Bello Hamza" />

Abubuwan Da Suka Gurbata Dabi’ar Arewa Da Makomarta (II)

Ci gaba daga makon jiya:

Idan za ku tuna a makon jiya muka fara batu a kan Iklisiyya da suke bata dabi’u a arewa. Yau za mu karkare wannan makalar. Ita dai ‘iklisiyya’, watu wasu kalmomi na karin magana ko fasaha ko hikima wadanda muka saba da su, amma kuma watakila sukan yi tasiri a cikin rayuwarmu, domin la’alla su canja nazari, fahimta, ra’ayi da sauransu. Kamar dai yadda bayaninsu ya gabata a makon jiya. Ga ci gaban.

1.Allah Ne Ya Kaddara: Wannan furucin ko lafazin, ya kan kai ga janyo mutum ya gaza yin abun da ya dace a lokacin da ya dace, sau tari mutum kan jingina kalmar daga Allah ne ya kaddara, wannan yana fitar da zimmar da kumajin yin ababen da suka dace.

2.Ka Bar Wa Allah: Wannan karin maganar tana rage wa dan adam, kungiya ko gungun jama’a neman hakkinsu daga kowace irin zalumci da aka musu. A al’adar dan adam, da zarar aka yi masa wani abun da bai dace ba, za ka ji wasu na ce ka dogara ga Allah ka barshi ga Allah. Eh haka ne, komai akan barshi ne ga Allah musamman wajen neman zabinsa, amma wasu iklisiyyar ana kawai amfani da shine wurin rage wa mutane kumajin neman hakkinsu.

3.Ka Dangana Ga Allah: (Depend on God) ba tare da dangana ga wani wurin neman tallafinsa ko agajinsa ba. In mutum bai yi a hankali ba, sai ya gaza neman agajin wani ko wasu tare da amfani da wannan furucin.

4.Waye Ya Ke Haka Yau/ Ba’a Haka Yanzu: ‘Wannan iklisiyyar tana gayar rage wa mutane kumajin yin ababe na daban, gwargwadon abun da mutum yayi imani da shin a kwarai ko marar kyau hakan na rage armashin shugaban na kwarai daga kasancewarsa ko abun da suke son ya kasance a ofis.

5.Zamani Ne Ya Kawo/ Ya Abaci: Haka siddan sai ka ji mutum ya furta cewar ai zamani ne ya kawo abu kaza domin kawai ya samu gansuwar daukaka darajar abu ko na al’adar da ya shude ga yaran. Ko yake son a bi son ransa, wanda wanna furucin a wani lokacin kan zama a’ala amma a wasu lokutan kan gurbata ci gaba da tarbiya. Misali yaro zai yi wani abun da ya saba wa ma al’adarsa, sai ya fake da cewar zamani ne ya kawo hakan, misali koda shigar malam Bahaushe ne a yanzu, sai ka tarar matasa ko yaran Hauwasa ba su son yin shiga irin ta malam Bahaushe, in ka nemi karin bayani sai a ce maka ai zamani ya kawar da wancan yanzu kaza ake yayi. Hakan na gurbata mana zamantakewa sosai, mu mance asalinmu muna rungumar na zamanin da wasu turasawa suka kaka ba ma.

6.Kai/Shi Waye: Shi/Ita waye? Iklisiyyar nan ta jingina Kalmar waye shi, na gayar rage wa al’umma samun ci gaba ko gyara ko ci gaba. Wani ko wata za ka iya tararwa sun zo da wani abu na ci gaba ko da zai kawo sauyi ko gyara a cikin al’umma, sai ka ji wani ko wasu su ce maka waye shi din? In aka jib a wani bane sai abun da ya kawo din ya raunana ko ma a ki na’am da shi. Idan kuma aka nemi sanin waye shi? Sai aka samu gwamna ne ko dan majalisa ne, abun nan ko marar kyau ne sai ka ga wasu sun dauka sun daura sun yi amfani da shi. Hakan na gurbata mana tarbiyya. Da janyo rashin adalci a cikin al’umma, misali wani ko wasu sun zalumci wani, idan aka ce waye shi? Sai aka samu soja ne ko dan sanda ko dan siyasa ko mai kudi, haka za ka ga jama’a sun rage karfin kumajin nema masa adalci ko tabbatar da an yi masa adalci kan zalumci da wane ya masa, kenan wannan furucin da muka aro muka daura na rage mana armashin rayuwa idan muka gaza lura da hakan.

  1. Wa Ya Isa? Kana Shugaba Din kuma? Kalmar waya isa tana hana mutane marasa karfi neman hakkinsu. Da zarar ka ji an ace waya ya isa, sai ai ka ga mutum ya ji raunin neman adalci a zuciyarsa, daga wurin wani da ya zalumce sa. Misali gwamnati, sai a ce maka wa ya isa… wa zai iya.. furucin ta hana jama’a neman hakkinsu ko rage musu armashin nema.

8.Duk Abin Da Zai Faru Ya Faru/ Ba Abinda Zai Faru: Furuci biyu a wuri daya, tana iya zuwa a wurare da dama; misali za a iya kakaba wa jama’a shugaban da basu so ko ana yunkurin daura musu wani da ba su so; masu yunkurn suna iya amfani da furucin duk abun da zai faru ya faru sai sun daura wane. Wannan Kalmar tana kara musu kumajin su yi duk abun da zuciyarsu ya raya musu koda ba daidai ba ne.

9.Wa Ya Isa?: Haka a nan ma, za mu iya buga misali da jawabin na baya. Za a iya yin komai a kuma dauko Kalmar wa ya isa a kakaba domin samun kwarin guiwa.

10.Rabu Da Su: mance da su, daina kulasu, haka sanya wasu dainawa ko kin amsar shawarar wasu gungun jama’a ko daidaiku daga gyara wa shugabani kurensu.

11.Amarya Ba Ta Laifi: Wannan iklisiyar na gayar sangarta amare da su yi abun da ransu yake so mai kyau ko marar kyau sai a jingina wa macen ai ke amaryace baki laifi. A daure da a cije da abun da ta yi. Hakan na gayar janyo matsala musamman a zaman takewar aure. Misali, ango zai ga abun da amaryarsa za ta masa wanda sam bai so ko ba daidai bane. Sai ya ce ai amarya ba ta laifi ba zai mata gyara kan wannan abun ba. Bayan tsawon lokaci idan amaryacin ya kara a lokacin da ita kuma ta saba da wannan abun angon ya fara nuna bai so ko bacin ransa a lokacin da gyaran zai masa wuya ko ma ya gaza yi.

12.Na Miji Ba Dan Goyo Da Zani Ba Ne: Furucin da muka ara da ke sanya mata shakku da rashin yarda da mazajensu wanda hakan ba daidai bane. Musamman a lokacin da miji ya tashi kara aure sai ka ji mace na cewa ba dan goyo da zani ba ne, alhali abun da zai yi ba haram bane.

13.So! So Ne Amma Son Kai Ya Fi: wannan abun na rage wa mutum son dan uwansa ko wasu ko ma dai nema musu sassauci ko tallafi domin a kowani lokaci wannan furucin ya aikemu da mu yi wa junanmu rowa ne.

14.Ni Ba A Koya Min Haka A Gidanmu Ba: Wannan furucin an fi samunsa a wurin matan aure musamman ‘yan amare. Da zarar miji ya nemi sanyata ko gyara mata wani sai ta ce ba ta koya a gidansu ba. A maimakon ta sake bude babin koyon zaman rayuwa a gidan aure a’a, sai ta ce bata koya a gidansu ba.

15.Allah Ya Sa Mu Dace: Addu’a mai kyau da jama’a kan yi amfani da furucin wajen dates zance ko neman a yi abun da ya kamata. Kwatsam sai ka ji Kalmar Allah sa mu dace a maimakon a yi abun da ya kamata.

16.Gaya Masa Ya/Ta Ji: An fi samun wannan Kalmar a lokacin jayayya, sai ka ji an ce fada mata dai da ta ji. Me za ta ji ko me zai ji? Su ji ra’ayin abun da yay i daidai da son zuciyar mai fadin hakan da wanda ya fadi Kalmar farko.

Filin namu zai tsaya haka sai kuma wani makon mu duba wani batun, amma kafin nan, yana da kyau muke kulawa da karim maganar da muke furtawa yau da gobe domin tasirin da hakan ke da su ga ci gabanmu. Na ku har kullum, Hassan Hassan

Exit mobile version