Rabiu Ali Indabawa" />

Abubuwan Da Suka Biyo Bayan Canja Shugabannin Tsaron Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun afkawa sansanin ‘yan ta’addar Boko Haram a dajin Sambisa. Harin ya biyo bayan sa’o’i kadan da aka nada sabbin hafsoshin sojojin Nijeriya.
Sojojin sun bayyana cewa sun wargaza sansanin ‘yan ta’adda 4 a yankin na Sambisa. Sojojin Nijeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta ‘Multinational Joint Taskforce, MNJTF’, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.
An bayyana nasarar ne ‘yan sa’o’i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja. Aikin da Birdiya Janar Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.
Wata majiyar soji ta fadawa PRNigeria cewa sansanonin sun kasance sansanin horar da mayakan kungiyar tare da girke dakaru masu shirin ko-ta-kwana a shirye-shiryen kai harin kwanton bauna a wuraren sojojin da ke kusa.
Majiyar ta ce an kashe wasu kwamandojin kungiyar ‘yan ta’addar da kuma mayaka masu yawan gaske, yayin da yawa kuma suka samu munanan raunuka yayin kai harin.
An kame dimbin kayan aiki daga hannun ‘yan ta’addan yayin da kayan abinci, Na’urar abubuwan fashewa, bama-bamai, abubuwan dinkin kayan sawa duk an lalata su. “Mun share Maiyanki, Darulsallam, Bula kurege kuma yanzu mun karbe Izza, dukkansu tsoffin wuraren Boko Haram ne masu karfi. Sojojinmu sun sha kai hari mafakarsu, cikin dare, amma duk an fatattake su yayin da aka yi wa makiyan mummunar rauni. Ya kuma bayyana cewa soja daya ne ya rasa ransa yayin da sojoji uku suka ji rauni.
A wani labarin kuwa, Jami’an sojojin Nijeriya a barikinsu sun cika da farin ciki yayin da suka samu lamarin sallaman tsoffin hafsoshin tsaro a ranar Talata da kuma sanar da wadanda za su maye gurbinsu. Wani bidiyon mai dakikai 20 ya nuna lokacin da wasu Sojojin ruwa a barikinsu da ake kyautata zato na birnin tarayya suke ihu suna rawa kan labarin.
SaharaReporters ta ruwaito cewa, irin haka ya faru a sauran barikin sojoji dake fadin tarayya. Bayan kiraye-kiraye daga ‘yan majalisun tarayya da manyan masu ruwa da tsaki a Nijeriya suka yi wa shugaba Buhari kan ya sallami hafsoshin tsaro, kuma ya nada wasu, Buhari ya amsa wannan kira. Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Nijeriya a ranar Talata, 26 ga watan Janairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba. Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, shi ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.
A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AbM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.
Wani rahoton kuma ya nuna cewa, dakarun sojin Nijeriya na cigaba da samun nasara a yakin da suka yi da ‘yan ta’adda a kasar. Rundunar sojin ta sanar da cewa Dakarun Operation Tura Takaibango sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda a Borno da Yobe.
Sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigu da harsasai yayin da suke cigaba da bin sahun ‘yan ta’addar da suka tsere, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito. Sanarwar da Dirakta mai rikon kwarya na sashen yada labarai na rundunar, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar, a ranar Litinin, ta ce sojojin sun yi nasarar taka wa ‘yan ta’adda birki a jihohin Yobe da Borno.
Sanawar ta ce, “Dakarun Operation Tura Takaibango, wani sashi na Operation Lafiya Dole a Arewa maso Gabas na cigaba da dirkake ‘yan Boko Haram da ISWAP a yayin da suka kai musu hari a maboyarsu a garin Chindila a Yobe da Mayankari a Borno. “A ranar 25 ga watan Janairun 2021, misalin karfe 1 na rana, dakarun bataliya ta 233 da ke Babangoda, yayin sintiri sun yi arangama da ‘yan Boko Haram a kauyen Chindila.
Sun bude musu wuta inda suka yi nasarar halaka biyar cikinsu yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga. “Kayayyakin da suka kwato sun hada da; bindiga kirara Ak 47 guda 3, da alburusai. Sojojin sun bi sahun abokan gabar kuma suna cigaba da mamaye yankunan.”
An kuma kashe ‘yan bindiga da dama a wasu kananan hukumomin jihar Kaduna. kanananan hukumomin sun hada da Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan a ranar Talata.

Exit mobile version