Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ke Sa Fata Ta Yamushe Ko Ta Tsufa Da Wuri

by
4 months ago
in ADON GARI
2 min read
Fuska
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kowane mai rai dole ne wata rana ya tsufa, amma akwai abin da idan aka yi wa fata zai sanya ta tsufa da wuri. Kuma dole ne mu yi iya kokarin barinsu. Abubuwa da suka hada da rashin bacci da yawan gajiya da amfani da kayan kwalliyar da ba ta dace da fata ba. Yawan shan taba da kuma yawan cin naman shanu bayan an bai wa shekara arba’in baya.

Abubuwan Kamar Haka: Gajiya: Yawan gajiya da shiga damuwa na matukar sanya fatar jiki tsufa. Idan mutum ya shiga damuwa, fatarsa na fitar da wani abu ‘cortisol’. Wannan ‘cortis’ din yana yi wa fata dameji. Sai a ga mutum ya tsufa da wuri. Shi ya sa sai a ga wanda yake cikin damuwa da talauci yana riga sa’anninsa tsufa da ke birni, kuma cikin jin dadi. Don haka sai a yi iya kokarin rage sanya kai tunani da damuwa.

Kayan kwalliya: Akwai wasu kayan kwalliya da ke dauke da sinadarai kamar su; zinc odide da dimethicone da propylene suna iya sanya fata tsufa, musamman idan an yawaita amfani da su. Wasu sinadaren suna bata fuska, kaikayi daga nan sai fesowar kuraje har fuska.

Labarai Masu Nasaba

Saboda Kauce Wa Bacin Rai Daga Teloli Na Koyi Dinki Da Rana Tsaka — Hadiza D. Auta

Dole A Hada Hannu Don Kawo Karshen Fyaden Kananan Yara -Sameerah Shinko

Taba: Yawan shan taba na sanya tsufar fata da wuri domin wannan sinadarin da ke cikin sigari nicotine, wanda ke toshe magudanar jini. Shan tabar na sanya fata ta sake karfinta. A rage shan taba saboda tana janyo tsufan fata.

Yawan cin soyayyen abinci da cin abinci a kan kari ba don yunwa ba na sanya fatar jiki kiba, kuma hakan zai janyo fatar fuska cika, sai a ga mutum tsabagen kiba ya fi shekarunsa.

Yana da kyau Uwargida ki san irin nau’in fatarki kafin ki yi amfani da kowane irin sabulu. Idan sabulu bai dace da fatar ki ba, zai iya sanya tsufan fata. A rage cin abinci mai dauke da mai, musamman idan shekaru sun ja. Bai kamata idan an kai shekaru arba’in a rika cin naman shanu ba. Yawan cin irin wadannan abubuwa yana janyo ciwon kafa da sanya mutum tsufa. Yana da kyau a ki rika samun barci a kalla awa bakwai a kullum, rashin samun barci a kan kari na sanya tsufa da wuri .

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Ake Kiwon Kajin Gidan Gona (1)

Next Post

Wang Yaping: ’Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

Labarai Masu Nasaba

Saboda Kauce Wa Bacin Rai Daga Teloli Na Koyi Dinki Da Rana Tsaka — Hadiza D. Auta

Saboda Kauce Wa Bacin Rai Daga Teloli Na Koyi Dinki Da Rana Tsaka — Hadiza D. Auta

by Rabi’at Sidi B.
1 week ago
0

...

Fyade

Dole A Hada Hannu Don Kawo Karshen Fyaden Kananan Yara -Sameerah Shinko

by Yusuf Kabiru
2 weeks ago
0

...

Hafsat

Abubuwan Da Suka Zaburar Da Ni Zuwa Harkar Siyasa – Hafsat Azare

by Bilkisu Tijjani
1 month ago
0

...

Sana'a

Ina Tausaya Wa Macen Da Ba Ta Da Sana’a —Lubabatu Ingawa

by Rabi’at Sidi B.
1 month ago
0

...

Next Post
Jannati

Wang Yaping: ’Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: