Abin Da Ya Sa USAID Ta  Zuba Jari A Fanin Noma

Daga Abubakar Abba

A bisa kokarin bunkasa tattalin fannin tattalin arziki da fannin noma na zamani hukumar samar da ci gaba ta kasa da kasa ta kasar Amurka (USAID)  ta  kaddamar da zuba jarin dala miliyan 60 har na tsawon shekaru biyar don zuba jari a fannin kasuwanci a nahiyar Afirka da kuma bunkasa fannin noma a Nijeriya.

A cewar hukumar ta (USAID)  hakan zai kuma samar da ayyukan yi sama da sababbin ayyuka guda 40,000.

har ila yau, hakan zai kuma taimaka wajen samar da hanyoyin yin kasuwanci a saukake a fanin aikin noma.

A jaabin sa a wurin kaddamarwar d aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja Jakadan Amurka a Nijeriya Mary Beth Leonard ya sanar da cewa, Nijeriya ta na da kasar yin noma da za’a iya zuba dimbin jari mai yawa.

Jakadan Amurka a Nijeriya Mary Beth Leonard ya ci gaba da cewa, muna nunawa bukatar mu ta kara zuba jari a fanonin tattalin arziki da kuma fannin noma a Nijeriya ta hanyar tattaunawa ta kasa da kasa.

A cewar Jakadan Amurka a Nijeriya Mary Beth Leonard, a yau muna bikin kara karfafa zuba jari da kuma a fannin kasuwanci, mummman ganin cewar kasar Amurka ta kasance wadda ta zuba jari mai dimbin yawa a Nijeria.

Harkar ta hanyar kasauncin biyu, ta kai tad ala biliyan 10 a duk shekara.
Ministan ma’aikatar noma da raya karkara  Alhaji Sabo Nanono wanda ya samu wakilicin Mojisola Odusoye, a wurin taron ya yi kira gay an Nijeriya dasu yi amfani da damar wajen habaka fannin aikin noma, musamman don su ragewa kawunan su radadin talauci da kuma kara inganta rayuwar su.

A wata sabuwa kuwa, akwai alamun da nuna cewa, akwai fata na gari a fannin noma Ruber a Nijeriya bayan da masu ruwa da tsaki a fanin suna nuna cewar a shirye suke su farfado da fannin, inda a jihar Koros Ribas, aka kbe kadadar yin noma 15,000 don noman Rubber a jihar.

kungiyar masu sarrafa rubber ta kasa ce ke shirin yin noman na rubber inda aikin zai kai tswon shekaru 10 ana gudanar dashi,, inda aikin ya hada da shuka sabbin irin yayan  rubber.

Shugaban kungiyar ta NARPPMAN reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kaddamar da kungiyar ta kananan ukumomi dake a a cikin jihar ta Koros Ribas da aka gudanar a garin Kalaba.
A cewarsa, kirkiro da kungiyar ya zama wajibi idana akayi la’akri da irin dimbin mahimmancin da noman rubber yake dashi.

Shugaban Rabaran Inameti ya ci gaba da cewa, a bisa la’akarin da akayi na ganin masu ruwa da tsaki a jihar ta Koros Ribas wajen mayar da hankali kan farfado da noman rubber a jihar.

Exit mobile version