Abba Ibrahim Wada" />

Abubuwan Da Suka Faru A Shekara Ta 2020 Data Gabata A Bangaren Wasanni

Editorial Use Only Mandatory Credit: Photo by Javier Garcia/BPI/Shutterstock (10577674db) Goalkeeper Jan Oblak of Atletico Madrid Liverpool v Atletico Madrid, UEFA Champions League, Round of 16, 2nd Leg, Football, Anfield, UK - 11 Mar 2020

Za a iya cewa shekarar 2020 tazo da abubuwan ban mamaki wadanda babu wanda yayi zaton su a shekarar 2020 kuma tunani ba zai taba kawowa zasu faru ba musamman buga wasan kwallo babu ‘yan kallo.

Shekara ta 2020 ta zama mai cike da kalubale a fadin duniya har da bangaren wasanni, bayan da cutar korona ta dagula al’amura a fadin duniya sannan ta tsayar da abubuwa da dama ciki kuwa hard a wasannin kwallon kafa.

Cutar ta sa an dauke wasu wasannin daga lokacin da aka tsara zuwa wani lokacin nan gaba, sannan kuma an koma buga wasu ba magoya baya, bayan da wasu kungiyoyin suka bukaci ‘yan wasa su rage albashi, wasu ma suka yafe na wasu watannin a wasu kungiyoyin musamman a kasar Sipaniya da Faransa.

Cikin shekarar nan fitattun ‘yan wasa sun mutu da suka hada da Diego Maradona da Kobe Bryant da sauransu sannan duk da bullar cutar korana an ci gaba da wasanni, bayan da aka dauki matakan hana yada annobar, hakan ya sa an samu ‘yan wasa da kungiyoyi da jami’ain da suka taka rawar gani a shekarar 2020.

Watan Janairu

Dan kwallon tawagar Italiya, Daniele De Rossi ya yi ritaya daga buga wasa, dan wasan ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Roma kwallo a kakar wasa 18 inda ya taimakawa kungiyar ta lashe wasanni da dama hadi da lashe gasar cin kofin Seriya A ta kasar Italiya.

A karon farko dan kwallon tawagar Senegal da Liverpool, Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na shekara ta 2019 kuma shine karo na farko da dan kasar Senegal ya lashe kyautar tun bayan El-Hadji Diop.

A dai shekarar ta 2020 kuma a watan Janairu, tsohon zakaran kwallon kwandon Amurka da Los Angeles Lakers, Kobe Bryant da ‘yarsa Gianna suka mutu a hatsarin jirgi a jihar California dake kasar ta Amurka.

Marigayi Bryant, ya lashe kofin NBA a Lakers karo biyar 2000 da 2001 da 2002 da 2009 da kuma 2010) sannan hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ta soke gasar da ya kamata China ta karbi bakunci a watan Maris din shekara ta 2020 sannan  an kuma cimma wannan matsayar saboda bullar cutar korona.

Watan Fabrairu

‘Yar kasar Amurka, Sofia ce ta lashe gasar kwallon tennis ta Australin Open ya yinda a bangaren maza kuwa, Nobak Djokobic ne ya zama zakara a gasar ta Australian Open ta 2020 a wasan Dambe kuwa dan damben Burtaniya Tyson Fury ya kawo karshen shekara biyar da Deontay Wilder ya yi da kambun WBC.

Watan Maris

A cikin watan Maris aka tsare fitatcen dan kwallon Brazil, Ronaldinho da dan uwansa Roberto Assis a kasar Paraguay bayan an same su da laifin shiga kasar da fasfo na jabu inda kuma daga karshe aka yanke wa Ronaldinho hukuncin zaman yari.

Hukumar kwallon kwandon Amurka ta dakatar da wasannin NBA, bayan da dan wasan Utah Jazz, Rudy Gobert ya kamu da cutar korona

A shekarar ne kuma aka dakatar da wasannin gasar cin kofin zakarun turai na UEFA Champions League da na Europa League don gudun yada cutar korona bugu da kari hukumar kwallon kafa ta Turai ta dage gasar Euro 2020 zuwa shekara daya saboda cutar korona sannan haka ma aka dage gasar Copa America ta shekara ta 2020 zuwa shekara daya don gudun yada annobar.

Haka ma a dai hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa tadage Fifa Club World Cup da ya kamata a yi a China itama hukumar UEFA ta dage wasannin karshe na Champions League da na Europa League saboda gudun yada annobar.

Kamitin Olympic na duniya shima ya sanar da dage wasannin da birnin Tokyo zai karbi bakunci, sakamakon bullar cutar korona sai dai kwamitin Olympic na duniya ya ce zai gudanar da wasannin tsakanin 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Agusta a Tokyo da na nakasassu tsakanin 24 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumbar shekara ta 2021.

Watan Afrilu

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta soke duk wani wasa tsakanin kasa da kasa don gudun yada cutar korona a watan Aprilu sannan a watan ne dai aka dage gasar tseren motocin Formula 1 da ya kamata a yi a kasar Canada, saboda tsoron yada cutar korona.

An dage gasar tseren kekuna ta Tour de France zuwa 29 ga watan Agusta, saboda cutar korona itama gasar Berlin Marathon a karon farko, wadda aka fara tun 1974 an dage ta zuwa wannan shekarar da muka shiga saboda Korona.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, itama ta dage wasannin kwallon mata UEFA Euro 2021 zuwa 2022, saboda cutar korona sannan itama Fifa ta sanar da za ta raba kudi dalar Amurka 150 ga mambobinta don rage radadin cutar korona sannan an soke gasar kwallon Faransa aka bai wa kungiyar Paris St Germain kofi a matsayin wadda ta lashe kakar 2020.

Watan Mayu

A watan Mayu aka amince hukumomin kwallon kafa su fara amfani da dokar sauya ‘yan wasa biyar a cikin fili, saboda cutar korona sannan a cikin watan dai an ci gaba da wasannin Bundesliga na kasar Jamus, bayan dakatar da fafatawar cikin watan Maris.

Suma hukumomin gasar Premier League ta Ingila a cikin watan suka bayyanacewa  za ta ci gaba daga ranar 17 ga watan Yuni ba tare da ‘yan kallo ba daga kasar Italiya ma Serie A kuwa ta tabbatar cewar 20 ga watan Yuni za’a ci gaba da fafatawa ba ‘yan kallo su kuwa mahukuntan gasar Spanish La Liga suka sanar da za’a ci gaba da wasanni ranar 11 ga watan Yuni.

Watan Yuni

A watan Yuni kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta lashe gasar Copa Italia, bayan doke Juventus 4-2 a bugun fenariti ya yinda a shekarar ne kuma New York Marathon da ya kamata a yi a Nuwamba aka dage zuwa Nuwambar wannan shekarar ta 2021 don gudun yada cutar korona.

Fifa ta sanar cewar Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a kwallon mata a shekarar 2023 itama kungiyar Liverpool ta lashe gasar Premier League a karon farko tun bayan shekara 30.

Barcelona ta dauki dan kwalon Juventus, Miralem Pjanic kan dalar amurka miliyan 67 a watan Yunin daya gabata sannan daga nan gida kuma hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta dage gasar kofin Afirka na 2021 da ya kamata Kamaru ta karbi bakunci inda ta ce sai a shekara ta 2022 za a buga saboda gudun yada cutar korona.

Watan Yuli

A cikin watan Yuli kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya ci kwallo ta 700 a raga a tarihin buga kwallonsa sannan a dai cikin watan ne Bayern Munich ta lashe German Cup, bayan da ta doke Bayer Leberkusen daci 4-2.

Sannan an fara kakar Formula da Australian Grand Prid ta shekarar wadda aka dunga sauya lokuta, kuma direban Marsandi, Baltteri Bottas shi ne ya zama zakara sannan daga kwallon kafa kuma hukumar UEFA ta sanar da dage dokar hana Manchester City shiga gasar Champions League shekara biyu.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar La Liga kuma karo na 34 jumulla, bayan doke Billareal 2-1 sannan tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Andre Schurrle ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo.

Ba wanda aka bai wa kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2020 wato Ballon d’Or, saboda cutar korona sannan Paris Saint-Germain ta lashe 2020 French Cup, bayan da ta doke Saint-Etienne 1-0.

A cikin watan ne dai dan wasan tawagar Ingila da Leicester City, Jamie Bardy, ya zama mai yawan shekaru da ya ci kwallo a gasar cin kofin Premier League.

Watan Agusta

A watan Agusta kungiyar Arsenal ta lashe gasar cin kofin kalubale na FA Cup karo na 14 jumulla, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea daci 2-1 a filin wasa na Wembley dake babbar birnin kasar Ingila, London.

Shima dan wasa Ciro Immobile ya lashe takalmin zinare a cikin watan na Agustan daya gabata bayan da ya ci kwallo 35 a wasanni 36, kuma shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Italiya da kuma nahiyar Turai.

Shima dai dan kwallon Manchester City, Kebin De Bruyne ya lashe kyautar dan kwallon gasar Premier League da ba kamarsa sannan Sebilla ta lashe 2020 UEFA Europa League, bayan da ta doke Inter Milan da ci 3-2 itama kungiyar Bayern Munich ta lashe Champions League, bayan da ta doke Paris Saint-Germain 1-0.

Arsenal kuwa ta zama zakara a shekarar 2020 English FA Community Shield, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 5-4 a bugun fenariti sannan gwarzon dan wasa AC Milan, Zlatan Ibrahimobic ya sanar da zai koma AC Milan da buga wasa.

Watan Satumba

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya sanar zai karasa kaka daya da ta rage masa a Barcelona sai kuma Dominic Thiem wanda ya lashe 2020 US Open, bayan doke Aledander Zbereb a wasan karshen da suka gwabza.

Dan kwallon tawagar Wales, Gareth Bale ya koma Tottenham don ci gaba da buga gasar Premier League daga Real Madrid a matakin aro sannan itama kungiyar Atletico Madrid ta sanar da daukar Luis Suarez daga Barcelona.

Watan Oktoba

Bayern Munich ta lashe 2020 German Super Cup, bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2 sannan a kasar ta Jamus dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Turai na 2020.

Manchester United ta sanar dadaukar dan kwallon Uruguayan, Edinson Cabani kan yarjejeniyar shekara a matakin wanda bai da kungiya sannan Iga Swiatek bta doke Sofia Kenin ta kuma lashe 2020 French Open.

A karawar maza kuwa Rafael Nadal ne ya zama gwani, bayan da ya casa Nobak Djokobic a kasar Amurka kuma Los Angeles Lakers ta doke Miami Heat 106-93 ta kuma lashe kofin NBA a karon a shekara 10 kuma na 17 jumulla sannan dan kwallon Argentina, Pablo Zabaleta ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo.

Watan Nuwamba

Arsenal ta doke Manchester United 1-0 a gasar Premier League a Old Trafford a karon farko tun bayan shekara ta 2006 sannan Direban Marsandi, Lewis Hamilton ya lashe 2020 Formula 1 ta duniya kuma kofi na takwas jumulla.

Tsohon dan wasan Barcelona da Argentina, Jabier Mascherano, ya sanar da yin ritaya sai kuma Fifa wadda ta dage 2020 FIFA Club World Cup zuwa Fabrairun 2021, don gudun yada cutar korona.

Sai kuma babban rashin da akayi a shekarar data gabata ta Diego Maradona wanda ya mutu wanda tsohon dan wasan Barcelona ne da Napoli tsohon dan kwallon tawagar Senegal, Papa Bouba Diop shima ya mutu.

Watan Disamba

Napoli ta sanar da sa sunan filinta zuwa Diego Armando Maradona bayan rasuwar tsohon dan wasan sannan shima tsohon kocin Liverpool, Gerard Houllier ya mutu sai Robert Lewandowski wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na shekarar 2020 sai kuma Dogon Kyallu ya zama sarkin damben gargajiya, bayan da ya buge Ali Kanin Bello a Kano.

Exit mobile version