Rabiu Ali Indabawa" />

Abinda Buhari Ya Fada Wa Mambobin Kwamitin ECA A Ganawarsu Ta Farko

A ranar Laraba ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da mambobin sabon kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (ECA) da ya kafa a fadar gwamnatin tarayya, Billa, da ke birnin tarayya, Abuja. Yayin ganawar ta su, shugaba Buhari ya jaddada kudirin gwamnatinsa na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10. Shugaba Buhari ya shaida wa mambobin kwamitin ECA cewa, tattalin arzikin Nijeriya ba ya bunkasa kamar yadda ya kamata tare da sanar da su cewa yana bukatar su yi amfani da gogewarsu da iliminsu wajen zakulo hanyoyin da za a inganta tattalin arzikin Nijeriya a cikin gida. “Ina son yi muku godiya bisa amincewarku domin hidimtawa kasa. Akwai aiki mai muhimmanci a gabanku. Burin mu shi ne tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekaru 10.

“ Tabbas mun fita daga matsin tattalin arziki, amma har yanzu tattalin arzikin mu ba ya bunkasa ta yadda za mu samu sukunin cimma muradun mu “A cikin gida ya kamata mu nemo hanyoyin inganta tattalin arzikinmu, ta yadda zai dace da tsarin kasar mu. Dole mu samar da wasu hanyoyi a cikin gida da zasu bunkasa tattalin arzikinmu. Ina jira da sauraron shawarwarinku a kan yadda za mu iya cimma hakan. “Dukkan ma’aikatan gwamnati masu nasaba da aikin ku za su iya gana wa da ku domin tattauna wa a kan yadda za ku iya taimaka musu,” a cewar shugaba Buhari.

Exit mobile version