Mukhtar Zailani" />

Abinda Ya Sa Hon. Bello Kumo Ya Ciri Tuta A Siyasar Gombe

Hon. Bello

Irin girman tasirin da Jagorori suke yi a fannonin rayuwa a kullum za ka ga ya ta’allaka ne da irin manyan nasarorin da suka samu a fannin da suke taka rawa. Hakan ne kuma ke jawo musu biyayyar mutane da fata na gari saboda irin sikkar da suke da shi a kansu.

Honorabul Usman Bello Kumo, Ciyaman na Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin ’yan sanda mai wakiltar mazabar Tarayya ta Akko daga jihar Gombe, ba kawai ya kai wannan matsayin ba ne, ya kuma bar gagarumin tasiri saboda irin ayyukan da ya yi.

Wannan kuma ya gangaro ne daga irin kudurinsa na siyasa da ba da himma ga ayyukan ci gaba kamar yadda aka san su a duk fadin duniya.

Abin da kuma ya sa yake yin tasiri a siyasance ba kawai saboda zuba jarin da yake yi kai tsaye ba ne a kan ayyukan ci gaba, amma ta irin yadda wadannan ayyuka suke yin tasiri a kan ci gaban arzikin jama’a bisa alkalumman kungiyoyin ci gaban jama’a da ma gwamnatoci.

Misali, a sashen kiwon lafiya, akwai damuwowi a harkar kiwon lafiya na al’ummu, abin da ya tilasta wa gwamnatin Tarayya ware kashi guda cikin dari na dukkan kudin da ke shiga lalitar gwamnati a shekara ga samar da kula da lafiyar jama’a a matakin farko. Wadannan sune irin hidindimun da ake yi wa jama’a a matakin mazabu. Sai dai kuma kash! Irin wadannan hidindimu suna gamuwa da tasgaro ta fuskacin lalacewar gine-ginen dakunan shan maganin da ma irin yadda aikin ke gudana.

Shi ya sa don ganin kula da lafiya a matakin farko na tafiya yadda ya kamata a mazabarsa, Honorabul Usman Bello Kumo ya shiga cikin ginawa, gyarawa da kuma samar da kayayyakin aiki a dakunan shan maganin da ba su gaza shida ba. Wadannan sun hada da wadanda ya gina a garuruwan Badara, Kembo da Kumo.

Wannan mataki da ya dauka ya yi daidai da kudurin Hukumomi irin su DFID, UNICEF, da WHO wadanda suke yin kamfe don inganta samar da lafiya a matakin farko don rage cinkoso a Cibiyoyin lafiya matsakaita da kuma manya.

Kamar ka ce hakan bai isa ba, Honorabul ya sa hannu a samar da nagartattun hidindimun kiwon lafiya a Asibitin Kumo ga wadanda suka ci gajiyar cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da ya samar.

Har ila yau, bisa irin goyon bayan da yake bayarwa ga shirin bunkasa harkar noma da ake da shi a kasar nan, wanda zai mai da da yawan jama’ar kasa ga noma tare da bunkasa harkokin kiwo, Honorabul Usman Bello ya fahimci muhimmancin ba kawai a zuba kudi a harkar ba, a kuma samar da kayayyakin more rayuwa da za su jawo ci gaban wannan sashe mai muhimmanci ga jama’a. A kan haka ne ya sa ya giggina wasu hanyoyi da za su saukaka sufirin jama’a da kayayyakinsu ba tare da shan wata muguwar wahala ba. Daya daga cikin irin wadannan hanyoyi da ya gina ita ce mai tsawon kilomita 30 da ta taso daga Kidda zuwa Panda, wacce ta hada gonaki da kasuwanni, ganin irin yadda ta ratsa kauyuka da dama.

Bugu da kari ya taimaki matasa da ababen hawa don taimaka wa sufurin mutane da kayayyakinsu da kuma samar da aikin yi ga mamallakan wadannan ababen hawa. Akalla matasa 20 ne daga Karamar Hukumar Akpo da ke cikin mazabarsa suka amfana da wannan shiri nasa.

Wani al’amari kuma da ya sa kansa a ciki shi ne harkar samar da gidaje ga jama’a. A wannan shiri Honorabul Usman Bello Kumo ya samar da gidaje masu saukin kudi ga matasa akalla ashirin. Wannan ya bunkasa ci gaban wadanda suka ci gajiyar wannan shiri, don kuwa ya ba su damar su mai da hankulansu ga sauran harkokin rayuwa na yau da kullum.

Wani muhimmin shiri kuma da ya kama yi gadan-gadan shi ne na samar da ruwan sha a Pindiga da kewaye. Wannan wani yanki ne da ya dade a cikin matsalar rashin wadataccen ruwan sha, musamman lokacin rani. Wannan ya shafi lafiyar yankin da kuma barkewar annoba irin na kwalara da zawo. Ya yi kokarin tabbatar da cewa ana samun ruwan sha ta gina rijiyoyin burtsatse wadanda suka cika bukatun Hukumar UNICEF. Wannan ya bunkasa yin rayuwa cikin tsafta da saukin samun ruwan sha.

Ta fuskacin ilimi kuwa, in aka yi la’akari da yawan karuwar jama’a a Nijerya, musamman a Arewa maso Gabas za a ga abin na karuwa. Cibiyar kididdigar jama’a na Amerika ta sanya karuwar jama’a a Nijeriya da kashi 3.2% a kowace shekara. Don haka Nijeriya da ake ganin tana da jama’a miliyan 195.5 a 2019, to yawan jama’arta zai doshi miliyan 400 a 2050. To, in aka yi la’akari da irin yadda jama’a ke karuwa, to samar da abubuwan more rayuwa kamar ilimi na bukatar karin zuba jari. Ana bukatar gine-gine da tsare-tsare nagartattu da kuma kwararrun jama’a a Harkar ilimin.

Ta nasa bangaren, Honorabul Usman Bello Kumo ya gina makarantun Firamare da na Sakandare guda shida a mazabarsa. Ya kuma ba da gurbin karatu ga wasu daidaiku don dai a samar da kwararru a wannan sashe na ilimi.

A matsayinsa kuma na mutum mai son addini, ya taimaki jama’a da dama ta fuskacin addininsu da ke mazabarsa. Wannan ya jawo hadin kai da ci gaban jama’a a yankin. Ya biya wa kiristoci sun je ziyara a birnin Jerusalem. Ya kuma biya wa musulmi da dama kudin zuwa hajji don sauke farali a Makka. Ya kuma giggina wuraren ibada da masallatai.

Wani muhimmin batu da ya sa ake ganin baraka a ayyukan ‘yan sandan kasar nan shi ne yadda sassan rundunar ba sa tafiya kafada da kafada da juna wajen tafiyar da ayyukansu.  Sannan kuma akwai yadda wasu jami’an ‘yan sanda dubu guda suka shafe watanni 12 ba a biya su hakkokinsu ba bayan sun gama daukar horo. Honorabul Usman Bello ne ya ta da wani kuduri wanda ya kai ga biyan su hakkokinsu.

Shi ya sa yana da kyau irin wadannan jajirtattun mutane da suke da kyakkyawan kudurin siyasa a rika yin bayaninsu ga jama’a. Da haka ne su kansu jama’a za su fadaku, su rika yin zaben kwarai don ci gaban al’ummunsu. Ko ba a fada ba, tabbas Honorabul Usman Bello Kumo zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar Gombe.

Exit mobile version