Sani Hamisu" />

Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Yayin Da Kake Chajin Wayarka

Mutane da yawa masu amfani da wayar hannu kuma suna yawan korafin cewa wayoyin su ba sa rike chaji ma’ana suna saurin fitar da chaji Idan aka musu cikin gaggawa.Wani lokaci sai su dora laifin ga masu sana’ar chajin wayan wanda hakikanin maganar ba haka bane.

Nan wasu kura-kurai ne  da duk mai amfani da waya ya kamata ya sani lokacin da yake chajin wayar sa.

Idan ka sanya wayar ka a chaji to ya kamata ka barta har sai ta fara chajin daga matakin farko na chajin sannan kar kayi amfani da ita har sai ka tabbata cewa chajin ya kai wani babban mataki.

Sannnu a  hankali chajin zai rinka shiga ciki wayar ka cikin sauri zuwa tsawon wani lokaci muddin yana farawa kuma kabar wayar a wajen da bashi da zafi.

Kayi la’akari da batirinka kamar jikin mutum,ta yanda zaka rinka sabunta shi kuma kana bashi hutu , ba wai kullum zaka rinka amfani da shi a waya amma kuma baza ka barshi yayi chaji na wasu yan awanni ba.

Barin waya ba tare da ka taba ta ba lokacin da take chaji yana sanya waya ta rinka fitar da zafin da yake jikin ta lokacin da take chajin,kuma yin hakan yana da matukar muhummanci don kaucewa zafin da na’urar zata dauka,saboda haka duk wani zafi da wayar ta dauka ta hanyar zafin rana to a wannan lokacin ne zata saukar da shi duka.

Ta bin wadannan hanyoyi ne kadai zaka hana na’urar ka daukar zafi kuma zai taimaka mata sosai wajen ingancin batirin.

Ka kula sosai duk lokacin da kake chajin wayar ka, ka lura da inda ka sata chaji, kullum na’ura tana son a rinka ajjiye ta a waje mai kyau mai tsafta, saboda lura da Inda ka ajjiye ta Idan muhallin yana da kyau to zai taimakawa batirinka wajen rage daukar zafi.

Kowaccce waya tana daukar zafin jiki wanda hakan ya faruwa ne daga lokacin da take yin aiki da ita kullum kuma gashi inda ake chajin ta waje ne mai zafi to hakan ma yana kara rage mata karfin batiri.

Ya kamata ace wayar ka tana chaji a wajen da yake da sanyi inda babu zafi sosai kamar wajen da iska ya wadata, iskar zata taimakawa batirin lokacin da ake yiwa na’urar chaji sabosa abune mai zafi yake shiga jikin ta Idan ana samun iska a wajen zai sanya batirin ya rinka aiki yanda ya dace.

Ya zamana kullum kana amfani da waya tsakanin awa biyar zuwa takwas saboda batirin wayar ka yana bukatar hutu na awa biyu zuwa uku, chajin waya a daddare yana taimakawa batirin wajen dadewa da chaji wanda kuma yana rage matsalolin batiri.

Bugu da kari yana da kyau ka rinka sanya wayar ka a chaji musssaman lokacin barci har zuwa lokacin da rana zata fito kuma kasan a wacce irin chaja zaka sa wayar ka saboda kaucewa matsalar batiri.

Mafi yawan wayoyin hannu suna amfani da wani abu da ake kira micro Kebul domin chajin waya saboda wasu dalilai,mafi ya yawan mutane sukan chaza wayar su lokacin da bai dace ba,kuma rana chaji suna amfani da ita wanda hakan yakan rage mata karko. Duk da haka, wannan bai dace ba kuma a dokar waya zai iya zama kuskure.

Gaskiyar magana yawancin wayoyin hannu suna da wata na’urar a jikin su da ake kiran ta da suna USB kuma wannan ba yana nufin duk kan wayoyi yana basu chajin da ya dace ba.

Wasu caja suna da banbanci da wata na’urar saboda wata chajar karama ce Idan kasa wayar ka a jiki zata iya zama matsala, nan ma abin kula ne mutum ya san irin cajar da zai yi amfani da ita.

Zaka iya samu masana’antu suna sayar da chaja wadanda suka fi rahusa, to kar kabi arahar ka tsayi mai tsadar saboda zata fi maka amfani fiye da wacce take da arahar.

Ya zamana idan kana amfani da chaja a wayar ka to kar ka rinka sanya wasu wayoyin saboda yin haka yana rage kyawun chaja kuma yana rage karfin batiri daga lokaci da ake amfani da shi.

Exit mobile version