ba a turawa ko kalaman batsa, sannan muma da cikakken tsarin baiwa  kowa dama matukar bai ketare iyaka ba. Wannan ta ba mu damar mu’amilla da mutane masu hangen nesa da kuma kyakkyawar tarbiya.

Duk da muna mu’amilla da matasa masu karancin shekaru amma wannan bai bayar da damar wuce gona da iri ba, kowa ya san matsayinsa, muna kuma yin iyakar iyawarmu wajen taka burki ga duk wanda muka fara hangen rashin sanin ya kamata ta fuskarsa domin kauce wa zama wake daya da ka iya bata mana gari. Don haka kafin shigo da kowa cikin wannan kungiya sai mun tabbatar da ingancin tarbiyarsa da kuma mutuntakar sa.

 

Mene burin wannan kungiya na gaba?

Babban Burin mu shi ne samar da wani dandamali da za a iya amfani dashi wajen aika duk wani sakon wanda ke cike da kyawawan bayanai wanda al’umma za su amfana, wannan tasa nan gaba kadan za mu samar da wani tsari na gabatar da tambayoyin da muka tabbatar za su amfani jama’a. Wadanda muke amsar su mu bayar wadanda ba mu sani ba za mu yi kokarin isar da su ga manyan malamai da masana domin yi mana fashin bakin domin amafanin jama’a.

Haka muna da niyyar samar da wani tsari na fadakar da ‘yan uwa karin hanyoyin dogaro da kai domin kauce wa mummunan halin da wasu ‘yan siyasa ke jefa matasa aciki. Sannan kuma muna da aniyar samar da wani dandamali wanda duk ke bukatar a zabe shi kan wani mukami za mu gayacce shi cikin wannan shiri domin yi wa jama’a bayanin abin da ke cikin zuciyarsa wanda yake ganin idan an zabe shi zai aiwatar wa jama’a na alhairi.

Saboda haka za mu nuna wa matasa sanin darajar kimar da Allah ya yi masu wanda a lokuta da dama ake amfani da su wajen aikata wasu ayyuka marasa kyau, sannan kuma muna shirin fadakar da ‘yan matasa maza da mata illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da dangoginsu, sai kuma amfani da duk damar da muka samu domin bibiyar abubuwan da ‘yan siyasa ke cewa sun samarwa jama’a mu bayyana masu gaskiyar al’amarin domin auna kowa da irin halinsa.

 

Mene ne sakon ka na karshe ga matasa musamman wadanda ke cikin wannan kungiya da kake shugabanta?

Na gode kwarai da wannan  tambaya, musamman kasancewar matashi dan’uwana zai fi fahimta bayanin da muke yawan yi masu, da farko dole matasa mu farka da dogon barcin da ke neman zame mana illa babba, haka kuma ya zama wajibi matasa maza da mata su tashi tsaye wajen neman na kansu, a daina dogara da gwamnati domin yaudarar kai ne a ce wai jiran gwamnati muke ta samar mana da dukkan abubuwan da muke bukata. Don haka ya zama wajibi mu tashi domin yiwa kanmu da kanmu fada ta hanyar shiga cikin sana’u iri daban-daban.

Sannan ina kira ga muhukunta da ‘yan siyasa da su dubi Allah wajen sauke nauyin da Allah ya dora masu, wannan ne zai samar da cigaban da muke fata a kasar nan, sannan kuma a karshe ina kara mika godiya ta musamman ga mambobin wannan kungiya wadanda muke wannan aiki ba dare  ba rana domin kawo sauyi cikin zantuka da kalamanmu musamman kan abubuwan da muka dauka a matsayin soyayya. Na gode kwarai da gaske
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: