Connect with us

CIWON 'YA MACE

Abincin Buda-baki Mai Sauki Ga Iyali

Published

on

Masu karatu tare da sallama mafifiya, Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barkanmu da Azumi Ibadar Allah, da fatan yadda muka ga farkonsa lafiya, Allah ya nuna mana karshensa lami lafiya.
Bayan haka, ‘yan’uwana mata, shin wadanne irin nau’in abinci kuke shirya wa iyalinku na buda baki? Ku biyo ni ku ji yadda za ku yi.

Iyaye mata yana da kyau mu sa ni a cikin wannan yanayi da muke ciki, wanda aka tsare magidanta daga fita neman halal, ba mu da wani zabi illa mu yi amfani da duk abin da ya sauwaka kuma mu godewa Allah a kan hakan.
Kar mu damu da sai mun yi soye-soye, saboda azumin bara mun yi. Mu sani azumin bana ya zo da abubuwa kala-kala wanda muke fatan ganin wucewarsa da yardar Mai Duka.

Yana da kyau ku sama wa iyali kunun Couscous a lokacin buda baki. Abin da ake bukata kalilan ne wanda ba sai an wahala matuka ba. Za ku sa mu:

Couscous
Madara
Sukari
Lemon tsami
Idan kuna da madarar gari za ku dama da ruwa, ya zama ruwan sanwar kunun, daidai yadda Cous cous din zai nuna da kyau ba ya yi kauri kamar tuwo ba. Idan ruwan madara ta tafasa sai ki juye couscous dinki ki yi ta gaurayawa har ta nuna ta yi kaurin da kike so, in ta yi kauri sosai kina iya kara ruwa don ta sake. Ki sauke ki zuba lemon tsami kadan, sai sukari kadan, ba ya bukatar sukari mai yawa, domin idan ya yi yawa zai kashe gardin madarar.
Ki samu farar shinkafa da miya a matsayin abincin dare. Hakika iyalinki za su yi farin ciki da haka, har da Maigida ba tare da an bata kudade wurin soye-soye ba.
Idan madarar ruwa muka tanada, a tabbatar sai bayan an sauke kunun sannan za a zuba madarar ruwan.
Mu sha ruwa lafiya, Allah ya karba mana ibadunmu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: