kwararru da masana dankalin Hausa sun yi kira ga mutane da su yawaita cin dankalin ganin cewa yana dauke da sinadarorin dake kare mutum daga kamuwa da kowacce irin cuta a jiki.
A kasashen duniya da dama ana matukar noma wannan dankali saboda amfanin da yake dashi a jiki.
Wasu dag ciki amfanin da yake yi a jikin mutum sun hada da:
1. Yana kare jiki daga kamuwa da cututtuka.
Dankalin Hausa na dauke da sinadarin bitamin B6 wanda ke kaifafa kwakwalwa, hana kamuwa da dajin dake kama jini, hana damuwa, kawar da laulayin haila da sauran su.
Dankali na dauke da sinadarin bitamin C wanda ke warkar da mura, tari, warkar da ciwo ko rauni da sauran su.
Sannan yana dauke da sinadarin bitamin D dake karfafa aiyukkan hanji, karfafa kasusuwa, hana kamuwa da dajin dake kama fata da sauran su.
2. Ya kunshi sinadaran Magnesium da Potassium
Sinadarin Magnesium yana taimakawa jikin mutum wajen hutu musamman ma idan an gaji, yana kara inganta bugawar zuciya, karfafa jijiyoyi, kasusuwa da dai sauransu.
Bugu da kari kuma shi sinadarin Potassium na kawar da kumburin jiki, kawar da cutar koda, kare mutum daga shiga hali na bugawar zuciya ga kuma karfafa jijiyoyi.
3. Dankalin Hausa ya kunshi sinadarin Beta-carotene da yake karfafa ido da karfafa garkuwan jiki.
4. Dankalin Hausa na kawar da cutar siga.
5. Yana dauke da sinadarin bitamin A da yake inganta karfin ido.
6. Bugu da kari kuma ya kunshi sinadarorin hana kamuwa da cutar daji kowacce iri a jiki.