Abubuwan Da Nijeriya Za Ta Mora Daga Taron Saudiyya Da Jamus
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Nijeriya Za Ta Mora Daga Taron Saudiyya Da Jamus

byKhalid Idris Doya
2 years ago
Jamus

Masana na ci gaba da fashin baki kan taron kolin da aka gudanar ka bunkasa tattalin arziki a tsakanin Afirka da Saudiyya da kuma Jamus.

A makon jiya ne aka gudanar da na Saudiyya, yayin da na Jamus kuma ya gudana a wannan makon.

  • Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
  • Zaben Kano: ‘Yansanda Da Masu Zanga-zanga Sun Yi Arangama A Kano

LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Kwamared Sabo Muhammad, wani mai sharhin lamuran yau da kullum da ke jihar Bauchi kan alfanun wannan taron, inda ya yi bayani kan taron Saudiyya.

A cewarsa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu irin wannan damar yake bukata domin jawo kasashe masu arziki kamar Saudiyya su zo su sanya hannun jari a musamman bangaren man fetur da iskar gas da sauransu. Na biyu kuma taron zai kara inganta kasuwanci da Saudiyya da sauran kasashen Labarawa. Abu na uku kuma shi ne domin ya tabbatar wa Saudiyya da sauran kasashe da suke da zimmar zuba jari, cewa yanzu ‘Njeriya’ wata kasa ce sabuwa wadda kofarta take a bude da ake kira ‘Free Market economy’ cewa za ka zo ka yi kasuwancinka cikin sauki kuma idan ka sanya hannun jarinka za ka samu riba mai inganci sannan babu wasu tarnake-tarnake da ake da su a baya, misali na idan ka sanya kudi babu wata wahala za ka fitar da kudinka kasar waje kamar yadda muka gani a baya. Manya-manyan kamfanoni na jiragen sama sun daina hulda da Nijeriya kamar British Airways da kuma kamfanonin da suke Daular Larabawa da kasashe da dama saboda ba su iya samun kudadensu na  waje da ake biya ta dalar Amurka.

“A wannan ziyarar na shugaban kasa ya tattauna da Yarima mai jiran gado Bin Salman har ma Saudiyya ta ke da zimmar cewa nan ba da jimawa ba za ta sanya kusan dalar Amurka miliyan dari biyar shi ne kimanin riyal din Saudiyya miliyan dubu biyu a matatun man fetur na Nijeriya wanda gwamnati take da su guda hudu kuma za su sanya hannun a kan yarjejeniyar yadda za a karfafa alakar na sauran fannoni da suka shafi makamashi ta yadda za a karfafa wa kan yadda ake tafiyar da harkokin makamashi na zamani kuma shi ministan tattalin arziki na kasar Saudiyya ya ce nan da karshen wannan shekarar ko a zangon farko na shekarar da za mu shiga za a zo a yi jarjejeniya a sanya hannu.”

A cewar masanin, Bola Tinubu na kokari ne don tabbatar wa kasashen da yake ziyarta cewa, gwamnatin Nijeriya a karkashinsa tana bi dukkanin dokoki na kasuwanci na kasa da kasa kamar misalign shawarar da ya bi ta cire tallafin mai da kudin da ake narkawa wajen kare darajar Naira.

“Sannan na uku kuma, tunin a kan haraji an riga an yi kwamiti mai karfi wanda zai cire dukkanin wata sarkakiya na na haraji daban-daban da suke sanya wa kamfanoni masu hannun jarida. Da kuma bukatar da shi shugaban kasa ya ke da ita cewa su yi aiki da kasashen duniya musamman ita Saudiyya da sauran kasashen duniya musamman na Labarawa domin a samu a yaki matsalar tsaro ta yadda shi shugaba Tinubu ke son Nijeriya da Saudiyya su yi aiki tare domin yaki da akidun kungiyoyi irin su Boko Haram, ISWAP da sauransu da ke Nijeriya da yankin Chadi.”

“Abu na uku idan suka yi aiki tare a bangaren tsaro akwai akwai yiwuwar ita kasar Saudiyya za ta fi bai wa Nijeriya taimako na kayan aiki da kuma na kudade da canza bayanai na sirri tun da akwai ISIS a Nijeriya kuma ISIS suna da karfi a kasashen Labarawa ka ga Nijeriya za ta samu bayanan sirri daga wajen  Saudiyya domin dakile kungiyon ISIS-ISWAP da sauran kungiyoyin ta’addanci, shi ya sanya ma a ziyarar akwai mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado da shugaban tattara bayanai na sirri Malam Abbakar, to dukka wadannan alkairi ne, amma gaskiya ba za a ga wadannan alkairan a yanzu-yanzu ba.” Ya bayyana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Next Post
Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Wani Sinadarin Gishiri A Nijeriya

Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Wani Sinadarin Gishiri A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version