Mataimakin Darakta na sashen ayyukan gona na ma’aikatar nona da raya karkara Malam Isa Adamu ya sanar da cewa, ma’aikatar na son a noma amfanin gona a kasar da taking gargajiya wanda da ba a yi ma sa wani gauraye da sanadaran yin noma na zamani ba, musamman da suka bazu a yankin Arewa Maso Gabas.
Ya sanar da hakan a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Abuja.
Ya ce, “Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya ta sanar da cewa, ta na son a noma amfanin gona a kasar noman da ba’a yi amfani da sanadaran yin noma na zamani ba, musamman da suka bazu a yankin Arewa Maso Gabas.”
Mataimakin Darakta na sashen ayyukan gona na ma’aikatar Malam Isa Adamu wanda ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Abuja ya ci gaba da cewa, tron na shekara-shekara na kasa, an shiyar shi ne kan yin amfani da takin gargajiya don noman kasuwanci (NOABS) a Nijeriya.
Mataimakin Darakta na sashen ayyukan gona na ma’aikatar Malam Isa Adamu wanda ya wakilci Uwargida Igoh Janet Mataimakiyar Darakta ya ce, ana noma kayan lambu da dama a Arewacin Nijeriya da takin gargajiya.
A cewar Mataimakin Darakta na sashen ayyukan gona na ma’aikatar Malam Isa Adamu, mu na son aikin ya shiga jihohinin Borno, Sokoto, Kebbi, Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna da kuma sauran jihohin da ke a cikin Arewacin Nijeriya kamar yadda ake yinsa a Kudancin kasar nan.
Mataimakin Darakta na sashen ayyukan gina na ma’aikatar Malam Isa Adamu yabi gaba da cewa, Ma’aikatar ta Aikin Noma da Raya Karkara, ba wai tuna nuna ban-banci kan sauran dabarun yin noma na zamani bane.
Shi kuwa Farfesa Bictor Olowe, daga Jami’ar Aikin Noma ta Tarayya dake a garin Abeokuta kuma Shugaban Kungiyar masu noma da takin gargajiya ta kasa AOAPN ya bayyana cewa, a fadin duniya, a na yin amfani da yin noma da takin gargajiya dake lashe dala biliyan 100.
Farfesa Bictor Olowe ya kuma sanar da cewa, duk da yadda girman Afirka take ba ta iya bayar da gudunmawar da ta kai sama da kashi uku na dala biliyan 100 ba, inda ya yi nuni da cewa, akwai bukatar Nijeriya ta rungumi fannin, Inda Farfesa Bictor Olowe ya kara da cewa, Nijiriya ta na da masu samar da takin na gargajiya da dama, inda Farfesa Bictor Olowe, daga Jami’ar Aikin Noma ta Tarayya dake a garin Abeokuta ya yi nuni da cewa, idan masu yin amfani da takin na gargajiya da kuma masu samar da shi da ke a kasar nan su ka rungumi wannan fannin, zasu samu judaden shiga masu dimbin yawa daga amfanin su da su ka sayar da takin na gargajiya.