Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, za ta karbo rancen dala biliyan 1.2 kwatankwacin Naira biliyan 459 daga kasar Brazil.
Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a zauren majalisar wakilai da ke a Babban Birnin Tarayyar Abuja, inda ta kara da cewa, Gwamnatin tarayya za kuma ta mallaki kadada 100,000 a kowace jiha don samar da abinci.
A cewar Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, za a gina hanyoyin mota a irin wadannan wurare don samar wa manoma damar kai amfanin gonakansu zuwa kasuwanni don a rage masu asarar da suke tabkawa a yayin da suka yi girbi.
Sai dai, ‘yan Nijeriya da dama sun so ki shirin a lokacin da bashin kasar ke ci gaba da karuwa, inda misali, Ofishin Kula da Bashin ya bayyana cewa, a yanzu yawan bashin da ake bin Nijeriya ya kai Tiriliyan 31.01.
Wannan furucin na Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ba shi ne na farko da gwamnati ke magana game da rancen ba.
Bugu da kari, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, da Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono ne suka fara sanar da shi a watan Yunin 2020, a wani taron manema labarai a Abuja.
Jawabin da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya karanta a taron, wanda aka wallafa a shafinsa na Tiwita, ya ba da cikakken bayani game da rancen.
A cewar Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, za a yi amfani da rancen ne don kawo sauyi a harkar noma a Nijeriya ta hanyar wani shirin aikin noma da ake kira a turance “Green Imperatibe”, inda ya kara da cewa, shirin ya kai dala biliyan 1.2 kuma za a aiwatar da shi a cikin shekaru biyar zuwa 10.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya ci gaba da cewa, kudade don shirin zai fito ne daga Bankin Raya Kasa na kasar Biirazil da Bankin Deutsche, tare da inshorar da Kamfanin Garanti da Hukumar Gudanar da Asusun da Kamfanin Islama na Kamfanin Inshora na Bankin Bunkasa Musulunci ya bayar da kuma hadin gwiwar Gidauniyar Getúlio Bargas.
Ya ce, shirin zai shigo da sassan taraktoci kusan 5,000 da kayan aiki masu yawa, inda ya kara da cewa, yarjejeniyar an yi ta ne a matsayin mai zangon shekaru 10.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya kara da cewa, hakan zai kuma taimaka wa cibiyoyin aikin noma da ke kasar nan.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce, hakan zai kuma samar da ayyuka a cibiyoyin aikin noma da suka kasance a kananan hukumomi 774 dake a fadin kasar, musamman don bunkasa yin amfani da kere-kere a bangaren aikin noma, da sarrafawa ko kara daga darajar amfanin gona da ake noma wa a kasar nan wanda zai haifar da inganci da kuma dakile asarar bayan girbi, ta haka za a rage kudin abinci a duk tsawon shekara.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammedya yi ikirarin cewa, hakan zai samar da guraben aikin yi kimanin miliyan biyar ga ‘yan kasar nan, inda ya kara da cewa, kuma zai sanya sama da dala biliyan 10 cikin tattalin arziki cikin shekaru 10.
Ya ce, shirin zai samar da wadataccen tsarin samar da kayayyakin amfanin gona ga manyan kamfanoninmu na samar da kayayyaki zuwa gida, ta yadda za a adana biliyoyin dalar Amurka da abinci da kuma horar da kimanin malaman gona su 100,000 cikin shekaru uku.
Ya ce, wannan zai iya shafar sama da mutane miliyan 35 ta fannin abinci da tattalin arziki, inda Lai Mohammed ya bayyana cewa, za a sake farfado da bincike da ba da gudanar fadada aikin noma a Nijeriya ta hanyar kayan aikin kere-kere na shekaru biyar.