Maigari Abdulrahman">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Abubuwan Da Masu Shirin Shiga Sansanin NYSC Ke Bukata

by Maigari Abdulrahman
June 18, 2019
in NAZARI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Saura ‘yan kwanaki kadan ma su hidimar kasa rukunin ‘B’ su shiga sansanin horas da ma su hidima da za a gudanar a dukkanin fadin jihohin Najeriya.

Kan haka, muka ga dacewar rubuta jerin wasu abubuwan da sabon-shiga ke bukatar zuwa da su a sansanin.

samndaads

Wannan rukunin farkon, su ne mafi bukatuwa da mutum ya kamata ya tabbatar ya dauka a tare da shi.

1. Katin shaidar makaranta (ID Card)

3. Takardar kira ta hukumar NYSC

4. Hotuna fasfo wanda ba a dade da dauka ba (passport photograps)

Daukar wadannan zai baka damar kammala rijistar rukunin farko a sansanin, wanda zai baka damar karbar kaya (uniform).

Baya ga wadannan, akwai kuma karin wadansu abubuwan da mutum zai iya bukata a yayin zaman sa a cikin sansanin.

1. Man goge hakora, buroshin wanke baki, sabulun wanka

2. Omo da sabulun wanki

3. Kayan al’ada (ga mata)

5. Tawul

6. Bokiti domin yin wanka da wanki

7. Karin gajeren wando da farar riga farare duka

8. Zanen kwanciya (Akwai katifa a can)

9. Turaren sakawa a jiki

10. Takalma silifas (domin zuwa ban daki da sauran su)

11. Mashaci, kayan gyara kai da jiki da sauran su

12. Gidan sauro

13. Kular saka abinci, kofi, chokali da makamaitansu

14. Kwaduna domin rufe jaka/akwati

15. Akwatin yin karin cajin waya

Duka wadannan abubuwan da aka lissafa, ba wai ba a samun su a sansanin ba ne, a’a, kusan akwai komai da mutum zai iya siya a can wanda ya ke bukata. To sai dai da mi, za ka samu abubuwan da tsada fiye da in ka siya tun a gida. Wani abu zai iya kusan nunka kudin sa, idan ma bai nunka ba a can. Saboda haka, siya a gida dabara ne.

Wani abu mai muhimmanci da ya kamata mutum ya tanada shi ne karin kayan da ake anfani da su, wato fararen gajerun kaya; wando fari da riga fara. Lalle sayensu na da muhimmanci domin mutum zai bukace su ko sun kai kala nawa.

A tsawon zama a sansanin, ana anfani da fararen gajerun kaya ne (idan banda ‘yan kwanaki kadan), saboda haka, sai ka kwatanta, kala nawa ka ke bukata a irin wannan yanayin ‘birkida jakin’ da za ku dinga yi a cikin kasa, ruwa ko rana. Iya yawan kayan ka, iya karancin yawan wanki da za ka yi. A gane kuma, akwai karancin lokaci, dan haka lokacin ba zai zama na wanki ba koyaushe.

Da fatar a je lafiya, a dawo lafiya, amin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Danladi Sankara Ya Taya Sanata Lawal Murnar Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Next Post

An Bukaci Masu Juna-biyu Su Kara Kaimi Wajen Sinadarin Karin Jini

RelatedPosts

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

by Maigari Abdulrahman
18 hours ago
0

Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...

National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Maigari Abdulrahman
6 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL...

Mata

Kayan Da’a Na Mata: Illa Ko Amfani? (3)

by Maigari Abdulrahman
6 days ago
0

Daga Sameerah Bello Shinko, 08025729364: Hana daukar Ciki: Wasu maganin...

Next Post
Daukar Ciki Bayan Shekara 35 Na Iya Haifar Da Matsaloli—Masana

An Bukaci Masu Juna-biyu Su Kara Kaimi Wajen Sinadarin Karin Jini

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version