Daga Idris Aliyu Daudawa
Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya wata jarabawa wacce malaman makarantun Firamare 21,780 daga cikin 33,000 suka faɗi. Ita dai wannan jarabawar da suka rubuta, irin wacce ake yi wa ’yan aji huɗu na Firamare ne.
An bayyana maƙasudin jarabawar a matsayin wata hanya ta son gane kaifin hazaƙa da fahimtar da malaman makarantun Firamaren Jihar Kaduna.
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a shekaran jiya, yayin da ya amshi baƙoncin wasu jami’an Bankin duniya (IMF), a ziyarar da suka kai zuwa jihar.
Hakanan da akwai matsalar Malami da ɗalibi a makarantun ƙauye saboda wasu makarantu ana samun yawan malaman bai dace ace suna wurin ba. A wasu Ƙananan Hukumomin ana samun Malamai 1 na kula da ɗalibai 9, wasu kuma Malami 1 shi ke kulawa da ɗalibai100.
Ya cigba da cewar a wani matakin da aka ɗauka na maido da martabar ilmi Darektocin makarantu, sun yanke shawarar sa ‘ya’yansu a makarantun gwamnati, wannan kuma za a fara ne daga shekarar karatun da ake ciki.
Shi ma da yake jawabi mai wakiltar Bankin duniya kuma shugaban tawagar Kunle Adekola, ya nuna jin daɗinsa, akan yadda jihar Kaduna ta maida hankalinta wajen kawo gyara a harkar ilmi, ba musamman ilmi’ya’ya mata, ya ƙara da jaddada cewar jihar ta nuna shirin basu haɗin kai, domin su cimma burinsu.
Ya ce, Bankin duniya ya bada tallafi na Naira milyan 30 a makarantar Firamare ta Rigasa, wadda take da ɗalibai 22,000, a matsayin gudunmawar da ta ba jihar.
Sashen bada tallafi a ɓangaren ilmi na Bankin duniya da sauran wasu mataimaka domin kawo ci gaba, tana bada taimako ne yanzu a jihohin Arewa waɗanda suka kai kusan 13, da kuma jiha ɗaya daga kowane sashe daga cikin sassa shida da ake da su a Nijeriya.