A ranar 25th ga watan Disamba ne mabiya addinin Kirista a Nijeriya, su ka bi sahun sauran miliyoyin ‘yan uwansu da ke a fadin duniya domin gudanar da shagulgulan bikin Kirismeti da na sabuwar shekara.
Bikin ya kuma jefa murmushi a fuskokin masu sayar da Kaji da ke a kasar nan, ganin cewa, sun ran samun riba mai dimbin idan za su sayar Kajin na su a lokacin.
Mafi yawancin masu kiwon Kajin, musaman wadanda su ke kiwata Kajin gidan gona domin sayar wa a lokacin bikin na Kirismetin da kuma bikin sabuwar shekara, sun samu kudaden shiga da ya wa.
Sai dai, a wannan shekarar, wasu masu kiwon Kajin ba su samu wata ribar a zo a gani ba, saboda ganin cewa, su na hakilon ganin sun sayar da Kajin nasu, saboda farashin Kajin ya yi tsada matuka, musamman saboda yadda farashin abincin Kaji ya yi tashin gwaron zabi.
A bisa wani bincike da aka gudanar a wasu manyan kasuwanni da ke kasar nan, ya nuna cewa, farashin Kajin gidan gona ya kai kimanin kashi 100, inda hakan ya nuna karuwa kan farashin Kajin da ya kai kusan kashi 100 bayan da masu sayar da Kajin su ka yi ta fama da tashin farashin abincin Kajin na gidan gona tun a farkon wannan shekarar.
A cewar wani karamin mai sayar da Kajin na turawa Austin Ben ba kowa ba ne ke da niyyar sayen Kajin kan farashin naira 5,000 ko wacce daya ba, inda ya kara da cewa, wasu masu sayen za su iya sayen Kajin da farashinsu bai wuce naira 3,500 kuma ‘yan kadan ne su ka iya sayen Kajin kan farashin naira 4,500.
Ya ci gaba da cewa, bayan sayar da Kajin kan dan karamin farashi, hankali na ya tashi matuka, musamman idan nayi la’akari da irin yawan kudaden da na kashe wajen kiwonsu da saya masu abinci kuma bayan na auna, naga na samu ribar naira 5,500 ce kacal.
Har ila yau, a jihar Lagos an ruwaito cewa, an samu banbancin farashin na Kajin a wasu manyan kasuwannin da ke jihar, kuma farashin ya danganta ne kan yadda girman Kajin su ke.
A wajen kiwon Kajin na Noiler da ke a rkunin gidaje a anguwar Jakande da ke a Isolo, an sayar da Kajin na gidan gona kan farashin naira 6,000 na kowacce Kaza daya, inda kuma aka sayar da wasu kan farashin naira 4,000 zuwa naira N5,500 haka an kuma sayar da wasu kan farashi daga naira 2,200 zuwa naira and 2,500.
Bugu da kari, a wasu wuraren a jihar, an kuma sayar da Kajin kan farashin naira 5,000 ko wace Kaza daya, inda kuma aka sayar da wasu kan farashin naira 7,000.
Wani mai kiwon Kaji a yankin Epe da ke a jihar Folake Aina ya sanar da cewa, babu wani mai kiwon Kajin da yake yin murna a wanann shekara, domin mafi yawancinsu sun yi asara, inda ya alakanta hakan kan tashin gwaoron zabin abincin Kajin na gidan gona.
A kasuwar Oregbeni a jihar Edo kuwa na ruwaito cewa, farashin Kajin ko wacce daya ya karu daga naira 7,000 zuwa naira 9,000 haka an kuma sayar da wasu kajin kan naira 3000 zuwa naira 4000 wasu kuma kan farashin naira 4,000 zuwa naira 5000.
Labarin ma haka ya ke a Benin, Aduwawa da a babbar kasuwar Ekiosa Satana, inda wasu Kiristoci su ka koka kan tashin farashin na Kajin.