Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
A ranar Juma’a 5 ga Fabrairu, 2021, Malam Ibrahim Abdul’aziz, gawurtaccen dan jarida mai zaman kanshi ya rasu, biyo bayan hatsarin da ya rutsa dashi akan hanyarsa ta tafi garin Bauchi domin halartan bukin daurin aure.
Tuni dai aka gudanar ma sa da sallar jana’iza, bayan dawo da shi Yola fadar jihar Adamawa, domin iyalanshi su gana dashi ta karshe.
Yanzu haka dai jama’a na tuturuwa gidan mamacin domin jajantawa iyalansa, cikin mutanen da suka jajantawa kungiyar ‘yan jaridu NUJ da kuma iyalan mamacin sun hada da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri.
“Mutuwar Abdul’aziz ta zo ne a lokacin da kafofin yada labarai ke bukatar amfana da irin hazakar da yake dashi” inji sanarwar.
Haka kuma sanarwar gwamnan ta bukaci iyalan mamacin da su dauka jarabawace daga Allah su dauki angana, da jabawar a daidai wannan lokaci mai daci.
Marigayi Abdul’aziz, baya ga kwarewa da jajircewa kan aikin jarida haka kuma akwaishi da hakazar tafiyar da ayyuka da dama a lokaci guda.
Alhaji Muhammad El-Yakuk, shugaban kamfanin sadarwa ta Gotel Communications, ya ce “gaskiya rasuwan Ibrahim Abdul’aziz, babban rashine ba ga ‘yan uwansa kadai ba, rashice ga jama’ar jihar Adamawa da Nijeriya baki daya.
“Kuma mun rasa abokin aiki mun rasa amini mun rasa dan ‘uwa, mun rasa wani wanda yake tada masu aikin jarida a duk lokacin da su ka yi kuskure, don haka wannan rashin ba na iyalanshi bane kadai, rashine na mu gabaki daya, Allah ya jikansa da rahma” inji El-Yakuk.
Haka shima tsohon shugaban gidan radio ABC Yola, Malam Sambo Abubakar, ya ce “gaskiya rashin Ibrahim Abdul’aziz ya bar gibe wanda da wuya a ciketa, mutum ne tsayayye a aikin jarida wanda kuma ba zaibar komai ba sai ya tabbata ya cimma burinsa na samarwa jama’a abinda sukeso su ji ko su gani.
“Saboda haka wannan gibing za’a dade ba’a samu wanda zai cikeshi ba, gaskiya munyi rashi Allah ya jikanshi da rahma, ya yafe mishi kurakuransa” inji Sambo.
“Akwai abubuwa da dama da za mu tuna Abdul’aziz da su, idan muka tuna da shirin tsaka-mai wuya, Abdul’aziz ya bada gudumawa sosai da bajinta matuka, a jihohin Adamawa/Taraba, ya kamata ‘yan jarida su koyi kaskantar da kai, su koyi darusa daga rayuwarsa” inji Dedan.
Haka suma sakwannin da su aike na ta’aziyya, Mamba mai waklitar Numan, Demsa da Lamurde a majalisar wakilai ta kasa Kwamoti La’ori, Sanata Aishatu Ahmed Binani, sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa, sun bayyana Abdul’aziz a matsayin hazikin dan jaridar da ba’a mance dashi ba.
Kafin rasuwarshi ya yi aiki a kafafen sadarwa da dama, da su hada da Daily trust, Blueprint, Premium Times, New Telegraph, da sashin Hausa na muryar Amurka (VOA).
Haka kuma ya yi aiki da FRCN Fombina FM, Bissoin Radio, da kuma Gotel Communications, baya ga kafafen sadarwar dandalin sada zumunta, kafin wannan mummunan hatsarin mota ya rutsa da shi.