Gwamnan Jihar Katsina Alh. Bello Masari Ya bayyana cewa abubuwan kirki da marigayi Sir Amadu Bello Saradaunan Sakwato ya yi wa jama’a ne yasa har yanzu ba su manta da shi ba kuma ba za su manta da shi ba.
Gwamna Aminu Bello Masari yana magana a lokacin da tawagar gidauniyar tunawa da Marigayi Sir Amadu Bello Sardaunan Sakwato suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a karkashin jagorancin Galadiman Katsina
Hakimin Malunfashi Mai shari’a Maman Nasir Ya kuma bayyana cewa shekaru sittin da suka gabata sir, Amadu Bello ya ra su amma har yanzu ana tunawa da shi saboda yadda ya gina al’umma ta zama mai dogaro da kanta bisa tsari da kuma adalci.
Ya ce daga cikin abubuwan da marigayi Sardaunan Sakwato ya dage kai da fata akan su, sune ya tabbatar an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin arewa kuma shi a rayuwarsa bai dauki tara dukiya wani abin
Alhaji Aminu Masari ya nuna takaicinsa akan yadda wasu ke amfani da addini wajan neman mulki ba tare da lura ko la’akari da bukatun al’umma ba, inda ya ce jihar Katsina bata da wani dalili na kin mutunta mutanan da suka yi hidimar karatu a tsohuwar kwaleji Ilimi ta Katsina wanda ake alfahari da su har gobe.
Haka kuma Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin biyan naira miliyan hamsin daga cikin miliyan dari da hamsin ga gidauniya wanda ya yi alkawarin tun a ranar da aka kaddamar da ita inda ya ce kafin nan da karshen shekara za a biya sauran miliyan dari.
Tun da farko da yake nasa jawabin babban jagoran gidauniyar Sardauna Galadiman Katsina Hakimin Malunfashi, Mai Shari’a Maman Nasir wanda ya yi dogon bayani game da halayan kirki na marigayi Sir Amadu Bello Sardauna ya yi kira ga shuwagabanni da su koyi da shi.
Daga cikin ‘yan tagawar Gidauniyar tunawa da Sir, Amadu Bello Sardaunan Sakwato har da Sardaunan Katsina kuma tsohon Shugaban ‘Yan Sanda Najeriya Ibrahim Amadu Kumasi da Yariman Zazzau, Alhaji Mannirn Ja’afaru da sauran ma’aikatan Gidauniyar.