Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Abuja Da Kewaye: Yadda Daɗin Shayi Ya Kafa Tarihi A Gwagwala

by Tayo Adelaja
October 6, 2017
in RAHOTANNI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdulrazaƙ Yahuza Jere,   Abuja

Wasu matasa a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada da suka fara sabawa da juna ta dalilin shan shayin ataya (Shayin Buzaye), sun kafa tarihi a yankin ta hanyar ƙarfafa shan shayinsu da wasu ayyukan cigaban al’umma.

samndaads

Daga taruwa su sha shayin da maraice bayan sun dawo aiki ko wuraren kasuwancinsu, a yanzu haka daɗin shayin ya ƙara musu azama har suka kafa wata ƙungiya da suka kira Shayi Youth Association (Ƙungiyar Matasa Masu Shan Shayi).

Duk wanda ya ji sunan ƙungiyar daga nesa, zai ɗauka matasan haɗuwa suke a teburin mai shayi su sha su watse, amma lamarin ba haka yake ba. Da kansu suke dafawa a cikin butar shayi, a zuba sukari a rarraba a ‘yan ƙananan kofuna.

“Ya kamata duk abin da za ka yi ka san amfaninsa da cutarwarsa kafin ka fara. Haka nan duk abin da za ka ci ya kamata ka san cewa yana da amfani a jikinka ko a’a. To har ga Allah da muka duba sai muka ga – shayin – yana da kyau. Idan ka sha za ka ji yana ƙara maka ƙarfin jiki idan ka samu weakness (rashin kuzari) a jiki. Kuma yana maganin malaria (zazzaɓin cizon sauro) sannan yana narkad da yawan kitsen da ke taruwa a jikin mutum. Haka nan idan mutum yana da cutar shawara idan ya sha wannan shayin, da yardar Allah za ka ga ya samu lafiya da dai sauran abubuwa da yawa”.

A yayin gudanar da ƙwarya-ƙwaryar bikin ƙaddamar da ƙungiyar da rantsar da shugabanninta wanda ya gudana a Unguwar Azara da ke Gwagwalada, shugaban ƙungiyar ya bayyana yadda aka yi suka fara shan shayin har kuma ya kai su ga kafa ƙungiya sukutum ta matasa masu shan shayi.

“Tarihin ƙungiyar ya fara tun muna ‘yan ƙananan matasa. Muna zama da iyaye ne da abokai da yayye muna shan shayi irin wanda ake ce wa ‘Shayin Buzaye’ ko ‘China Green Tea’. Tun ba mu iya dafawa har muka zo muka koya. Mun yi bincike a kan shan shayin tunda yanzu zamani ne na intanet. Muka gano shayin yana da amfani a jiki da ƙara ƙarfin basira.

“Muna nan muna shan shayin shekara da shekaru sai muka yi tunanin me ya sa ba za mu mayar da abin ya zama ƙungiya ba? Da muka fara shan shayin ba mu kai mu 20 ba, sai muka mayar da abin ƙungiya na taimakon juna. Idan wannan zai yi aure sai mu haɗa gudunmawa mu bashi. A shekarar 2005 muka fara wannan. Muka naɗa shugabanni saboda Musulunci ya ce ko mutum biyu aka samu a wuri ya kamata a samu shugaba. Mun naɗa shugabanni tun daga shugaba har zuwa ƙasa. Mun fara tunanin yi wa ƙungiyar rajista a shekarar 2006 amma abin bai yiwu ba sai a 2010. Bayan mun cika ƙa’idojin rajista kamar yadda Ƙaramar Hukumar Gwagwalada ta shimfiɗa sai aka ba mu ‘certificate’ a shekarar 2011 a matsayin ‘Shayi Youth Association’ wato Ƙungiyar Matasa Masu Shan Shayi. Mun cigaba da taimakon juna, idan aure ya tashi ko suna ko rashin lafiya duk muna taimaka wa juna. Daga cikin mu 40 kusan mutum 20 duk ƙungiyar nan ce ta yi musu aure, idan ban manta ba”.

A cewar shugaban, a shekaru biyun da suka wuce ne ‘ya’yan ƙungiyar suka yi tunanin ya kamata taimakon da suke yi ya shafi sauran al’umma ba ‘ya’yan ƙungiyar kawai ba.

“A cikin ƙungiyar kowa akwai irin sana’ar da yake yi, akwai ma’aikatan gwamnati sannan akwai ‘yan kasuwa. Muka shawarci iyayenmu kan yunƙurin da muke yi na faɗaɗa taimakon da muke yi wa juna zuwa kan sauran al’ummar gari, su kuma suka ƙarfafa mana gwiwa kan haka.

“Akwai waɗanda sun gama sakandare suna son sayen fom na JAMB da kuma waɗanda suna son rubuta jarabawar WAEC amma iyayensu ba su da halin sayan musu, sai muka riƙa tsara musu ‘eɗtra lesson’ wanda a ƙarƙashin haka akwai yara guda bakwai da suka shiga Jami’a yanzu.

Shugaban ya kuma ce taimakon nasu wanda daga aljihunsu yake fita ya kuma haɗa da tallafa wa marasa ƙarfi da abinci a lokacin Azumi da kuma yi wa marayu da gajiyayyu kayan sallah dai-dai gwargwado.

Har ila yau, Ƙungiyar ta Shayi tana yin sulhu a tsakanin mutanen da suka samu saɓani walau da ‘ya’yanta ko da wasu, da ziyarar asibitoci da gidan yari domin kai taimako.

Shugaban ya yi kira ga waɗanda suke da halin taimaka wa jama’a su zo su haɗa hannu da su domin bunƙasa ayyukan taimakon da suke yi, domin a cewarsa “muna shan wahala kafin mu iya haɗa abin da muke taimakawa jama’a da shi. Kuma muna kira a taimaka mana mu samu sakatariya tamu ta kanmu saboda Alhaji Nura ya ba mu filin da za mu gina amma har yanzu ko katako ba mu saya ba saboda ko mun tara kuɗin za mu fara aiki sai mu ga wani abin tausayi na taimako mu ɗauka mu bayar”.

A nashi ɓangaren, shugaban taron, Dakta Uba Muhammad Inuwa, ya bayyana dalilinsa na amincewa ya zama shugaban taron kuma uban ƙungiyar.

“Babban dalilin da ya sa na zo shi ne ganin ƙungiyar ta fuskanci cigaba ne ba irin wacce ta bar matasa kara-zube ba. A cikin ƙungiyar babu ko mai shan taba (ba wai don muna kushe mai sha ba). Ka ga a wannan hali da ake tsoro matasa suna shiga harkar shaye-shaye sai ga shi su waɗannan babu ruwansu. Matasa ne masu hangen nesa. Matasa ne masu sana’o’i daban-daban da ba ma kawai kansu suke taimakawa ba har da sauran al’umma. Gaskiya wannan ƙungiya ce da ya kamata a ba ta goyon baya. Manya da matasa na kowane yanki su ƙarfafa mata domin a samu cigaba”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, wakilin Basarake Aguman Gwagwala, Honarabul Ɗanjuma Mohammed ya yaba da ayyukan ƙungiyar kana ya ce “mu dama irin waɗannan abubuwan muke so na cigaban al’umma amma ba waɗanda za su lalata jama’a su kawo riki ci ba. Ina tabbatar muku da cewa zan isar da saƙonku zuwa wurin Aguma Gwagwalada”.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai takwarorin ƙungiyar da suka haɗa da ‘Concern Youth Gwagwala’, da Nagari na Kowa, Matasan Kwankwasiyya da sauran su.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Munazzamatu Fityanul Islam Ta Buɗe Reshe A Suleja

Next Post

Mun Gamsu Da Yadda Ake Aikin Hanyoyinmu —Gwamna Masari

RelatedPosts

Matasa Su Dage Da Neman Ilimi Da Koyon Sana’oin Hannu – Dakta Ibrahim Agege 

Matasa Su Dage Da Neman Ilimi Da Koyon Sana’oin Hannu – Dakta Ibrahim Agege 

by Sulaiman Ibrahim
29 mins ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai Legas Neman ilmi da koyon sana’oin...

Hajiya Ummi Muhammed Ta Zama Sarauniyar Matan Jihohin Yamma

Hajiya Ummi Muhammed Ta Zama Sarauniyar Matan Jihohin Yamma

by Sulaiman Ibrahim
35 mins ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai, Legas Koda- yaushe cancanta da rashinta...

Abin Da Ya Sa Na Shirya Gasar Wakar Nijeriya A Kan Zaman Lafiya – Rarara

Abin Da Ya Sa Na Shirya Gasar Wakar Nijeriya A Kan Zaman Lafiya – Rarara

by Sulaiman Ibrahim
41 mins ago
0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina Shahararar mawakin siyasar nan da ya...

Next Post

Mun Gamsu Da Yadda Ake Aikin Hanyoyinmu —Gwamna Masari

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version