Abubuwa 10 Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Sinadarin Kodin

da gwamnatin tarayya ta yi na sha da sayar da maganin nan da asalin sa an kirkro shi ne domin Hanin maganin tari, mai suna Kodin, (Codine), wanda daga bisani batagari suka canza masa manufa inda suke shan sa da wata manufar ta daban musamman domin neman jirkita hankulan su, al’umma su na ta tofa albarkacin bakin su.

A ranar 1 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta dakatar da bayar da izinin shigo da maganin tarin na Kodin.

Ministan Lafiya, Isaac Adewole, wanda shi ne ya bayar da wannan umurnin cewa ya yi, ya zama tilas ne daukan wannan matakin ganin yanda wasu batagari suke amfani da maganin ta hanyar da ba ta dace ba.

Yayin da ‘yan Nijeriya da dama suke maraba da wannan doka ta hana shigowa da maganin ruwan na Kodin, wasu kuma gani suke kamata ya yi a binciki hanyar da ake bi ana shigo da maganin da ma raba shi a cikin kasa ta barauniyar hanya.

Kasantuwar ba wani bincike na musamman ake gudanarwa kan kamfanonin da ke hada maganin tarin mai tarin yawa ba, inda a lokuta da yawa lalatattun ma’aikatan kamfanonin suke amfani da wannan daman suna gudanar da wata kasuwar ta bayan fage daban.

A shekarar 2016, wani bincike da wata cibiya mai zaman kanta ta yi a nan Nijeriya wanda kafar yada labarai ta, PREMIUM TIMES,’ ta wallafa a shafin ta ya nu na, dimbin barazanar da maganin tarin na Kodin da makamantan shi suke yi ga matasan mu, musamman nan Arewacin Nijeriya.

Wadannan Sune Abubuwa 10 Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Yadda Ake Amfani Da Maganin Tarin Na Kodin Ta Hanyar Da Ba Ta Dace Ba A Nijeriya

  1. Kodin magani ne mai kashe radadi a jiki, sannan kuma yana maganin kamar abin da ya shafi mura. Sai dai in an sha shi har ya wuce kima zai iya haddasa nauyin jiki da mutuwar gabobin jikin da dai makamantan hakan.
  2. Matasa ne suka fi yawan saye da sayar da maganin tarin na Kodin, matasan da suke da gurguwar fahimtar wai, su dai su ji su a wata duniyar ta daban. Abin mamakin ma a nan shi ne, ‘yan mata su suka fi yawan tu’ammuli da Kodin din hada har da mata masu ciki.
  3. Duk da shike, sauda yawa shigo da Kodin ake daga wajen kasarnan, sama da kamfanonin hada magunguna na kasan nan 20, suna hada Kodin din.
  4. Kwalbar Kodin din guda ana sayar da ita ne tsakankanin Naira 1000 zuwa 1200, ya danganta ne da ko na wane kamfani ne. wadanda ciwon shan Kodin din ya kama su sosai, sukan iya shan kwalba 4 a rana guda.
  5. Duk da cewa, an haramta shan Kodin din da nufin yin maganin tari ba tare da izinin Likita ba, amma dai maganin tarin na Kodin sananne ne. masu shan na sa ta hanyar da ba ta dace ba sukan hada shi da lemun Kwalba kamar Kokakola, ta yanda za su iya shan sa a ko’ina suka ga dama ba tare da mutane sun fahimci ko me suke sha ba.
  6. A nan Arewacin kasar ne aka fi shan Kodin din ta hanyar da ba ta dace ba fiye da sauran sassan kasarnan. Ana tsammanin hanin da aka yi na shan giya a wasu sassan shi ya sanya matasan suka koma ga shan Kodin din da makamantan shi irin su, tramadol,rephnol da sauran su, da in an sha su ba bisa ka’ida ba sukan iya zama wata masifan.
  7. Sama da kwalabe milyan uku ne na Kodin din ake sha a kullum a Jihohin Kano da Jigawa kadai, a cewar Majalisar Dattijan Nijeriya.
  8. Hukumar yakar miyagun magunguna na kasarnan tana bakin kokarinta na yakar wannan bala’in. a samamen da ta kai na baya-bayan nan, ta kwace Kwalaben na Kodin sama da dubu 24,000, da aka shako su a cikin wata babbar mota a Katsina.
  9. Mawakan Nijeriya suna taimakawa wajen yawaitan shan Kodin din, ta hanyar wakokin su da a ciki suke kwatanta shan sa da wai, ‘ka ji ka a daidai.’ Ko kuma wai ka ji ka a sabuwar rayuwa.
  10. A duk lokacin da aka sha shi ba bisa ka’ida ba, Kodin din zai sa ka ji ka ba karsashi, ya kashe maka gabobin jiki, ya mantar da kai halin da kake ciki, zai ma iya sanya ka cikin wata dimuwan ta daban daga gaskiyan halin da kake ciki.

 

Exit mobile version