Rabiu Ali Indabawa" />

Abin Mamaki Game Da Wani Gini Mafi Tsawo A Duniya

Shi dai tarihin dogwayen gine-gine za a iya bin diddiginsa tun shekaru daruruwa ko ma a ce dubbai da suka wuce, lokacin da makera da kuma maginan asali suka fara yin kokarin gina dogwayen gine-gine Mahadi ka ture. Kama dai daga kan Dalar Giza ta kasar Misra, har zuwa kasaitaccen ginin hasumiyar birnin Dubai wanda yanzu haka ake tsaka da gininsa.

Tun shekaru da dama da suka gabata lokacin da aka fara samun ci gaba a bangaren fasahar gine-gine, masana ilimin zanen gine-gine suka rika zane da kuma kirkirar samfuri daban-daban na dogwayen gine-gine, kama dai daga ofisoshi na ma’aikatu yadda za su dauki ma’aikatu da dama, har ya zuwa otel-otel da Asibitoci da kuma Gidajen Tarihi.
Har ila yau kuma sakamakon juyin zamani da yanayin muhalli da kuma bukatun al’umma ya sa tsarin dogwayen gine-gine yake kara zama ruwan dare gama duniya.
To idan kuwa ana batun gini mafi tsawo a duniya sai a ce, ginin hasumiyar birnin Dubai da ke hadaddiyar daular larabawa, shi ne gini ma fi tsawo yanzu haka a duniya, kuma kasancewar ba a kammala shi ba tukuna, ana kara bayyana shi da cewa shi ne gini ma fi tsawo da aka sani zai tabbata a nan gaba. In da yanzu haka shi wannan gini ya kai hawa 145 kamar dai yadda maginan suka bayyana. Kuma in ban da shi, ba bu wani gini a doron duniyar nan da ya kai hawa 145.
An dai fara gina wannan hasumiya ta birnin dubai a ranar 21ga watan Satumba, 2004. Kuma an kammala shi a shekara ta 2009. Inda an kammala shi din, an tabbatar da ya kasance yana da sama da hawa 160.

Exit mobile version