Abin Da Za Mu Yi Da Tubabbun Boko Haram – Zulum

Zulum

Sakamakon maganganun da jama’a ke yi musamman a yankin Arewa game da karbar tuban Boko Haram, Gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum ya yi jawabi ga manema labarai kan yadda za su yi da mayakan Boko Haram da suke tuba inda ya bayyana matakan da za su dauka a tubabbun mayakan da mutanwen gari da kuma mayar da wasu zuwa cikin al’umma

Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu mayakan Boko Haram sama da 2500 da ‘yan kai ne suka mika wuya ba tare da tsangwama ko takura ba, wanda ko shakka babu hakan wata ‘yar manuniya ce da ke nuna alamun samun nasarar yaki da yi da ; yan kungiyar.

“Dalilin da ya sa ka za mu karbi tuban wadannan mutane shi ne, akwai mata a cikinsu masu rauni, sanna kuma wasu kuma kananan yara ne da sace su aka kai su can dajin tun suna da shekara biyar da haihuwa har suka girma aka koya musu wannan abu, akwai kuma wadanda ba yaran bane amma ba jin dadin aikata wannan aiki suke ba, to idan ka ce ba za ka yafe musu ba ya za aka yi da su. Don haka za mu duba kuma mu tantance, kowa daidai da laifin da ya aikata, wanda ya cancanci hukunci a yi masa, sannan wadanda za’a sake su sai a san inda za a kai su,” in ji shi.

Da aka tambaye shi game da zargin da wasu ke yi na ko gwamnatinsa ta ba wa wadannan tubabbu wani abu ne domin shawo kansu, sai ya yi rantsuwa da cewa ko sisin kwabo basu ba wa kowa ba, “Wallahi ba kwa bina bashin rantsuwa babu wanda muka ba wa ko kwabo ba, sun mika wuya ne bisa radin kansu, kuma ko ana tsaka da yaki mutum ya ajiye makamansa ya kan samu rangwame, amma hakan ba ya nuna za mu bar abin ya tafi haka bane, don haka mutane su sani bamu ba da kudi don wani ya tuba ba kuma nan gaba ma ba za mu bayar ba wannan ita ce matsayar gwamnatin Borno.

Kuma yakamata mutane su fahimci wani abu, wannan aikin fa ya fi karfin gwamnatin jiha dole sai Gwamnatin Tarayya ta shigo ciki, bayan wadannan tubabbu fa kada a manta akwai Sansanin ‘Yan Gudun Hijira su ma ana nan ana ta kula da su, saboda hakan abin ne ya yi yawa shi ya sa muka yanke shawarar karbar su gami da amincewa da tubansu, abin da zai biyo baya nan gaba kuma wannan Allah ne kadai ya sani, domin shi ne masanin gaibu. Saboda haka duk wanda ya ajiye makamansa ya zo ya mika wuya za mu karbe shi, wanda kuma ya ki, to zai hadu fushin sojoji a daji da kuma ‘yan kungiyoyinmu na sa kai, wannan ita ce maganar gaskiya,” in ji shi.

Exit mobile version