Connect with us

ADON GARI

Abin Da Ya Sa Na Fi Ba Da Karfi A Girke-Girke Fiye Da Sauran Sana’a – Bilkisu

Published

on

Girke-girke adon mata, duk macen da ta ba ta iya girki ba da sauranta. Bakuwarmu ta wannan makon, mace ce da ta taso tare da son girke-girke kuma da alama za a iya cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu, kasancewar a duk sana’o’in da take yi babu wata ta fi mayar da hankali sosai a kai kamar girke-girke. Ba ta tsaya koyon girki irin namu na gida ba, ta tsallaka har zuwa wurin Turawan Faransa domin koyon wasu sababbin girke-girken. A karanta hirar a ji har karshe a ji abubuwa na karuwa kan girke-girke da kuma sauran harkoki na rayuwa kamar haka:

 

Da farko masu karatu za su so sanin sunanki da dan taklkai taccen tarihin ki…

Da farko sunana Bilkisu Hussein an haifeni A kano na girma a Cotonou, Jamhuriyar Benin, a nan na yi karatuna na gama na dawo Kano inda nake yanzu.,

 

A yanzu a wanne bangaren kike kamar aiki ko karatu, sana’a, kuma a wani mataki kike, ko zaman gida kike?

Eh to gaskia yanzu bana karatu zaman gida nake sai dai abun da ba a rasa ba muna yin kasuwanci kala kala, kamar irinsu kwalliya da gyaran gashi amma na fi karfi a harkar girke girke da sauransu har kayan sawa irinsu atamfofi daga Cotonou da kananan kaya da takalma da jakunkuna da sauransu.

 

Masha Allah! Bari mu dau fanin gyaran gashi mai  karatu zai so jin shin kina da “saloon” ne?

Eh Sister na ce ta bude saloon inda muke aiki tare tana makeup sosai nima ina dan tabawa in aiki ya yi yawa kamar ana bikunkuna da tarirrika muna zuwa har gida munamyi maka.

 

Ya yi kyau hakan, kamar na so na ji kin ce fanin girke-girke  ko za ki mana bayanin yadda wannan lamarin yake?

Yawwa gaskiya ni dai inda na fi karfi kenan wajan girki, na ta so tun ina karama da son girki mukan dan yi jagwalgwalo, kuma da na taso a Cotonou na ga yayata ita ma tana son girki to a wajanta na koyi wasu lokacin Ina karatu danagama naga ba abunda nake sai zaman banza sai kawai na ringa sha’awar koyar cake din yana burge ni sosai lokacin a Kano ba kowa ke yin cake a Kano ba lokacin 2013 daga baya na tilasta wa kaina na, na biya kudi a wani restaurant na ‘yan France na koyi cake da snacks na wajan wata 4, bayan na gama na dawo gida sannan na koma Cotonou 2017 na sake koyan girki a wani hotel 5star inda na koyi girki na tsawon wata2, daga nan ne na ci gaba da sana’ar abinci da cake da snacks.

 

Masha Allah! Shin ko akwai kalubale da kike ko kika taba fuskanta gun koyon wannan sana’a?

Eh to da farko na samu mutane suna ta kalubalantar abun sun zaci kawai bata lokacina nake sai daga baya da suka ga irin yadda abun yake sai mutane suka ringa sha’awar abun sosai har da wasu suka ba da kudi nake koya musu don ina koyarwa a gida da kuma online classes duk ina yi ko da azumi ma ina yi, sai dai in ce Alhamdillah.

 

A baya kin ambaci kamar kikan koya wa mutane masu sha’awar irin wannan sana’a taki? Shin ko kina da wata hanya ta zahiri ko ta kafar sadarwa da kike koyar da wannan sana’a?

Eh ina yi sosai sabida na koyawa mutane da dama abinci da snacks kuma Masha Allah mutane da dama sun sami karuwa wasu har sun fara yin nasu na siyarwa wasu kuma suna yi a gida kuma sun ji dadin hakan.

 

Masu karatu za su so jin me ya taba faruwa dake a rayuwa ta farin ciki ko akasin sa da ba za ki taba mantawa ba?

Gaskiya abubuwa da dama sunfaru da ni masu dadi da marasa dadi kuma in dai kana rayuwa a duniya dole ka fuskanci abubuwa daban daban na game da rayuwa mai kyau da mara kyau, dama Allah shi ba wanda ba ya jarabta a duniya sai dai muce Allah ya yi mana karshe mai kyau ya kuma sa mana albarka a rayuwarmu.

 

Ko kina ganin akwai wata hanya da gwamnati za ta iya shigowa cikin irin wannan sana’a taku dan ba da gudunmawa ko taimako?

Sosai ma kuwa abin da ya kamata gwamnati ta ringa taimaka wa mutane ballantana wanda suke son koya amma ba su da karfi kin ga in gwamnati ta taimaka musu suka koya kin ga su ma sun samu abin da za su rike kansu zai amfani su da iyalensu da sauran al’umma da ke kewaye da su ballantana bangaren abinci, abun yana da mahimmanci ga al’umma baki daya.

 

Wace gudun mawa kike da ita da za ki iya ba wa al’umma wadda za su amfana?

Gaskiya ba abun da zan ce wa mutane ballantana mata irina da kar su dogara a jiran sai wani ya basu da su tashi su samu abun da za su yi amfani da kansu don gudun wulakancin dan Adam.

 

Wacce shawara za ki bawa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum wanda idan suka yi koyi ko amfani da ita, rayuwa za ta inganta?

Kamar yadda na fada a baya kar ka taba kasawa kullum kasa a ranka za ka iya kuma ka sa a ranka Allah yana tare da kai don shi kadai ne mai taimako, ba wani ba in dai ka yarda da Allah da hakuri a kan komai to rayuwarka za ta yi daidai, Insha Allah.

 

Masu karatu za su so jin ko kina da aure ne?

[Dariya] Gaskiya ban da aure kuma ban taba yi ba sai dai a kullum addu’a nake kar na mutu ban yi ba don rashin yinsa na damuna sai dai na bar wa Allah komai, don shi ke tafiyar da rayuwar mu kuma sai yadda ya yi da mu haka za mu kasance ba wai wayonka ba sai dai in ce Allah ya sa mu dace.

 

Hakane Allah Ubangiji ya kawo miji na gari. Ko akwai abunda kike son fada ko shawara ga matasa mata ‘yan uwanki ko wani abu da bamu tambayeki ba kike son fada?

Babu

 

Masha Allah! Adon Gari nagodiya da kasancewarki da mu cikin wannan shiri a nan zamu saka a ya, ki huta lafiya.

Wassalamu alaikum, ni ma Ina godiya ku huta lafiya sai wani lokacin in da rabo.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: