Yusuf Shuaibu" />

Abokina Ne Ya Sa Ni Yin Sata A Coci, Cewar Wanda A Ke Tuhuma

An gurfanar da Ighale Tochukwa dan shekara 26 a gaban kotun Isolo, bisa satar kayan kida na coci wanda kudin su ya kai naira 390,000, ya bayyana wa kotu cewa, abokinsa ne ya sa shi yin sata a coci domin ya samu kudin kashe wa. Tochukwu ya yi sata har sau biyu ne a cocin ‘Redeemed Church, Liberty Parish’ da ke lamba takwas a kan titun ‘Madwell Mbamalu Street’, cikin yankin Okota, a karo na farko ya saci kayan kida wanda kudin sa ya kai naira 140,000, inda karo na biyu ya saci kayan naira 250,000, ya yi ikirarin cewa abokinsa ne ya shigar da shi cikin wannan mummunar aiki domin ya samu kudade masu yawa wadanda zai dunga gudanar da rayuwarsu da su.

Wanda ake tuhuma ya amince cewa, ya sayar wa Onyekechi abokinsa wanda ya sashi yin satar kayayyakin a kan kudi naira 15,000. “Na hadu da Onyekachi ne a yankin Mile 2, inda ya ke shan wiwinsa, sai ya fada min cewa idan na samo kayayyakin kida na coci, to zai ba ni kudade masu yawa. Shi ne ya zugani yin wannan satar. Kafin wannan lokaci dai, ina gudanar leburancina a rukunin gidaje da ke ‘Greenfieid Estate’ cikin yankin Okota. Na sayar wa Onyekachi abun magana kan kudi naira 15,000. Jiya ne na biyun da na yi yunkurin yin sata a coci. Ina amfani ne da karfe wajen cire rufin sama na coci sai in samu hanyar shiga,” in ji shi.   

A cewar lauya mai gabatar da kara, Oje Uagbale, an samu nasarar cafke Tochukwu ne ta hannun masu gadi cocin, inda ya yi ikirarin cewa fasto ne ya aiko shi ya gyara kayayyakin kidan. Ya ce, nan ta ke aka mika shi ga jami’an ‘yan sanda da ke Ago-Okota, inda aka gurfanar da shi a gaban kotu ranar Juma’a 28 ga watan Afrilun shekarar 2019.

Alkali mai shari’a Olufunmilayo Teluwo, ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wanda ake hutuma a gidan yari, tun da babu wanda ya nemi a bayar da belin sa.

Exit mobile version