- Kuri’un Da Aka Kidaya Sun Haura Na Zaben Gwamna A 2019
- Yadda Gandujiya Ta Yi Koyi Da Kwankwasiyya
- APC Ta Kyankyashe ‘Kwan Kaza’ 528, Ba Baragurbi
- Dalilinmu Na Kin Fita, Inji Wasu Masu Zabe
- Ko Ba Komai An Yi Lafiya, A Cewar Wasu
A duniyar Nijeriya ta yanzu, da yawan mutane da ma masu lura da al’amuran yau da kullum su na kallon gudanar da zabukan kananan hukumomi a matsayin bata lokaci, domin duk a yadda aka tuka shi, jam’iyya mai mulkin jihar da aka yi zaben ce ke wawashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomin da kansilolinsu, lamarin da ya sanya ake ganin shi ke sanya mutane ba su cika fita kada kuri’a.
To, sai dai kuma a Jihar Kano an bayyana cewa, yawan jama’ar da aka kidaya cewa, su ne suka fito suka kada kuri’a a zaben na kananan hukumomin da ya aka gudanar ranar Asabar da ta gabata, wacce ta zo daidai da 16 ga Janairu, 2021, sun fi yawan mutanen da suka yi dafifi suka fita kada kuri’a a lokacin da aka gudanar da manyan zabukan kasar a 2019, musamman ma zaben gwamnan jihar.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na JIhar Kano (KANCSEIC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka, ne ya bayyana wannan sakamako ranar Lahadi a birnin Kano lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, inda ya ce, duk da cewa an gamu da wasu kananan kurakurai a lokacin gudanar da zaben, duk da haka, hukumar ta samu nasarar gudanar zaben cikin nasara.
Bayan hakan ne ya wara fayyace abinda dake daukar hankali, inda ya ce, yadda yawan kuri’un da aka kada wa Jam’iyyun APC Da PDP a zaben Gwamnan Jihar Kano na shekara ta 2019 sun haura yawan kuri’un da aka kada a zaben kananan Hukumomin da ya gabata ranar 16 ga Janairun 2021.
Sakamakon karshe na shekara ta 2019 ya nuna cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 1,033, 695, yayin da babban mai adawa da shi a zaben, Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida) na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 1,024,713. Jimillar kuri’un bakidaya da jam’iyyun biyu suka samu ya kama 2,058,408, wanda shi kuma sakamakon zaben kananan hukumomi da Farfesan na KANSEIC ya bayyana ya kama 2,350,577.
Sai dai kuma wasu na cewa, jama’a ba su yi mamakin jin wannan sakamakon zabe daga bakin Farfesan KANSEIC ba, kasancewar jam’iyya mai mulki ita ce ta yi kidanta kuma ta yi rawarta, musamman ganin babban tsagin da ke hamayya da gwamnati mai ci, wato tsagin PDP Kwankwasiyya sun shelanta kaurace wa zaben, inda hakan ta sa aka gudanar da zaben lami lafiya, kuma da su daya tsagin da ke karkashin tsohon minista, Ambasada Aminu Wali, ba a ji duriyarsu ba, idan aka yi la’akari da yadda sakamakon ya nuna wani dan ladan gabe kurum suka samu daga cikin kurin da shugaban hukumar zaben na Jihar Kano ya shelan cewa an kada ba.
Sannan kuma wasu masu adawa da jam’iyya mai mulki sun bayyana cewa, yara kanana ne suka dinga kada kuri’a, kamar yadda hotuna ke ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda shi ma ya zama wani abin al’ajabi a zaben.
Koma dai me ake ciki ita ma wannan gwamnatin kamar wadda ta gada kazarta ta kyankyashe kwan shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da kansiloli 484 ba tare da baragurbi ba, inda jimillarsu ya kama kwai 528.
Sai dai kuma duk da kallon da ake yi wa Gidan Gandujiyya da tafka irin wannan cinye-du, ana kallon lamarin a matsayin ba a kasa ta dauka ba, domin gado ne daga gwamnatin Kwankwasiyya da ta gada, inda a lokacinta aka fara ganin irin wannan zabe a tarihin Jihar Kano, zaben da ko kujerar kansila, jam’iyyar adawa ba ta iya lashewa.
A zagayen ganin kwakwaf da LEADERSHIP A YAU ta gudanar a ranar Asabar din, ta lura da rashin fitowar al’umma, kamar yadda wasu hotuna suka nuna, yayin da a gefe daya kuma su ma jami’an zabe ba su isa filayen zaben akan lokaci ba, musamman a mazabar Tukuntawa, inda jami’an zaben sun isa rumfunan zaben ne da misalin karfe 11:30 na safe, lamarin da ya sanya aka fara kada kuri’a da karfe 12:25 na rana.
Ya ce koda ya zo, wasu ya tarar a akwatinsa suna ta yin dangwale sai dai yana kada kuri’arsa sai ya bar wurin, “kuma ka ga dai-daikun mutane ne ke sanye da takunkumin rufe baki da hanci. Gaskiya ba zan kara yin zaben kananan hukumomi ba,” inji Yusuf.
Ita ma wata mata a rumfar zaben mai suna Hadiza Ibrahim cewa ta yi, “ni na zo ne na kora yara na zuwa gida kawai.” Ta kara da cewa, tana da katin zabe, amma mijinta ya ce, sam kada ta je ta zabi kowa.“Ko kai yanzu ka ga babu wata macen arziki da ta fito yin zabe. Akan me to ni zan fito,” a cewarta.
Shi kuwa Sadik Abubakar ya ce, zabe yana tafiya daidai kamar yadda suka yi tsammani, sai dai ya ce duk da rashin fitowar al’umma, an samu zaman lafiya.
“Tun da na zo gurin nan ba wanda ya zagi wani. Kowa yana yin zabe cikin kwanciyar hankali. Wannan shi ne abinda ake so dama,” a cewar Sadik.
A wani cigaban kuma hukumar shari’a ta Jihar Kano ta kafa kotun sauraron koke-koken zabe a Jihar Kano, Alkalin alkalan jihar Mai shari’a Nura Sagir Umar ne ya kafa kotunan sauraron koke-koken zaben guda biyu karkashin sashe na 36 (1) na dokokin zabe na Gwamnatin Jihar Kano na shekara ta 2002.
Sanarwar da mai magana da yawun Babbar Kotun Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana cewa, kotunan za su kasance karkashin Mai Shari’a Hauwa Lawan Umar da kuma Mai Shari’a Muhammad M. Jibrin.
Ya kara da cewa, an dora wa kotuna alhakin sauraron korafe-korafen zabe da kuma yanke hukunci kan al’amuran zaben na ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2021.