Daga Mahdi M. Muhammad,
Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF), a safiyar ranar 21 ga Fabrairu 2021, ne ta tabbatar da cewa daya daga cikin jiragen ta, kirar ‘Beechcraft KingAir B350i’ (NAF 201), ya yi hatsari yayin da yake dawowa zuwa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan da ya bayar da rahoton tsayawar aikin inji a wuraren Minna, inda aka aika shi don gudanar da ayyukan sa-ido a kan jihar Neja da kewaye dangane da kokarin hada karfi don ganin an sako daliban ma’aikatar da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, Jihar Neja.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, kamar yadda bayani ya gabata, babban hafsan sojin sama (CAS), Air Bice Marshal Oladayo Amao, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin. Yayin da kwamitin ta fara aikin, NAF, bayan ta sanar da ‘yan uwa da dangin mamatan, da bakin cikin sanar da ma’aikata 7 din da suka rasa rayukansu a hatsarin, wadanda suka hada da;
- Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Captain).
- Flight Lieutenant Henry Piyo (Co-Pilot).
- Flying Officer Micheal Okpara (Airborne Tactical Obserbation System (ATOS) Specialist).
- Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist).
- Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist).
- Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist).
- Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).
Tun da farko, Shugaban ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru, tare da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, Babban hafsan tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, da sauran shugabannin hafsoshin soji. Shugaban, a madadin hafsoshi, sojojin sama da maza da mata na NAF, yana sake yin ta’aziyya ga dangin mamatan tare da addu’ar Allah madaukakin Sarki ya yi masu rahama kuma yasa sun huta.