Umar A Hunkuyi" />

Abin Kunya Ne A Bari Kungiyoyin Kwadago Su Koma Yajin Aiki – Usmaniyya

Babban abin da ba a so shi ne a ce ma’aikata sun shiga yajin aiki, domin in aka ce an fara shiga yajin aiki, tabbas abu ya lalace. Na farko an ji kunya a kasar gaba-daya, domin wannan umurni ne da Shugaban kasa ya bayar cewa ya yarda, ya kuma aminta da a fara biyan wannan sabon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 30,000, Shugaban kasa da kansa ya fadi hakan kuma duk duniya ta ji, sannan kuma a ce har yanzun ba a fara biya ba, babu wata jiha ko wata hukuma ta gwamnati da ta fara biya, to ka ga a nan har aka ce ta kai a halin yanzun kungiyoyin kwadago sun fara bayar da wa’adin komawa cikin yajin aiki a kan dai wannan batun, to ni a gani na wannan abin kunya ne kuma sam bai dace ba.

A nan muna yin kira ne ga Shugaban kasa da ya tilasta wa dukkanin Jihohi, ma’aikatu da sauran hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta fara aiwatar da wannan doka ta biyan sabon tsarin albashi da aka aminta da shi na naira dubu 30,000. Domin in har aka ce kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki a kasa irin Nijeriya ko da na yini guda ne, ba fa karamar asara ce za a yi ba, wacce za a gwammace da gara ma a ce a biya kudaden da wannan asarar ta yini guda, ballantana ma a ce an sami kwanaki ana gudanar da yajin aiki, tabbas hakan abin kunya ne wanda kuma sam bai dace a bari hakan ta faru ba.

Shi ya sa muke dada yin kira da babbar murya ga Shugaban kasa da ya tilastawa dukkanin Jihohi da ma’aikataun gwamnati da daukacin hukumomin da suka wajaba da su fara biyan wannan kudaden na sabon mafi karancin albashi na naira dubu 30,000 kafin kungiyoyin kwadagon nan su kai ga fantsama a cikin yajin aiki. Domin shiga yajin aikin nan yana janyo masifu da bala’o’i ne masu yawa, zai kuma shafi kowane sashe da bangare na rayuwar al’umma wanda hakan kuma ya zama abin kunya ne ga Nijeriya. Saboda haka muke nanata yin kira ga Shugaban kasa da ya hanzarta daukan matakin da ya dace na ganin an fara biyan wannan sabon tsarin albashin na naira 30,000, wanda shi da kansa ne ya sanya hannu ya kuma yi umurni da a fara biyansa, tun kafin kungiyoyin kwadago su shiga wani yajin aikin kuma.

Exit mobile version