Abubuwan Da Suka Wajaba A Kiyaye A Mahautunmu Don Kiwon Lafiya

Mahauta

A watannin baya na taba yin rubutu irin wannan, wanda a wannan rubutun ma na kwaso da yawa daga cikin wancan da na rubuta saboda muhimmancinsa. Wannan kuwa ba wani abu ba ne illa abubuwan da za a kiyaye kula da su da kuma wajibcin bin hanyoyin da suka dace don kare lafiya da rayuwar jama’a da ma ta dabbobi, musamman a mayankun dabbobin da muke da su a kasar nan. Domin idan muka yi dubi da irin abubuwan da suke faruwa a wadannan wurare, abin babu kula da sha’anin lafiya a ciki.

Mahauta, wani wuri ne da ake amfani da shi wajen yankan dabbobin da ake sayar da namansu a kasuwanni da wuraren cinikayyar nama, inda yake da matukar muhimmanci a kiyaye kula da tsafta da kuma kyaun wadannan wurare.

Yawan naci game da muhimmancin wayar da kan al’umma bisa hadarin da ke tattare da abubuwan da suke faruwa a wadannan wurare, wani abu ne mai kyau, a yi ta nanatawa har sai masu hannu a ciki sun farga su tashi tsaye don kawo gyara, musamman ganin cewa akwai matakan da gwamnati ta dauka don kiyaye lafiyar jama’a, amma maganar gaskiya ba a bin wadannan dokoki a wasu wuraren.

A shekarun baya, lokacin ina Editan jairdar LEADERSHIP HAUSA kafin a dawo a rinka fitowa a kullum, na taba yin wani babban labari game da irin yadda wadannan wurare suke gudanar da harkokinsu, musamman wajen babbakar fata da kanun dabbobin, inda a wasu wurare ake amfani da tayar mota, da kuma yadda ba a bin ka’idan wajen yanka da kuma safarar naman ma shi kansa.

A cikin wannan labari mun yi zuzzurfan bincike wajen yadda wadannan wurare suke gudanar da harkokinsu, musamman game da abin da ya shafi kiwon lafiya. Duk da cewa a ka’ida gwamnati ta sanya ido wajen ganin ana samar da tsaftataccen nama, inda ta ajiye ma’aikatan lafiya na musamman masu bincika lafiyar dabba kafin a yanka, da kuma lafiyar nama kafin a fita da shi zuwa kasuwa.

Za mu iya cewa akwai irin wadannan mayanka dabbobi a kusan kowace Karamar Hukuma, ko kuma ma mu ce a kusan kowane gari, musamman a Arewacin kasar nan, ta yadda kuma kowane wuri za ka samu yana da tasa hanyar da yake samar da manan, musamman wajen babbaka ko tabbatar da lafiyar dabba kafin a yanka.

Wasu mayankun idan mutum ya je ya ga yadda ake gudanar da harkar nama, to duk yadda yake da kwadayi ba zai iya cin naman ba, ba don komai ba sai don irin jagwalgwalon da ake yi a wajen, sannan kuma ga wani irin wari da ke tashi da zarar mutm ya zo wucewa ta wurin.

Haka kuma hatta yadda ake safarar naman a wasu garuruwa ma abin bai kamata ba, domin a wasu wuraren ma mutum zai ga a mashin ne ake jigilarsa, kuma wani bangare na naman ma yana jan kasa. A wasu wuraren kuma ana jigilar naman ne a wasu tsofaffin motoci, wadanda su kansu ba su da tsafta balle su dauki abin da mutum zai ci.

A wasu mayankun ana bin ka’idodin da gwamnati ta kafa wajen tantance lafiyar dabba kafin a yanka, da kuma tantance ingancin nama kafin a tafi da shi kasuwa, amma gaskiyar magana a wurare da dama, musamman a yankunan karkara, ba a ma san da wadannan ma’aikata na lafiya ba, ballantana su duba abin da ake yankawa.

Idan muka juya ga masu babbaka kuwa, abin ya zama yanzu saboda tsadar itace, a wasu wuraren ma sun koma suna babbaka ne da tayar mota da fetur, ba tare da la’akari da hadarin da ke cikin yin hakan ba, duk da yake yanzu a wasu wurare an samu ci gaba ana amfani da zuga-zugi. Domin a wancan rubutu na musamman da na ce mun yi a LEADERSHIP HAUSA mun kawo bayanai daga Likitoci da sauran masana kiwon lafoya game da hadurran babbaka da tayar mota.

Idan mutum ya yi arba da irin wadannan wurare zai ga yadda hayaki ke turnuke sama sakamakon wadannan tayoyi da ake konawa wajen babban kanun da fata. Wanda irin wannan abu, baya ga hadarin da ke cikin cin wannan nama, akwai kuma hadarin samar da gurbatar yanayi sakamakon wannan hayaki da ke tashi.

Wani masanin harkokin kiwon lafiya a Kaduna, Dk Yusuf Nadabo ya taba bayyana cewa irin hayakin da wannan kona taya ke haddasawa yana sabbaba manyan cututtuka ga kananan yanara, tsofaffi da kuma kara ma masu fama da cutar Asma ciwo saboda gubar da ke tashi daga kona tayar. Kuma yana abin kara samar da masu cutar zuciya a cikin jama’a.

Masanin ya ci gaba da bayyana cewa, abin takaici, idan mutum ya ziyarci Kananan Hukumomi zai tarar da kimanin mayankun dabbobi biyar zuwa goma, sannan duk wadannan mayankun ba su da wata hanyar babbaka sai ta amfani da taya, wacce kuma ya ce tana da mummunan hadari, musamman ga lafiyar dan adam, dabbobi, tsirrai da kuma wuraren da jama’a ke zaune.

Don haka ne nake ganin yana da matukar muhimmanci ga irin wadannan mutane masu sana’a a  wadannan wure su rinka sanya lafiyar jama’a a gaba wajen neman halaliyarsu, maimakon neman kudin kawai ta hanyar cutar da jama’a. Haka su kuma ma’aikatan lafiya da ke aiki a wadannan wurare, su sani cewa hakkin jama’a ne gwamnati da dora masu don su kiyaye lafiyar jama’a.

Sannan Kamar yadda na ce a sama, a wasu wurare na ga an koma ana amfani da zuga-zugi wajen yin wannan babbaka, wanda ya fi sauri, kuma ya fi tsafta, me zai hana sauran wurare ma su yi koyi hakan?

Sannan kuma muna yin kira ga duk wanda ya san yana da alhakin kula da wadannan abubuwa, ya san cewa amana ce aka dora masa, idan kuma ya ga cewa saboda dan abin duniya da yake samu ya gwammace ya bari a yi wasa da lafiyar dubban jama’a, to akwai ranar kin dillanci, domin Ubangiji Allah na nan a madakata.

Allah ya kare mu daga kamuwa da dukkan cututtuka, amin.

 

Exit mobile version