Shehu Bello, jami’i ne da ke kula da yadda ake tara kudin shiga a bangaren sayar da rasidin ababen hawa masu haya da Babur mai kafa uku da motocin Bas da ke zirga-zirga cikin gari a yankin Unguwannin Mando da yankin hayin Rigasa, ya shaida wa manema labarai a Kaduna cewa gazawar masu haya da Babura mai kafa uku ya sa gwamnati ta ba su aikin kulawa da sayar da tikiti domin a samu nasarar aikin tun a matakin karamar Hukuma.
Shehu Bello ya bayyana cewa hakika akwai wani lokacin da aka kira taro domin tattaunawa da shugabannin ‘yan kungiyar masu haya da motoci da masu haya da Babura.
Ya ce, “a wajen taron an tambayi masu haya da motoci ko za su iya sayar da rasidi na ababen hawa da za su rika tara harajin gwamnatin a kullum, suka ce za su iya, amma da aka tambayi masu haya da Babura mai kafa uku sai suka ce su gaskiya ba za su iya ba, wannan ta sa aka dauki aikin aka ba su daga matakin karamar Hukuma. Da wannan muke ce masu Allah ya saka masu da alkairi bisa irin kokarin da suke yi a kullum.”
Ya kuma shaida cewa suna yin aiki tare da tsare ka’ida da girmama kowa ba wata matsalar hayaniya, balantana a samu rashin jituwa da wani ko wasu, kuma suna gudanar da aiki ne daga safe zuwa karfe sha biyu, sha biyu da rabi sun tashi sai kuma Gobe.