Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025

byAbubakar Abba and Sulaiman
8 months ago
Aikin Gona

Fannin aikin noma na bayar da gagarumar gudunmawa a Nijeriya, duba da cewa; akasarin ‘yan kasar, sun dogara ne a kan sana’ar ta noma.

Kazalika, fannin na taimakawa wajen samar da kimanin kashi 23 ga tattalin arzikin kasar.

  • Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina
  • Kashi 85 Na Inibin Da Ake Nomawa Nijeriya, Daga Jihar Kaduna Ne – Dalhatu

Sai dai, abin takaici, har yanzu kasar ta dogara ne wajen shigo da kayan abinci cikin kasar, sannan kuma talakawanta da dama na kwana da yunwa sakamakon karancin abinci.

An karawa fannin kashi 127 a cikin kasafin kudi na bana zuwa Naira biliyan 826.5, sabanin yadda ake ware wa fannin Naira biliyan 362.9 a kasafin kudi na 2024, wanda wannan mataki na nuna cewa, gwamnatin tarayya a shirye take, don bunkasa fannin.

Sai dai wasu kwararru a fannin, sun bayyana manyan kalubalen rashin tsaro, sauyin yanayi, tsadar kayan aikin noma da tsadar gudanar da aiki, barkewar cututtukan da kwarin da ke lalata amfanin da aka shuka a matsayin manyan kalubale biyar da suka wajaba a magance su a wannan shekara, domin habaka noma.

Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024.

1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024.

Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024.

Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma magance yunwa.

Sai dai wasu manoman sun ce, rashin tsaron ya ragu a wasu Jihohin Arewacin Kasar da lamarin ya fi yin kamari.

2. Sauyin Yanayi: Wannan lamari ya zama tamkar ruwan dare a fadin duniya, wanda kuma yake jawo sauya tsarin noma, misali a 2024, wasu manoma a sassan Arewacin Nijeriya, sun koka kan rashin samun saukar ruwan sama a kan lokaci, wanda hakan ya jawo ba su samu wani yin girbi mai kyau ba.

Masana sun yi hasashen cewa, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, sauyin yanayi zai zama babbar barazana a kakar noma ta 2025, wanda kuma rashin daukar matakan kan iya haifar da hauhawar farashin kayan abinci.

A cewar wani rahoto na Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Duniya (FAO), ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma afkuwar annobar ambaliyar ruwan sama a 2024, ya lalata sama da tan miliyan daya na amfanin gona, wanda wannan adadi zai iya ciyar da mutane miliyan 13.

Kazalika, a watan Satumbar 2024, Dam din Alau Dam ya jawo mummunar ambaliyar ruwa, inda ya lalata hakta kimanin 700,000 a cikin kimanin gonaki 200.

Har ila yau, a 2024; sauyin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwan sama a Jihohin Borno, Bauchi, Sakkwato da kuma Jigawa.

3- Barkewar Cututtuka A Gonakin Da Kwari Suka Lalata Amfanin Gona: Misali cutar da lalata Citta da cutar murar tsintsaye da kuma cutar da ke lalata tumatir a 2024, sun yi matukar barna.

Akwai cutar da ta lalata wasu gonaki na Citta, wanda adadin kudin suka kai kimanin Naira biliyan 12 a 2023.

Manoma sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi a dauki matakan gaggawa tare da samar da dauki, domin dakile wadannan cututtuka a 2025.

4- Tsadar Farashin Kayan Gudanar Da Aikin Noma: Manoma sun fuskanci hauhawar farashin kayan da ake gudanar da aikin noma.

Wata kididdiga ta nuna cewa, farashin Man Fetur na haifar da hauhawar farashin kayan abinci, sannan kuma manoma da ‘yan kasuwa sun koka kan haramtaccen harajin na ‘yan na kama ke kakaba musu, bayan sun yo jigilar amfanin gona.

5- Hauhawar Farashin Kayan Noma: Tsadar farashin takin zamani, injinan ban ruwa, tsadar Irin noma, sun kasance manyan kalubale ga manoma, wanda hakan kuma ke shafar girbin amfanin gona.

Saboda tsadar ingantaccen Irin noma, hakan ya tilasta wa manoma sayen Iri, wanda ba shi da wani inganci.

Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi a 2025, a kawo karshen wannna matsalar, domin samar da wadataccen abinci a kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Buhu 116 A Jihar Kano

An Kama Miyagun Kwayoyi Kan Hanyar Zuwa Birtaniya A Filin Jiragen Saman Legas

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version