Bayanai na cewa, a kasar Sin, a duk inda ka ga mutane, to za ka ga abincin gargajiya iri na gundumar Sha, kamar yadda mataimakin darektan cibiyar raya sana’ar samar da abincin gargajiya ta gundumar Sha Zhang Xin ya bayyana, kawo yanzu gaba daya adadin dakin cin abincin gargajiya na gundunar Sha a fadin kasar ya kai sama da dubu 88, kuma adadin kudin da aka samu daga sayar da abincin ya zarta kudin Sin yuan biliyan 50.
Gundunar Sha tana birnin Sanming na lardin Fujian na kasar Sin, tun zamanin baya, ‘yan kasuwa suna tururuwan zuwa wurin, abin da ya sa ake kiran sa da sunan “gundumar rairayin zinari”.
A farkon shekarun 1990, tsohon darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Yubang na gundumar Sha Yu Guangqing ya kafa wani kantin sayar da abincin gargajiya na gundumar Sha a birnin Fuzhou, fadar mulkin lardin Fujian, a kai a kai abincin ya samu karbuwa matuka, saboda abincin yana da dadi kuma ba shi da tsada.
Daga baya dakin cin abincin gargajiya na gundumar Sha ya samar da abinci iri hudu wadanda suka fi samun karbuwa, alal misali, jiaozi da aka turara, da abincin da aka tafasa cikin karamar tukunyar tangaram, da abincin wonton, da gaurayar taliya.
A ranar 8 ga wata ne, aka shirya bikin nuna al’adun yawon shakatawa a gundumar Sha, inda aka baje kolin nau’ikan abincin gargajiya sama da dari daya domin mazauna gundumar da masu yawon shakatawa su dandana.
Yanzu haka abincin gargajiya na gundumar Sha ya bunkasa cikin sauri.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hasua)