Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Na Kyamaci Fita A Bangaren Rawa A Fina-finai – Yusuf Muhammad

by
4 months ago
in NISHADI
7 min read
Rawa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Shafin Rumbun Nishadi na wannan makon ya zakulo muku wani fitaccen Jarumin kuma shahararre wanda tauraruwarsa ke haskawa a yanzu cikin masana’antar Kannywood wato YUSUF MUHAMMAD ABDULLAHI wanda aka fi sani da YUSUF SASEEN ko kuma LUKMAN cikin shirin Labarina. Babban jarumin ya bayyana wa masu karatu dalilin da ya sa ya shiga masana’antar shirya fina-finan hausa, ya kuma yi bayani game da abin da ya shafi sana’arsa ta fim. Ga dai yadda tattaunawarsa ta kasance tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko masu karatu za su so sanin cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi… Assalamu alaikum, Sunana Yusuf Muhammad Abdullahi, wanda aka fi sani da Yusuf Saseen wasu kuma sun fi sanina da Lukman a cikin shirin Labarina.

Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? Takaitaccen tarihina Yusuf, an haifeni a unguwar gini garin ‘Kano Municipal’, wadda aka fi saninta da Kwalli, na yi makaranta a gidan Makama ‘Special Primary School’, daga nan kuma na wuce sabuwar kofa ‘K.Nassarawa Rumpa College’ inda na kammala a ‘airport road’. Bayan na gama ‘Secondary School’ dina ne kuma na tafi zuwa ‘Bayero Unibersity’ na yi ‘diploma’ akan ‘Management’. Daga nan kuma na samu aiki da ‘Horizon Hotel’ bayan ‘Horizon Hotel’ kuma daga nan na wuce boko ‘Benue state’ na yi ‘Pedia Poly Technic’, daga nan kuma na wuce ‘Benin Republic’ na je na yi karatun digiri dina inda na kammala B.Sc a ‘Business Admin’. Bayan na gama wannan kuma na wuce ‘Nassarawa State Keffi’, a can na je na yi ‘NYSC’ dina. Bayan na kammala kuma ni ‘Member’ ne na ‘Chartered Institute of Managrment and Leadership United State’. Sannan kuma ni Memba ne a ‘Social of Financial Institutions in Nigeria’, da dai sauransu

Labarai Masu Nasaba

Waka Da Gamon Jini Ne Silar Alakata Da Ambasadan TikTok Abis Fulani – Maryam

Tsokacin Nafisa Kan Yaran Da Ke Gararamba A Titi: Alarammomi Sun Karrama Naziru

Da kyau! Wace irin rawa kake takawa a masana’antar Kannywood? Rawar da nake takawa a masana’antar Kannywood Jarumi ne, sannan kuma ta wani barin furodusa ne ni, ko na ce ‘Edecutibe Producer’ dan dukka ina tabawa, ina ‘acting as actor’ sannan kuma ina ‘Edecutibe Producer’. Saboda ina sawa a yi inbesting, kuma ana shiga da ni a yi tsare-tsaren yadda za a yi, sannan kuma ina fitowa matsayin Jarumi, ‘Three in one’ kenan.

Gaskiya ne, toh me ya ja hankalinka har ka karkata ga shiga masana’antar kannywood? Abin da ya karkatar da hankalina har na yi sha’awar shiga masana’antar fim, bayan na yi karatu ina ganin cewa Kannywood wani wuri ne wanda za ka iya isar da sako sosai, sabida in ki ka duba ‘Followers’ din da suke da shi a ‘Instagram’ kadai sai ka ga Kannywood suna da falowas wajen mutum Milyan talatin in ka lissafa, kama daga taurari maza da mata da kuma wanda suke aiki da sauran ma’aikatansu in ka hada yana ‘accumulating’ za ka ga ya tafi wajen milyan talatin ko milyan arba’in ma, toh a nan za ka iya aikawa da sako a ce mutum milyan ashirin za su ga sako daya a ciki, ka duba kawai ko zabe na kasa sai ka ga mutanen da ake yin zaben su ma ba sa kai wa milyan ashirin din, wanda za ki ga da total bote din da aka yi zabe a ciki, toh ashe lallai Kannywood idan suka hade kansu za su iya aikawa da sakon da ransu ke so su gyara al’umma, shi ya sa na ga cewa wani guri ne da za ka iya amfani da shi ka baza hajarka ka yi ‘business’ ka samu na halak sannan ka taimaki al’umma da shi.

Wannan shi ne dalilin da ya ja ra’ayina na ga ya dace na ce nima na zo na yi sana’ata a gurin kuma na taimaki al’umma. Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance, ganin yadda wasu ke kuka da shiga masana’antar cewar sai mutum ya zuba kudadensa sannan zai samu damar karbuwa har ya yi fice, wasu ma na ganin ko da akwai kudin sai mutum ya dan wahala kafin ya samu shiga masana’antar, shin kai ma ka fuskanci irin wannan kalubalen wajen shiga ko ya abin ya kasance? Toh! Ni dai ban sha wahala ba, kuma ai ba Kannywood ce kadai haka ba, ita kanta rayuwa kowa da yadda kaddararsa take zuwa, wani za ki gani a ‘School’ ne zai sha wahala, wani kuma za ki gani ya zo kawai ya wuce ya tafi, itama haka Kannywood din take yadda duk yanayi na rayuwa yake haka take itama. Toh! amma dai ‘from my side’ ni dai gaskiya ban sha wata wahala ba, kuma ban fuskanci wani kalubale ba, ni ne ma na yi deciding din fim kawai, na yi tunani ya kamata na shiga ina shiga kuma na yi fina-finai daya, biyu, uku, shi ne sai dama ta zo min nake ganin Labarina ya zo da dai sauransu, wannan shi ne.

Toh ya batun iyaye fa lokacin da ka kai musu labarin kana son shiga masana’antar, shin ka fuskanci wata matsala daga gare su? Eh! Toh, Lokacin da na yi tunanin na shiga fim gaskiya na mallaki hankalin kaina, ni ban shiga fim ina dan mitsitsin yaro ba, sai da na kammala digiri dina ma kuma na yi tunanin kawai ya dace na shiga, dan a lokacin ma ‘Dad’ dina ya rasu sai mahaifiyata, lokacin na je na fada mata, nake fada mata mahimmancin abun, da kuma irin tarbiyya da na samu daga gurinta, da kuma gidan da na taso duk wani abu na Allah wadarai ni ba zan yi shi ba, abin da na sani kawai ni zan yi sana’a wadda ta yi dai-dai da hankali da kuma addini da al’ada, sai dai dan Adam kuma tara yake bai cika goma ba, amma dai Allah ya san zuciya dai-dai gwargwado ana kamantawa, ni ban samu matsala da ita ba, da na fada mata dai ta ce toh Allah Ubangiji ya ba da sa’a. Dan ina jin duka-duka ban cika shekara daya ba mahaifiyata ta rasu. Wannan shi ne dai abin da na sani sai dai abin da ba a rasa ba a ‘yan uwa a ce ya za ka ja abin kunya, za ka yi wannan, ana ta tofa albarkacin baki, toh irin wannan dai bai wuce surutu ba, wannan shi ne.

Daga lokacin da ka fara fim kawo i-yanzu za ka yi kamar shekara nawa kana yi? Lokacin da na fara fim zuwa yanzu an tafi shekara hudu kenan zuwa biyar 2017, mun shiga 2022 shekara hudu kenan zuwa biyar. A wanne fim ka fara fitowa, kuma wanne rawa ka taka cikin fim din? A fim din da na fara fitowa wani fim ne sunanshi ‘WANI KWARTO’ na Nazifi Asnanic wanda Sani Yari ya yi furodusin, shi ne na fara zuwa na yi, da na yi shi sai kuma ‘CANFI’, wancan ‘Wani Kwarto’ ni na fito da wata mata da nake soyayya da ita wadda ban san matar aure ba ce a gidanta nake zama.

Shi kuma Canfi matata na canfa nake tunanin cewa ita take kawo min karayar arziki, shi ne na sake ta na kirawo Sadik Sani Sadik a matsayin abokina, na biya shi dan ya aureta ya saketa na aura ya ki daga baya, wannan shi ne. Ko za ka iya tuna yawan adadin fina[1]finan da ka fito ciki? Kai! (Dariya) ba zan iya tunawa ba wallahi, suna da yawa.

A gaba daya fina-finan da ka fito ciki, wanne fim ka fi so kuma wanne ne ya fi shahara cikinsu? Toh! a gaba daya fina-finai dana fito sun kasu kashi biyu, akwai ‘Series film’ akwai kuma ‘Feature Film’ wanda ake, toh gaskiya a Siris dai ba kamar Labarina, sannan ga Sirrin Boye, sannan ga LUKMAN siris dina kuma wanda nawa ne nan ba da dadewa ba zai fara zuwa da kuma Suna da Yawa a cikin fim shi ma siris ne, wanda za su rinka zuwa a ‘YouTube Channel’ mai suna EGF Hausa TB, akwai fina-finai masu kyau fa sosai amma dai wanda na fi so, ya fi birge ni kuma ya fi shahara shi ne Labarina.

Za ka ga wasu Jaruman sun fi karkata ga fina-finan barkwanci, wasu kuma na soyayya, wasu na siyasa da sauransu, shin kai wanne ka fi maida hankali akai? Ni babu fim din da idan ya fito ba zan yi shi ba ciki, fim din da kawai ba zan yi ba a ciki wanda ya saba wa addini ko al’ada, ko na barkwancin ne ya samu dama in dai akwai ‘role’ dina a ciki zan yi shi, ko na siyasa ko na soyayya ‘in short’ dai ni kowanne bangare zan yi, ‘role’ din da ba zan yi ba kawai a ciki soyayya wadda ba irin tamu ba, a ce soyayya ta rawa.

Idan na fahimce ka kana so ka ce ba ka sha’awar abin da ya shafi bangaren rawa kenan? Eh! Abinda ya shafi bangaren rawa ba na son shi gaskiya, ba kuma wani dalili bane illah ilimina ne dai karami, ban sani ba ko kuma akwai inda ilimi zai zo in waye tare da shi, a cikin iya fatawa dana samu kafin na fara fim na yarda da cewa fim sana’a ne, kuma sannan duk inda yake akwai musulmai da kuma mazahabobi kala-kala na addini da garuruwa na musulmai su Iran, Irak, Saudiya, Dubai, ba inda ba su da ‘yan fim, ashe fim din ba shi ne mara kyau ba, yadda za a tafi da fim din toh! A nan ake samun rashin kyansa. Toh! gaskiya ni dai a yadda na ga waka akwai hadisai wanda suke magana a kan fitar tsiraici, to ka ce a fim macen babu ko kuma akwai ana dai kokari a gyara ganin cewa mata sa suturta kansu.

Hadisi na magana a kan cewa su mata masu dame jikinsu fitet kaya wannan ko kamshin aljannah ma ba za su ji ba, ita kuma rawa da waka tana tafiya da dame jiki da gantsare jiki da dai sauransu, toh ba mamaki ilimi na ne bai je ba, ni dai a yadda nake ganin ta kamar babu kyau kuma “be side” ma a al’adance ni ba al’adar bahaushe ba ce raye-raye da irin wannan a ciki, gaskiya wannan yana daya daga cikin abin da ya sa na kyamaci ma rawa da waka a cikin fim sabida Allah, gaskiya nake jin tsoro sabida wancan hadisin da yake magana a kan dame kaya ga mace ita kuma wakar ba yadda za a yi ta ba tare da gantsare-gantsare ba in dai da rawa, gantsare-gantsare yana fitar da tsiraici.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

´NILEST` Ta Yi Bikin Yaye Nakasassu Da Aka Horas Sana`o`i

Next Post

Gwamna Matawalle Ya Yi Kiran Sake Sabon Salon Yaki Da ‘Yan Bindiga

Labarai Masu Nasaba

Waka Da Gamon Jini Ne Silar Alakata Da Ambasadan TikTok Abis Fulani – Maryam

Waka Da Gamon Jini Ne Silar Alakata Da Ambasadan TikTok Abis Fulani – Maryam

by Rabi’at Sidi B.
6 days ago
0

...

Nafisa

Tsokacin Nafisa Kan Yaran Da Ke Gararamba A Titi: Alarammomi Sun Karrama Naziru

by Rabi’at Sidi B.
3 weeks ago
0

...

Zarah Ummarou

Muhimmancin Hada Kan Jaruman Fim Na Kano Da Nijer —Zarah Ummarou

by Rabi’at Sidi B.
4 weeks ago
0

...

Fim

Akwai Bukatar Gwamnati Ta Sanya Hannu Sosai A Harkar Fim —Amina Abubakar

by Rabi’at Sidi B.
1 month ago
0

...

Next Post
Yaki

Gwamna Matawalle Ya Yi Kiran Sake Sabon Salon Yaki Da 'Yan Bindiga

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: