Akwai wasu nau’oin abinci da a haka, wadanda ba za a yi tunanin cin su na da hadari ba amma akwai wasu abubuwa a cikinsu da suke da hadari
A haka, ana iya cewa babu wani hadari a tattare da abinci.
Amma maganar gaskiya ita ce, ba ko wanne abinci bane ake ci ba tare da daukar mataki ba, kamar dubawa da kyau, ko wajen dafawa ko shiryawa – kamar cire wasu sassan jikin abincin da ke iya cutarwa.
Idan ba a dauki wadannan matakan ba, akwai nau’in abincin da idan aka ci yana iya janyo cuta, kuma alamomin cutar na iya zama tashin zuciya ko gushewar hankali ko ma mutuwa.
Ga nau’in abinci biyar da ya kamata a duba sosai kafin a ci. Asali ma, idan ba ku da tabbas kan wadannan nau’oin abinci, bai dace a ci gaba daya.
1 .Kifin Puffer:
Kifin Puffer mai hadarin gaske shaharraren abinci ne a Japan
Kifin Puffer na iya kisa.
Yana dauke da sinadarin ‘tetrodotodin’, wani sinadari ne mai guba wanda ake tunanin ya fi sinadarin ‘cyanide’ hadari.
Sai dai duk suna da hadari, ana matukar son cin Kifin Puffer a wasu kasashen.
Ana horar da masu dafa abinci tsawon shekaru kafin a ba su damar dafawa mutane kifin.
Abin dubawa anan shi ne a tabbatar cewa kafin a fara ci, sai an cire duka sassansa masu dauke da guba, wadanda suka hada da kwakwalwarsa da fatarsa da idanun sai kuma kayan cikinsa.
Abin da ya sa wannan abincin ya fita daban shi ne ya kunshi tsutsotsi.
Wannan na iya sa wa a ji kyama, amma wannan cikwi din dan asalin garin Sardinia, na Italiya na da masoya da yawa.
Ana hada wannan cukwi din ta hanyar hada tsutsar kuda a cikin cukwi din ‘pecorino’, wani nau’i na cukwi mai kama da cukwi din ‘permesan’.
A hankali, kananan tsutsotsi na sa cukwin ya yi laushi yadda idan aka zuba a kwano za a ci, cikinsa ya zama ruwa-ruwa.
Cukwin Casu marzu yana da dandano na musamman saboda kanshin tsutsotsin.
Kafin a ci shi, sai an dauki wasu matakai.
Daga farko, sai mutum yana da hanzarin kama tsutsar saboda kuwa tana iya tsalle kamar na tsawon sentimita 15- idan ana cin cukwin.
Cukwin Casu marzu na da dandano na daban saboda kanshin tsutsotsin da suke cikinsa
- Ganyen Rhubarb:
Ana amfani da tsinken ganyen rhubarb sosai misali a girke-girken kasar Birtaniya.Abinci da yawa a Birtaniya yana dauke da shi.
Sai dai kuma dole a kula saboda koren ganyen rhubarb na dauke da guba.
Babban abin shi ne yana kunshe da sinadari mai guba da ake kira ‘odalic acid’, wanda idan aka ci shi da yawa yana janyo tashin zuciya da duwatsun koda.
- Jan wake da waken soya:
Ana ganin wake a matsayin abinci mai inganta lafiya, amma akwai wani nau’insa da idan ba a kula ba, yana iya haifar da rashin lafiya.
Jan wake da waken soya na cikin wannan nau’in.
A wani bangare, suna dauke da sinadaran ‘protein’ da ‘bitamin’ masu gina jiki.
Amma kuma, danyen wake yana dauke da wani irin mai, mai suna ‘phytohaemagglutinin’ wanda jikin dan Adam ba ya iya sarrafa shi.
Cin sa da yawa na janyo ciwon ciki da haraswa.
Abin farin ciki shi ne dafa waken sosai yana kawar da wadannan abubuwan.
Waken soya kuwa na dauke ne da wani sinadari mai guba mai suna ‘trypsin’, wanda ke iya hana jikin mutum sarrafa abincin.
Amma idan aka jika wadannan nau’uka na wake a ruwa tsawon awa 12, sannan a tafasa su hakan yana kawar da wannan sinadari.
- Gyadar Miya:
Gyadar miya na iya gusar da hankali idan aka ci ta da yawa
Wannan wani nau’i ne na kayan kamshi daga wata bishiya a kasar Indonesiya.
Tana da muhimmanci sosai wajen dafa wasu nau’ukan abinci kamar biskit da kunu.
Baya ga haka, ana amfani da gyadar miya wajen dafa dankali da nama da miya da ganyaryaki.
Sai dai kuma idan aka sa ta da yawa tana janyo abubuwa masu yawa tashin zuciya da daukewar numfashi har ma da suma- da kuma gushewar hankali.
Da wuya, rashin lafiya dalilin cin gyadar miyar (nutmeg) da yawa ya jawo kisa amma tana wahalarwa.
Amma me ma zai sa mutum ya ci kayan kamshi haka da yawa a lokaci guda? To, an dade dai ana amfani da gyadar miya a wajen gusar da hankali.
Sai dai idan aka yi la’akari da abubuwan da suke jawowa, babu ma amfanin cin gyadar ya wuce kima.