Abubuwa goma da suka kamata a sa ni game da cutar shawara cikin. Saboda kuwa a cikinn watanni da suka gabata, cutar shawara ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 40 kamar dai yadda rahotanni suka bayyana.A kasar Nijeriya. Sauro shi ne yake dauke da kwayar cutar shawara kuma ana kamuwa da ita ne ta hanyar cizon sauron. Hakanana ma cutar shawara ana iya maganceta ta hanyar rigakafi kuma tana yaduwa ne ta hanyar cizon sauron kadai
Ga jerin wasu ababuwa goma da ya kamata a sani game da ita cutar ta shawara:
- Rigakafi shi wata hanya ce mafi da cewa wurin maganin wannan cuta mai kisan mutane.
- Ana iya magance cutar idan aka dau mataki a kanta kafin ta bunkasa a jiki dan –Adam.
- Alamun cutar na bayyana ne cikin kwana shida, wadannan alamun sun hada da, masassara, ciwon kai da kuma ciwon baya.
- Kimanin minti15 wadanda suka kamu da cutar ta kan zarce zuwa rashin lafiya mai tsanani wadda kan iya haifar da zuban jini, rashin aikin wasu gabobin jiki da kuma mutuwa.
- Rigakafin kan iya zama illa ga mutanen da suka wuce shekara 60 da haihuwa.
- Hakanan ma mace mai ciki, rigakafin kan iya zama illa gare ta, ita an fi son ta tuntubi likata kafin tayi rigakafin.
- Idan har rigakafin ba ta samu ba, ana iya amfani da maganin sauro iri daban-daban.
- Dolene sai mutum yayi rigakafi idan zai tafi daya daga cikin kasashen Kudancin Amurka.
- Ga masu tafiya kuwa kasashen da suke fama da cutar shawarar, ana so mutum yayi allurar rigakafi a cikin kwanaki goma da shigar sa cikin kasar.
- Kashi 99 na wadanda suka yi allurar rigakafin na damar cin karfin kwayar cutar cikin wata daya da kuma har illa masha Allahu.