‘Abinda Ya Sa Mu Ka Bar Kasuwar Dabbobi Ta Soja Mu Ka Bude Ta Anagada A Abuja’

Daga Bello Hamza,

Masu sana’ar sayar da dabbobi a tsohuwar karar dabbobi da sojan kasa na Nijeriya su ka samar masu a yankin Giri Abuja, sun yi karin haske a kan lalacewar alakar wadda a ka kulla kamar shekara biyu baya. Jagoran ’yan kasuwar Malam Abdulkadir Muhammad ya ce a sakamakon haka, a yanzu sun yi hijira zuwa wata sabuwar kasuwar kara da su ka kafa a kauyen Anagada da ke kan hanyar Zuba zuwa Gwagwalada a yankin birnin na trayya.

Ya danganta matsalar lalacewar alakar kan dalilin rashin hadin kai irin na al’ummar Hausa/Fulani kamar yadda ya yi bayani, lamarin da ya ce ya kai ga wanda ya jagorancesu wajen kullata, ya janye hannunsa alamarin. “Hakan ta sa jagororin soja su ka bukaci da mu bar wajen. “Bayan nan sai a ka tura mana ma’aikata su ka tada mu daga tsohon wajen cikin halin ba-zata da hakan ya jawo mana matsalar rasa yawancin tsoffin abokan huldarmu da ke zuwa daga jihohin arewa da kuma kudu, don huldar kasuwanci.

Malam Abdulkadir ya ce, daga bisani, sun samu Mai-Garin Anagada da Sarkin Fawan wajen, su ka bayyana masu kudurinsu. Ya ce a yanzu sun samu cigaba fiye da na baya tun lokacin da su ka dawo zuwa sabuwar kasuwar karar, wadda ya ci ke ci a kullum, a maimakon bayan kwana hudu irin na lokacin baya. “A saboda haka, mu na kira ga sauran al’ummarmu ’yan kasuwa da su zo mu hada kai mu raya wajen. “Akwai tanadin waje ga sauran ’yan kasuwa masu sayar da kayan abinci irin hatsi da doya da tumatur, kuma mu na kira a garesu da su zo, mu hada kanmu baki daya.

Bayani ya nuna cewa kasuwar wadda ta samu aminicewar karamar hukumar Gwagwalada, tuni ta fara samun ayyukan tallafi daga karamar hukumar da ya hada da gina masu rijiyoyin burtsatsai guda 3, da kakkafa tankunan ruwa don shayar da dabbobi da kuma sauran bukatun jama’a, sai kuma yin dabe a bangaren mahautar dabbobin kasuwar. Shi ma a zantawarsa da wakilimu, jagoran bangaren kananan dabbobi na kasuwar Malam Abubakar Muhammad, ya ce duk da cewa kasuwar ba ta wuce wata 5 da kafawa ba, izuwa yanzu sun samu nasarori masu yawa.

Ya ce mahauta daga kwaryar birni na zuwa kasuwar su na sayan raguna ko awaki ko shanu tare da aikin fida a wajen, kafin wucewa da naman zuwa cikin gari. “Haka kuma mu na samun sakon sautun dabbobi daga abokan huldarmu daga yankuna irin Legas da Fatakwal da sauran wurare na kudancin Nijeriya, a yayin da a wani zubin kuma su ke zuwa nan da kansu don sayan dabbobin, inji shi. Jagoran ya ce akwai shirin kafa katanga da kuma gina shaguna, da ya ce karamar hukumar ta Gwagwalada ke shirin yi masu.

Exit mobile version