Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya (RIFAN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Numbu, ya yi nuni da cewa, kashi 70 zuwa 80 na al’ummar Nijeriya sun dogara ne da noma domin gudanar da rayuwar yau da kullum,
Alhaji Muhammad Numbu ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a jihar Kaduna, inda ya ci gaba da cewa, gwamnatoci a dukkan matakai da cibiyoyin hada-hadar kudi da kamfanonin da hukumomin da suka shafi harkar noma da manoman kansu da sauran masu hannu a harkar suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tafiyar da harkar noma da kiwo a kasar nan.
Ya yi kira ga manoman shinkafa su kara tashi tsaye wajen inganta harkar noma tare da biyan rancen da gwamnati ta ba su don bunkasa noman shinkafa, a matakin da ta dauka don karfafa gwiwar manoman.
Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Numbu ya yi nuni da cewa, Jihar Kaduna ta noma shinkafar da za ta iya ciyar da fadin jihar da kuma kasa baki daya.
Ya ce sirin nasarar noman shinkafar shi ne yadda suka yi amfani da ingantaccen iri da kuma maganin kwari da suka raba wa manoma rance, abin da ya ce ya sa noman ya yi matukar kyau a jihar.
Shugaban kungiyar Manoman Alhaji Muhammad Numbu ya bayyana cewa, duk wanda ya biya rancen da aka ba shi za mu kara masa fiye da abin da aka ba shi da farko, inda ya kara da cewa, idan mutum ya karbi rancen da ya noma hekta daya ne za mu ba shi wanda zai noma na hekta biyu nan gaba, amma idan ya dawo da shi.
Ya ce bayan cin nasarar rancen farko sun sake karbar na biyu wanda suke fatar samun abinda suke so, don haka ya kara nanata kira musamman ga manoman shinkafa daga Kudancin Kaduna su yi kokari su biya bashin da ake bin su don fitar da shi kunya tunda shi ma daga yankin ya fito.
Yayin da ya waiwaya kan matasa, ya gargade su da su rabu da bangar siyasa ko jiran ayyuka masu maiko, maimakon haka, su shigo cikin wadanda za su amfana da bashin noman shinkafa don kama harkar noma ce za ta fisshe su saboda irin alherin da ke cikinta.
Ya sanar da cewa, a yanzu ana shirye-shiryen wani sabon rancen ne tare da hadin kan Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Bankin Manoma (BOA) da bankin Unity Bank wanda hatta sababbin manoma na maraba da su domin cin gajiyar rancen da manufarsa ita ce bunkasa noman shinkafar da kasa za ta rika dogara da ita da kuma fitar da ita zuwa kasashen waje, kuma hakan na bukatar karin manoman shinkafa a Nijeriya baki daya.
Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Numbu bisa namijin kokarin da suke nun awa tare da bayar da goyon baya don bunkasa noman shinkafa don cimma burin Nijeriya a harkar noma a duniya.
Ya ce, akwai bukatar gwamnatoci da cibiyoyin kudi su kara azama ta fuskar samar da kudaden tallafi ga harkar noma da zimmar kawo gagarumin sauyi don cimma muradun da ake so a bangaren.
Ya ce, shirin na da alfanu sosai, inda kuma ya yi nuni da cewa, sai dai a bayyane yake cewa, har yanzu akwai bukatar gwamnati ta kara matsa kaimi sosai ta wasu fuskokin da suka shafi noman kai-tsaye.
Ya ce Nijeriya ba wai tana da karfin da za ta iya ciyar da kanta kawai ba ne; har ma tana da karfin wadata dukkan kasashen da take makwabtaka da ita a yankin yammacin Afirka; amma abin takaicin shine ita ma tana dogaro ne da shigo da mafi yawan abincinta daga ketare.