Connect with us

HANTSI

Abubuwan Da Ke Janyo Fyade Da Hanyoyin Magance Su

Published

on

Lallai akwai abin takaici irin yadda ake yi wa mata, an yi wa ‘yan mata dama yara mata kanana fyade kuma abun na karuwa harma yana kai wa da salwantar rayuka. Babu wani uba ko mutum mai hankali da zai goyi bayan wannan mummunar dabi’a ta fyade wallantana ya ji dadi ko ya amince hakan.

Akwai abubuwa da dama da ke sabbaba wannan mummunan dabi’a wadanda suka hada da

  • Babu shakka idan jama’a ko al’umma suka yi biris da tarbiyan addini to dole su bi tarbiyyar shaidan.

  • Watsi da tufafi na mutunci tare da maye gurbin su da na turawa yana kara fitsara da rashin kunya wanda zai iya jawo komai.

  • Rashin kulawa da tarbiyan yara musamman mata tare da rashin sanin ina suke zuwa ko samun mai rakiya in za su fita, yana jawo wannan masifa.

  • Yawan kallon fina-finai mara tarbiyya na cikin gida da na waje yana kara lalata tarbiyyar yara maza da mata.

-Rashin jin wa’azi ko rashin aiki da wa’azi shi ma yana janyo wannan bala’i.

Hanyoyin magance lamarin

  • Kulawa da tarbiyan addini wajibi ne ga duk al’ummar da ke son ganin karshen fyade.

  • Sanya sutura bisa tsarin addini da kyakkyawar al’ada jigo ne wajen kare kai daga fasadi dama fyade.

  • Sanya kula da bada kariya gwargwado ga yara mata tare da hana shiga gida da mu’amala da su ga duk wanda shari’a ta masa birki wajen shiga gida.

  • Hana kallon miyagun fina-finai na cikin gida Nijeriya da kuma na kasashen ketare.

  • Wa’azi tare da nuna illar bokaye da matsafa masu sa wasu yin fyade ga yara.

  • Yin hukunci na addini ga masu aikata fyade da wayar da kai ga kungiyoyin mata masu lalata tarbiyya da cire wa yara kunya a zukata ba.

Akwai abin takaici wajen wasu kungiyoyin mata masu wayar da kai a kan illar yi wa mata fyade da suke bugewa da cire wa yara kunya a zukata tare da mayar musu gurbin da rashin kunya da shedan ci, daga karshe ma sai a nemi kudi da yaran a kyale su zama mata masu lasisin fasadi.

Hukun cin Allah shi ne kadai zai iya kawo karshen fyade a kasa ta Nijeriya ba hukunci Dan’adam ba. A kwai kyakkyawar rayuwa da adalci da nasara a hukuncin Allah. Muna kira ga duk mai addini da ya nemi a yi hukunci na Musulunci ga duk wanda ya yi fyade ba, hukuncin zamani ba ko neman hukunci wai mai tsauri ba. Hukuncin Allah ya fi na kowa dacewa tare da zama ladabtarwa mai kawo karshen fyade.

Allah ka kare mana ‘yayanmu da matanmu da iyayenmu daga sharrin duk wani mai fyade ka kuma amintar da mu a kasarmu Nijeria, amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: