Abubakar Abba" />

Abinda Ya Sa Kiwon Tarwada A Nijeriya Ba Ya Bunkasa – Cif Obasanjo

Kiwon Tarwada

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya gana da shugabannin kungiyar ma su kiwon kifin tarwada , Inda kuma ya koka kan yadda sana’ar ta kiwon tarwada ba ta bunkasa a kasar nan.

A lokacin ganawar, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kuma koka kan yadda yan nakama su ke kara janyo wa fannin koma baya, Inda hakan ya kara janyo rashin bunkasar sana’ar a kasar nan.

Ma su kiwon sun dai gana da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ne a karkashin inuwar kungiyar ma su kiwon kifi ta kasa (CAFAN) a dakin karatu na Obasanjo da ke a garin Abeokuta cikin jihar Ogun.

Bugu da kari, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo wanda kuma ya kasance daya daga cikin wadanda su ka kirkiro da kungiyar ta CAFAN ya kuma koka kan yadda yan na kama a tannin su ka mamaye sana’ar, inda kuma ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a samar da canje-canje domin a ciyar da fannin gaba a kasar nan.

A cewar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ma su sana’ar sayar da tarwadar ce, su ka haifar da matsalar domin kuwa sun bar yan na kamar a wajen yin abinda su ka ga dama da kuma sauraron umarninsu, inda ya ci gaba da cewa, ku ne ku ke yin hudda da su domin son ku samu riba mai ya wa.

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ci gaba da cewa, hakan ya kuma nuna cewa, ma su sana’ar ta sayar da tarwadar, ba su da kudurin taimaka wa kansu, inda ya kara da cewa, in har za ku iya daga darajar ku, za su iya yin hakan a cikin shekara daya kacal kuma hakan ne ya kamata a ce kun yi.

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya kuma nuna gamsuwarsa kan kokarin da kungiyar ta ke kan yi wajen ciyar da ita gaba.

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya kuma bayar da tabbacin cewa, fannin na kiwon tarwadar a kasar nan zai kara habaka zauwa babban mataki ba tare da dadewa ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa, shi be ya fara yin kungiyar ma su kiwon kaji ta kksa, inda hakan ya sanya kungiyar ta samu dimbin nasarorid inda daga baya kuma aka kafa kungiyar ma su kiwon tarwada duk kafin a kama shi a kulle shi.

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ci gaba da cewa, a lokacin da na dawo, na dauka cewa, zan iya mayar da kasuwanci na noma kamar yadda ya kama ta bayan an sallamo shi daga gidan Yari.

Shi ma nasa jawabin, shugaban kungiyar ta CAFAN ta kasa Mista Sunday Musa Onoja, Inda ya kara da cewa,, kungiyar za ta kara samun kwarewa daga ilimin da ya ke da shi na kiwon kifin, musamman domin kara habaka kiwonsa a kasar nan, Inda kuma a yayin ganawar kungiyar ta gabatar wa tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da kundin kokarin bunkasa kiwon kifi da kungiyar ta yi

Exit mobile version