Yarjejeniyar Daina Kisa Mu Ka Cimma Ba Ta Garkuwa Ba, In Ji Su
Daga Hussaini Baba, Gusau
Abin jiya ya dawo jihar Zamfara, inda a ranar Alhamis da misalin karfe tara na safe ne gungun mahara su ka kai hari ofishin Hukumar Kare Hadura ta Kasa da ke karamar hukumar Tsafe cikin jihar Zamfara su ka harbi rot kwamanda mai suna Mubarak Hamza, wanda nan take ya ce ga garin ku nan, kuma su kai awon gaba da abokin aikinsa mai suna Muhammad Muhammad Birnin Kudu su ka shiga daji da shi.
Bugu da kari, maharan sun shaida wa dangin wasu matan Fulani da a ka kama cewa, ba a yi yarjejeniyar daina kama mutane tsakaninsu da jami’ai ba, illa dai ancimma matsaya a kan cewa, za su daina kashe mutanen da su ka kama ne kurum. To, amma har yanzu ba a tabbatar da dalilin da ya sa a wannan karon su ka bindige jami’in tsaron ba.
Aminu Abubakar Yashi ya bayyana ma wakilin mu cewa, sun tambaye su cewa ba an yi sulhu da su ba? sai maharan su ka ce mu su sulhun kisa ne a ka yi da su ba na sata ba. Donn haka sun dai na kisa, sai idan tsautsayi ya gita.
Jami’n hulda da jama’a na Hukumar Kare Hadora ta jihar Zamfara, Nasiru Ahmad, ya tabbatar da faruwar wannan abu kuma ya shaidama manema labarai cewa, “Hukumar da rundunar ’yan sanda na kokarin gano jami’insu da a ka yi awon gaba da shi.”
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne rundunar ’yan sandan jihar karkashin jagorancin Kwamishinan Shaba Alkali ta samu nasarar kwato jami’anta uku da maharan su ka yi awon gaba da su a Keta da ke karamar hukumar Tsafe cikin koshin lafiya.
Haka kazalika ma al’ummar Zamfara ba su manta da wani sabon salon da su maharani su ka fito da shi ba na satar mutane da yin garkuwa da su, sai su ka sace Sarki Maidaraja ta Biyu a jihar, watau Sarkin Bukuyum, wanda su ka iske shi har fadarsa kuma su kai awon gaba da shi.
Shi ma mataimakin shugaban karamar hukumar Anka masu Ggarkuwar sun yi awon gaba da shi har sai da ya yi kwana da kwanaki, sannan su ka dawo da shi bayan sun ja milyoin Nairori.
Wasu kansilolin har da manyan mutane ma ba su bar su ba da ’yan Kasuwa sama da mutum 40 da su ka yi garkuwa da su duk a cikin wannan shekarar.
Salon satar ya sa masu garkuwa da mutanen su ke bukatar milyoyin Nairori kafin sun fito da mutanen da su ka sata. Kuma ya sa dole ’yan majalisun jihar da kwamishinoni da masu mukaman siyasa su ka kaurace ma kauyukansu da gonakinsu, don gudun fadawa tarkon masu garkuwa da jama’a a watannin baya.