Connect with us

LABARAI

Abin Da Ya Sa Na Saduda Da Takarar Shugaban Kasa –Fayose

Published

on

Gwamnan jijar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyan dalilan da suka sanya ya janye daga hankoron meman shugabancin kasar nan a shekarar 2019.
Gwamnan mai barin gado ya yi wannan bayanan ne a garin Ado Ekiti ranar Juma’a, yayin da yake karbar bakoncin dan takarar shugabanciun kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, wanda ya isa jihar on neman goyon bayan wakilan jam’iyyar daga jihar a traron fida gwamni na jam’iyyar da ake shirin gudanarwa kwanan nan.
“A matsayi na shugaba na kwarai bai yi wu in bar mataimaki na da jam’iyyar APC ta kwace wa mulki zuwa neman wani matsayi ba,” inji Mista Fayose.
“Postan da na buga na na a cikin daki a iyen abin dake gaba na a hakin yanzu shi ne kokarin kwato mulkin da aka sace mana.”
A watan Satumba 2017 ne Mista Fayose ya aiyyana kudurinsa na takarar shugabancin kasar nan a wani taro a Abuja, in da ya yi alfaharin cewa, lallai ba abin da zai hana shi zama shugaban kasar nan a zaben shekarar 2019.
Ya kuma sha alwashin kada shugaba Buhari a zaben da za a gudanar.
“Na gaiyato ku ne a yau, shugabanin jami’yyarmu don in sanar da ku cewa, zan tsaya takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, ina wannan ne don tabbata da ci gaban jam’iyyarmu.”
“Amma da yake ni mutum ne mai son ganin an samu sabbin hannu da kuma matasa a harkar tafi da kasar nan musamman ganin irin halin da kasar ta samu kanta na halin kakani kayi.
“Abu mai mahimmanci a halin yanzu shi ne jam’iyyarmu ta mika takarar shugabancin kasa zuwa yankin arewa, kuma bai kamata a roki wani ya zo ya yi takarar ba sai wanda yake da ra’ayin yin takarar da kansa, wanda yake da jam’iyyarmuna cikin zuciyarsa.
“Muna nuffin kenan in har babu wanda ya fito daga arewa ba zamu tsayar da dan takara ba kenan?”
A bayaninsa ranar Jumma’a, gwamnan ya ce, kasancewar Kwankwaso ya shi go jam’iyyar PDP ya nuna cewa, lallai shugaba Buhari ba shi da karfin ci gaba da mulkin kasar nan ken an.
Sanata Kwankwaso na daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP dake neman a tsayar dasu takarar shugabancin kasa nan a zaben dake tafe.
Mista Fayose, ya kuma tunatar da cewa, a lokacin da ya yi wannan maganan a kan rashin iya mulkin Buhari, kwamkwanso na daga cikin wadanda suka mayar masa da kakkausar amsa.
“Amma ina godiya ga Allah da ya sa har ka gane gasikya ka dawo jam’iyyarmu ta PDP.
“A shekarar 2015 lokacin da Buhari ke yawon nem,an zabe, na ui bayanin cewa, Buharin ba zai iya mulki ba, duk inda ya ui muliki mataimakansa ke gudanar da mulkin a madadainsa, mutane suka ce wai me Fayose ke fada haka? amma gasi Allah ya gaskata ni kowa ya ga gaskiya..”
Gwamnan ya kuma ce, bai kamata jam’iyyar APC ta dauki Buhari a mastayin dan takara ba, saboda ba zai yi kasuwa ba, in day a kwatanta sji da “black market.”
Daga nan Mista Fayose ya bukaci ‘yan jam;’iyyar PDP su zabi dan takara na kwarai wanda ‘yan Nijeriya za su zaba a zaben shekarar 2019.
“Dole mu fuskanci wannan yaki a matsyin tsitsiya madauruki daya, wannan wani gargadi ne ga sauran ‘yan takara, lallai muna son dan takarane da zamu mika wa ci gaban kasar nan gaba daya cikin aminci da klwanciyar hankali,” inji shi.
A jawabinsa, Sanata Kwankwaso, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya anince, jam’iyyar APC babbar kuskure ne, kuma tun da farko bai kamata a zabi Buhari a matsayin shugaban kasa ba.
“Dukkanmu muna sane da halin da kasar nan ta shiga sakamakon wannan canji da muka dauko wa kanmu, na yi matikar takaicn wannan kuskuren da aka yi, saboda haka dole mu hada hanu mu gaggauta canza wannan canjin,” inji shi.
“da gudummawarku tare da na sauran jama’a PDP za ta kora jam’iyyar APC a 2019, mu kafa gwamnatin tarayya.
“Na zo jihar Ekiti neman goyon bayanka tare da goyon bayan wakilai daga wannan jihar, muna sane da matsallolin da kasar nan ke fuskanta, ina kuma da kwarin gwiwar zamu iya maganin dukkan matsalolin da kaar nan ke fuskanta kamar dai yadda muka yi a lokacin da nike mulki a jiharb kanbo.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: