Ga dukkan alamu Nijeriya za ta sake fuskantar karancin albasa a wannan shekarar ta 2022, sakamakon wasu matsaloli da suka dabaibaye harkokin noman albasar.
Shugaban Kungiyar Manoma da ‘Yankasuwa da Masu Sarrafa Albasa ta Nijeriya (NOPPMAN) Alhaji Isah Aliyu Binji ya bayyana haka wata tattaunawa da LEADERSHIP Hausa, jim kadan bayan kammala taron shugabannin kungiyar na kasa da ya gudana a zauren taro na NBC da ke Titin Lusaka a Unguwar Zone 6 a Abuja.
A ta bakinsa, “Muna kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) bisa ga alkawarin da ya yi mana na cewa zai ba manoman albasa bashi su noma albasa saboda manoman albasa sun dauki noma a matsayin sana’a.
Tun asali, tun fil’azal babu mai noma albasa don ya ci shi da iyalansa kawai, duk mai noma albasa don sana’a yake yi. Saboda haka yana da kyau Babban Bankin Nijeriya ya kama mana.
“Muna tunanin za a samu karancin albasa a wannan shekara ta 2022 saboda a wannan wata na biyar da muke ciki ya kamata ya zama ana sayar da albasa (buhu) dubu shida zuwa dubu bakwai amma abin mamaki yanzu albasa tana dubu 17 zuwa 18 a Arewa, a Kudu kuwa tana kai sama da dubu 20 amma muna tunanin cikin watan bakwai da takwas da kuma ember months (watanni hudu na karshen shekara) za a fuskanci wata ‘yar girgiza a harkar albasa saboda za a zo ana neman albasa da kudi amma a samu matsala. Muna kira ga gwamnati ta bai wa manoman albasa bashi don su yi noman damina saboda a rage radadin da za a ji na karancin albasa a wannan lokacin.”
Da aka tambaye shi ko akwai wata dabara da suke kokarin yi domin saukaka radadin karancin albasar a lokacin da ya ambata, Binji ya amsa da cewa, “akwai baturen da kila kun gan shi a wannan taron namu, ya zo mana da wani tsari na ajiye albasa na zamani. Wannan zai sa a rika tanadinta da kuma rage asarar da ake yi daga kashi 50 a cikin dari zuwa wata kila kashi 10.
Idan manomi yana noma albasa buhu 100 sai ya zama buhu 50 na lallacewa, ka ga ko wannan yana kara haifar da matsalar karancin albasa, amma idan aka samu igantaccen wajen ajiya, albasar da muke nomawa za ta kara yawa.”
Har ila ya kara da cewa suna sa rai idan har an yi amfani da dama ta noman damina, ana iya rage radadin karancin albasar da za a samu a watannin karshen shekarar.
Wakazalika, da yake tsokaci a kan babban taron nasu na shugabanni na kasa, Alhaji Aliyu Binji, ya ce taron ya ba su damar tattauna nasarorin da suka samu da kuma kalubalen da suke fuskanta na noman albasa a Nijeriya.
“Mun yi magana a kan kudin shiga da kungiya ta samu a cikin wata biyar da kuma ayyukan da muka gudanar.
Sannan mun gabatar wa mahalarta taron kalubalen da aka fuskanta kuma aka lalubo hanyoyin magance su.
Lallai kwalliya ta biya kudin sabulu. Abubuwan da muka sa a gaba yanzu su ne yadda za a bai wa manoman albasa bashi don su noma ta.
Sannan mun samar da tsari na ajiyar albasa da zai rage yawan asarar da ake yi.
Haka nan mun tattauna da Hukumar Inshora ta NAIC domin ganin ana yi wa kayan gonakinmu inshora saboda in aka samu ibtila’i ya kasance gwamnati ta shigo ciki domin taimaka mana game da matsalar da aka samu”.
Taron dai ya samu halartar wakilin ma’aikatar bunkasa ciniki da masana’antu ta tarayya da shugabannin rassan jihohi na kungiyar na kudu da arewa wadanda suka rika gabatar da jawabai kan abubuwan da suka shafe su, yayin da shugaban kungiyar na kasa ke bayar da amsa daya bayan daya.
Nijeriya dai ta taba fuskantar karancin albasa a shekarar 2019 da 2020 lamarin da ya sabbaba dan karen tsadar albasar.