Abu Ne Mai Muhimmanci Mace Ta Samu Hanyar Dogaro Da Kanta A Harkar Fim -Mansurah Isa

Mace

Daga Wakilimu,

Tsohuwar jarumar fim Mansura Isah matar jarumi Sani Musa Danja tana daya daga cikin mata da suke fafutukar neman abubuwan dogharo da kansu tare da tallafawa jama’a, hakan ya sa ta samar da gidauniyar tallawa mabukata wato Today’s Life Foundation. Baya ga haka tana harkokin kasuwanci da sana’o’I daban-daban, hakan ce ta sanya muka ji ta bakinta dangane da yadda mace ya kamata ta yi fafutukar neman na kanta a matsayinta na matar aure, don haka sai ku biyo ku ji irin amsar da ta ba mu.

To matsayin ki na matar aure kuma mai iyali kina daya daga ckin mata da suke fafutukar neman na kansu ko ya ya matar aure take kasancewa a wajen neman abin da zata dogara da kanta?

Mansura Isah: To ka san mu a nan yadda rayuwar mu take musamman matan Arewa, daga mace ta yi aure, idan tana aiki sai ta bar aikinta, idan kasuwanci take yi sai ta bari domin tana tunanin duk wata dawainiya tata mijinta ne zai dauke da iyalan da za ta haifa, to amma idan ka duba yadda rayuwar take da yadda Allah yake al’amuransa wani loakcin, ba wai don namijin bai isa bane a wajen kulawa, to, amma idan babu tsufa akwai mutuwa, mun sha ganin miji yana da kudi iayalansa babu abinda suka rasa, amma sai Allah ya dora masa rashin lafiya, har ta kai duk abinda ya mallaka ya kare, daga karshe ya mutu, to a nan sai iyalan su dawo su shiga wani irin yanayi su samu kansu a rayuwa da za a yi ta mamakin irin daular da suke ciki a baya, to wannan abin mun gani ya fara akan mutanen da muek rayuwa tare da su, don haka ba wai miji na ba zai iya ciyar dani ko kula da mu a matsayin iyalinsa ba ne, amma abin da na lura shine dogaro da mutum daya ba Allah ba akwai gajiyawa, kuma dalilin da ya sa muatne su ke ta ganin kamar ina zafin nema in bude shago nan da can na yi wannan harkar kasuwancin da sana’a abune da suka faru da yawa a baya, wanda suka bude min ido kuma suka koya min darasi. Domin kasantuwar lokacin da mijina ya yi hadari ya karye a kafa da hannu, kuma a lokacin babu inda ba mu je neman magani ba haka muka rinka daga filaye da sauran wasu kadarori muna ta sayarwa ta hanyar neman magani da addu’a, don ya samu lafiya wannan ya sa mun shiga wani yanayi. Don haka ya zaunar dani bayan ya samu lafiya, ya ke cewa dani yadda rayuwa ta kasance mana, ya kamta ke ma ki samu wani abu da zaki rinka yi a matsayin sana’a domin idan na kwanta ki samu ki dago ni, to wannan dalilin ya sa na tashi tsaye kuma shi ma yana taimaka min da jari don ganin harkar tawa ta bunkasa.

Daga wannan darasin da kika samu idan na fahimce ki kina zaburar da mata ne dongane da sana’o’in dogaro da kai kenan?

E haka ne, domin abu ne mai kyau kuma ya dace, domin a nan kusa da ni akwai wadda ta ke yi sana’ar alawar gullisuwa, tun tana yi kadan har abin ya bunkasa ta saye gidan da yake kusa da ita, kuma tana da ma’aikata mata da suke yi mata aiki, tana da rufin asiri na rayuwa a yanzu, kuma abin da zai ba ka mamaki ko firamare ba ta yi ba, amma gashi ta yi amfani da basiranta Allah ya daukakata mutane da yawa suna ci a karkashinta, kuma a cikin gidanta take yi ba tare da ta je ko’ina ba. Amma a irin wannan fafutuka da mata da al’amuransu na aure ba, ko abin da ya shafi kual da miji ba, baka ganin hakan ce ta sa ake kyamar sana’a ko aikin mata?

To ni dai ina kallon kaina ne, kamar yanzu da kazo ka same ni a shagona ne, na fito daga gidana zuwa shao kuma ga yara na da suke kula da wajen kafin na zo ko idan bana gari sannan ni nake zuwa na dauko yara daga makaranta ka ga ‘ya ta nan tun safe nake kaita makaranta, sai yamma naje na dauko ta, in kuma bana gari awkai mai daukota, don haka idan kaga mace ba ta kula da gida ba ta yi niyya bane, don haka sana’a ba zai hana ta kula da gidnata ba.

To a wajan gudanar da harkoki na kasuwanci da sana’a wanne irin matsaloli matan aure suke fuskanta?

Gaskiya matan auare suna shan wahala wajen samun abin yi kama aikin office za ka ga an san mata sun iya kuma za su yi aiki mai nagarta, amma sai a hana su dalili kawai don tana da aure, don haka sai ka ga an dauko wacce ba ta kware ba don ba ta da aure, a kawo ta kama idan ba ta yi yadda ya kamata ba a ce duk mata haka suek, to gaskiya hana mace mai aure aiki duk da an san za ta iya wannan ba karamin kuskure bane.

To ita matar auren ma ya ya kamata ta kasance a wajan aiki ko a kasuwa?

Abin dai da yake wajibi shi ne ta sani akwai ka’idojin aure da suek kanta, kuma akwai yada doka ta iyakance mata wajen mu’amala da mutane, don haka dole, idan matar aure da ta yi aiki ko wani, kasuwanci to dole sai ta san akwai abinda ya hau kanta wajan tafiyar da aikin ta a wajan da ba cikin gidan ta ba, don haka ina kira ga mata da su san irin mu’amalar da za su yi a wajan gudanar da aikin su ko kasuwancin da suek yi a wajan da ba gidan auren su ba.

To madalla mun gode.

Nima na gode.

Exit mobile version