Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTON MUSAMMAN

Abubuwan Da Suka Biyo Bayan Arangamar ‘Yan Gandujiyya Da Kwankwasiyya

by Tayo Adelaja
September 16, 2017
in RAHOTON MUSAMMAN
7 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka da Mustapha Ibrahim Tela, Kano

Tun bayan arangama tsakanin masu biyayya ga tsagin Kwankwasiyya da kuma masu biyayya ga sabuwar darikar Gandujiyya, ake ta samun musayar ra’ayin kan musabbabin rikicin da kuma abubuwan da suka biyo baya.

samndaads

Tun faruwar wannan lamari, mutane masu mambancin ra’ayi ke ta furta albarkacin bakinsu, wasu na gani rashin adalci aka yi wa ‘Kwankwasawa, yayin da wasu ke gani su Kwankwasawa ne suka yi sanadin faruwar rikicin.

Ganin irin rikicin baka da hakan ya haifar, ya sanya Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mallam Muhammad Garba fitowa karara tare da nisanta Gwamnatinsu da wannan aika-aika.

A jawabinsa, Mallam Muhammad Garba ya ce ‘yan Kwankwasiyya ne suka afkawa junansu sakamakon rashin cika alkawarin biyansu kudi naira dubu biyar-biyar da aka ce za a ba su, maimakon haka sai aka bi su da naira dubu biyu kowannensu, wanda hakan ne ya fusata wassu suka afkawa wadanda suke zargi da yi masu kwangen kudi.

Haka kuma ya kara da cewa matasan da suka taru a wannan wuri, ‘yan Kwankwasiyya sun debo su ne daga wasu jihohi, inda ya ce akwai na Jihar katsina, Jigawa da kuma Kaduna baya ga wadanda suke cikin garin Kano.

Ya ce sun tabbatar da hakan ne bayan da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce a dauki nauyin jinyar wadanda suka samu raunuka ciki har da ‘yan gandujiyya da abin ya shafa. Haka kuma ya kara da cewa wannan bayani ya tabbatar da shi ne ta hanya bayanin da ya yi a matsayinsa na dan Jarida.

Taron Manema Labarai Da Jagororin Kwankwasiyya Suka Gudanar

Shugabannin Kungiyar Kwankwasiyya dake biyayya ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Injiya Sanata Rabiu Musa Kwakwaso sun zargi jami’an tsaro da hannu dumu-dumu cikin harin da aka kai masu, yayin Hawan Daushe a Kano, inda karara suka dora alhakin hakan kan Gwamna Ganduje, suka ce mutanen da harin ya rutsa dasu sun hada da Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano a lokacin mulkin Kwankwaso, Rabiu Sulaiman Bichi, Tsohon shugaban ma’aikantan fadar Gwamnatin jihar Kano a lokacin mulkin Kwankwaso, Dakta Yunusa Adamu Dan gwani, Alhaji Yahaya Musa Kwankwaso wanda kani ne ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran tsofaffin kwamishinonin da aka raunata a lokacin wannan hari.

Dakta Adamu Dangwani ya ci gaba da bayyana wannan harin a matsiyin wani shiri na ganin an kawar da Kwankwasiyya tare da dakatar da ayyukan da suke yi,  wanda gwamnatin Kano ke kokarin yi ta kowacce hanya. Dakta Dan Gwani ya bayyana mummunan kalamai da Gwamnan Kanon ya yi a lokacin taron nuna goyon baya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da alaka da wanann hari. Shugabannin sun zargin dan majalisar Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar birni da kewaye Alhaji Baffa babba Dan Agundi da Alhaji Sani Lawan Kofar Mata da cewar su suka jagorancin wanann ta’addanci.

Ya ce, “idan za a iya tunawa Gwamna Ganduje ya ce ayyukan da ‘yan Kwankwasiyya ke yi  a wannan kasa bala’i ne, masifa ce, shashanci ne, iskanci ne kuma munafunci ne.”

Dan Gwani ya ce dalilin da ya sa gwamna yin wannan magana akan shugabannin jam’iyyar APC na Kasa  bai wuce kin yarda da suka yi da bukatar tabbatar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban Jam’iyar APC na Jihar Kano ba.

Har ila yau, Dan Gwani ya kara jaddada cewar, “sakamakon wadannan munanan kalamai na Ganduje ya yi, su ne sanadiyya harin da aka kaiwa ‘yan Kwankwasiyya ranar biyu ga watan Satumba 2017, wanda ‘yan dabar Gandujiyyar karkashin jagorancin Baffa Babba Dan Agundi da Sani Lawan Kofar Mata, tare da gudunmawar jami’an tsaro wanda suka hada da A/C Metro Balarabe Sule, wanda shi ne tsohon jami’an tsaro na gidan Gwamnain Kano da O/C Anti Daba  SP Tela da kuma mai taimakawa Abdullahi Abbas na musamman, wadannan sune suka kitsa yadda aka kaiwa ‘yan Kwankwasiyya da suka taru a kofar Kudu domin mika gaisuwa ga mai martaba Sarkin Kano.

“Wannan hari an yi shi domin a kawar da shugabannin Kwankwasiyya kamar yadda Gwamna Ganaduje ya bayyana niyyarsa ta lalata tafiyar Kwankwasiyya ta kwacce hanya a wurin addu’ar dodorido da ya shiryawa Shugaba Muhammadu Buhari. A cikin shugabannin Kwankwasiyya da wannan hari ya shafa akwai injiniya Rabiu Sulaiaman Bichi, Dakta Adamu dan Gwani, Yusif Bello Danbatta,  Alhaji Yahaya Musa Kwankwaso, Kwamared Baba Abubakar Umar,  Zainab Audu Bako da dai sauransu.

“Wanann mummunan al’amari idan aka bar shi ya ci gaba da faruwa zai kawo rashin zaman lafiya a jihar nan, haka na akwai yiwuwar komawa gidan jiya kamar yada aka yi siyasar Jamhuriyya ta biyu.

“Saboda haka ya ku ‘yan jarida ku sani, akidar Kwankwasiyya an kirkire ta ne domin taimakawa masu karamin karfi tare da yi wa kowa aiki ba tare da nuna bambanci siyasa, addini ko al’ada ba. An san ‘yan Kwankwasiyya da son zaman lafiya da aiki tukuru, sannan ‘yan kwankwasiyya ba sa tada fitina kuma basa daukar wulakanci, daukar bangare da jami’an tsaro suka yi aka yi wa mutanen da ba su ji ba basu gani baahani, ba zai tafi a banza ba, a lokacin da muke bawa dandazo magoya bayanmu hakuri da cewa kada su dauki doka a hannunsu, dole mu dauki matakin da ya dace ta hanyar tabbatar da adalci ga wanda aka zalunta.” A cewar Dan Gwani.

 Martanin Hukumar ‘Yan Sanda Ga ‘Yan Kwankwasiyya

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano Rabiu Musa ya yi tsokaci kan korafin da Kungiyar Kwankwasiyya ta gabatar gaban hukumar dake lura da harkokin rundunar ‘yan Sanda ta Kasa bisa zagin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da hada kai da Gwamna Ganduje domin kai  farmaki a ranar Salla. Ya ce wannan zukitamalli ne kawai da shantaka karya.  Kwamishinan ya shaidawa manema labarai cewa, taron manema labarai da kungiyar Kwakwasiyya ta gabatar ya dauki hankalin rundunar ‘yan sadan Jihar Kano sakamakon kirkirar karya, kazafi da borin kunyar da magoya bayan Kwankwasiyya suke na zargin jami’an rundunar ‘yan sanda cewa suna da hannu cikin rikicin siyasar da ya faru tsakanin su da ‘yan Gandujiyya.

Kwamishinan ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya tunawa ‘yan Kwankwasiyyar cewar lamarin ya faru bayan taruwar da suka yi a kofar asibitin Yara na Hasiya Bayero inda suka hada magoya bayansu daga jihohi daban-daban, yayin da tawagar Gwamna Kano ta tunkaro sai suka fara ihun ba-ma-yi ba-ma-yi.

Magaji Musa Majiya ya ci gaba da cewa lamarin ya faru a bikin Hawan Daushe rana ta biyu a bukukuwan sallah, taron da masarautar Kano ke shirya domin al’adun Kano ba siyasa ba.

Ya ce a wannan ranar ne dubban ‘yan Kwankwasiyya suka taru a kofar asibitin Hasiya Bayero wadanda aka debo daga jihohin Sokoto, Kogi da sauran makwabtan jihohi da niyyar tada hargitsi a taron da masarautar Kano ke gudanarwa.

“Yan Kwankwasiyya sun yi ta ihun ba ma yi, kuma haka ya faru lokacin tawagar Gwamna Ganduje ta gabato wurin kuma suka fara jifa da duwatsu.” A cewar ‘Yan Sanda.

Karakara ta ce, irin sanin da suka yi wa siyasa a da, yanzu komai ya canja, a cewarta yadda ake tafiyar da abokin adawa adawa shi ne, idan kun hadu da wanda ba ya tare da akidarka abinda sai a yi juna alhairi, gaisuwar mutunci da girmama juna.

“A zamanin siyasarmu ba haka ake yi ba, kyautatawa ce tsakanin abokan hamayya, ta haka sai a wayi gari ka jawo wanda a baya ba tare kuke da shi ba.

“Allah ya ji kan Malam Aminu Kano, lokacin da ya duba kuma ya tabbatar da cewa zai yi wuya mu yi nasara a zabe, ni ya kira ya ce Hajiya Rakiya Karakara kin fahimci halin da muke ciki? Ban ga alamar samun nasara ba. Na ce masa abu guda za mu yi. Ya ce mene ne? Na ce mu hada gwiwa da abokana hammaya. Nan take ya amince, sai ga shim un yi nasara a Kano da Kaduna.

“Duk ‘yan siyasar wancan lokacin suna  daraja juna, sau 33 ina zuwa Makka, zamanin Gwamnatin Rimi, duk da ina ‘yar adawa, tare matarsa Hajiya Sa’a da kuma shi Gwamna Rimi muke yin aikin Hajji. Wallahi ina tabbatar maka da cewa ba inda ba da ni aka zaga kasar nan ba a lokacin NEPU. Amma shi kenan saboda rashin sanin kimar jama’a a dauki nauyin wasu su afkawa shugabanni saboda kawai suna da irin tasu akidar daban?

SendShareTweetShare
Previous Post

An Yi Wa Mai Tsaron Ragar Burnley Tiyata

Next Post

Sammanin Fatihu: Attajirin Da Ya Fara Kasuwanci Da Jarin Dubu Biyu

RelatedPosts

JIBWIS-FCT

Kwamitin Tallafa Wa Marayu Na JIBWIS-FCT Ya Gudanar Da Taron Karshen Shekara

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Kwamitin tallafawa marayu na Jama’atu Izalatul Bid’a Wa’ikamatis Sunnah dake...

Sana’ar Mazarkwaila

Yadda Sana’ar Mazarkwaila Ta Sauya Daga Rawar Doki Zuwa Rawar Babur

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Mai karatu, yau alkalaminmu zai duba wani sashe ne na...

Hanyar Abuja-Kaduna

Tabbatar Da Tsaro: NAF Ta Gundunar Da Gagarumin Atisaye A Hanyar Abuja-Kaduna

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

A ci gaba da kokarin da ta ke yi na...

Next Post

Sammanin Fatihu: Attajirin Da Ya Fara Kasuwanci Da Jarin Dubu Biyu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version